Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 25

Chapter 25

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ji ba, ta kalli jabeer dake tsaye yana kallonsu yana murmushi tace ni wai me ma zakayi a daura ne ka kirkiri tafiyar gaggawa, alhj bara'u yayi dariya yace zuciyarki ce ta kirashi kenan dan tayi mishi wannan tambayar, jabeer yayi dariya kamar zai faďa musu sai kuma ya fasa yace ziyara kawai zanje yi ummi, tace to Allah ya bamu ladan tare, duk sukayi dariya haďe da cewa ameen, kallon babanshi yayi yace baba akwai maganar da zamuyi dakai akan wasu takardu suna nan a ďaki na in na dawo in shaa Allahu zamu tattauna, alhj bara'u yace Allahumma yashaa ka gaida Baba da Goggo, yace zasu ji sosai ya fita Amirah ta biyoshi da gudu tana mishi bye bye, hararta yayi yace Allah yasa a fasa miki jiki da dukan latti, tayi mishi gwalo ta shige mota tana dariya tana daga mishi hannu, shima motarshi ya shiga ya tada ya fita yana gaisawa da baba ado da sauran masu aikin gidan.. Hanyar daura ya ďauka ba tare da ya tsaya yaga Afeeyah ba saboda yana gudun bata mishi lokaci da zatayi dan yasan in har ya shiga to bazai taba tafiya da wuri ba,, Karfe 10 da mintina ya isa gidan kaka liman, bayan ya huta yaci abinci da furah suka dinga hira dasu Goggo, basu fara aiwatar da komai ba sai da sukayi sallar azahar sannan suka fita shi da kaka liman, suna tafe yana mishi bayanin irin mugayen tsafin da akayi ma Affan wadanda aka binnesu a cikin gidan, kaka limann yace saboda rashin imani irin na matar nan har kafin fita gida tayi mishi dan kar ma ya fita wani ya ganshi yayi mishi addu'a ko ya taimaka mishi, sannan ta katangeshi daga dukkan adduar mutane ta mantar da mutane ciwonshi in ba waďanda suke kusa dashi ba, jabeer ya jinjina kai yace ay ni ban ďauka zaluncinta har ya kai haka ba walhy kaka, amma in shaa Allahu karshenta yazo, wani kauye suka je a cikin kasar Nigar mai suna "Tsatsunburum (s Burum)" kauyen bashi da nisa da zangon daura, gaba da gidan sarki sukaje kaka liman yace ya tsaya anan, jabeer ya kalli gurin, a katange yake da wata katuwar bishiya a ciki, kaka liman ya fito ya shiga gurin jabeer na binshi a baya, ashe wata katuwar rijiyace a cikin gurin mai cike da tarihi, kaka liman ya kwance ledar da ya zo da ita ya fito da wasu layu da magunguna ya fara haka rami ya binnesu sannan ya ďauko wata gora a cikin jakarshi da magunguna a ciki yasa hannu a cikakkiyar rijiyar ya debo ruwan cikinta sannan suka fito daga gurin, jabeer dai kallon gurin yakeyi ga rubutu a jikinshi amma rubutun ya fara gogewa, ya kalli kaka yace kaka amma wannan rijiyar tana kunshe da tarihi ko, kaka liman yace kwarai kuwa, abin al'ajabi ya taba faruwa a gurin nan, ya nuna mishi wata bishi dake dan nesa kaďan da gurin yace kaga waccan bishiyar, jabeer yace eh kaka, yace to daidai saitinta da gurin kiwon shanu ne, shanaye da yawa ake kiwo a gurin, "akwai wata saniya guda ďaya kullum aka bata abinci sai taki ci haka ruwa, saidai a ganta kullum da yamma tazo nan gurin da muka shiga kafin a katange shi ta daďe a gurin har sai dare take komawa cikin yan uwanta, kullum haka takeyi sam bata cin abincin da ake basu, ana cikin haka rannan sai mai shanun ya dinga binta a baya dan ganin abinda takeyi a gurin, yana zuwa gurin yaga ta kafa kanta a wani ďan tsukukun rami tana shan ruwa, tana gamawa yaga ta kwanta karkashin bishiyar nan lokacin tana karama sosai a gurin take bacci har dare sannan ta koma cikin yan uwanta, in takaice maka dai wannan saniyar tunda ake kiwonta bata taba cin abinci ba wannan ruwan shine ya zamo ruwa da kuma abincinta sannan wannan bishiyar ta zamo gurin hutu a gareta har ta mutu a gurin, bayan ta mutu ne mutane suka haka wannan ramin ya zamo rijiyar da bata taba kafewa ba duk wahalar ruwan da akeyi a garin tofa wannan rijiyar na nan da ruwanta sannan wannan bishiyar tana nan bata taba fadi ba shekaru fin 100 dan nima labari aka bani, jabeer yace ikon Allah shine aka katange ta, kaka liman yace kwarai kuwa kuma cikin ikon Allah ruwan cikinta yana zama waraka ga duk wanda ya yarda da Allah kamar yadda ta kusugu take, jabeer yace Allah ya kara ma Annabi daraja, kaka yace ameen jabeer shiga muje dan zan ga Aminina "Maina dogon yaro" shima akwai abin da zai bani daga nan mu wuce cikin daura mu karasa, jabeer yace to kaka, suka shiga mota suka wuce jabeer na kallon girman bishiyar yana tasbihi ga Allah... Sai bayan magriba suka gama komai suka dawo gida a gajiye, dakyar jabeer ya iya taba abincin da Goggo ta kawo mishi sauri2 dan yana son ya dauki hanyar gida komin dare, babu yadda basuyi dashi ba akan ya kwana yace samm bazai kwana ba dan gobe da wuri yake so fara aiwatar da aikin cikin gidansu Affan wanda shine mataki na karshe na aikin,, sai da yayi isha' sannan kaka liman ya fito yayi mishi rakiya yana kara nuna mishi yadda zaiyi amfanin da maganin yana kuma mishi faďa akan yayi taka tsantsan da oyizah, jabeer ya shiga mota yace in shaa Allahu kaka zanyi duk yadda kace, mun gode sosai, kaka liman yace to Allah ya tsare kayi tuki a hankali ďan boko, jabeer ya tada motar yace baka da matsala tsoho, yaja motar suna ďaga ma juna hannu, saida yaga kulewar motarshi sannan ya juya gida, haka kawai ya tsinci gabanshi da tsananin faďuwa, a waje ya zauna yana bin sawun motar jabeer da kallo yana mishi adduar Allah ya kiyaye hanya... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣0⃣ By Aysha Ya'u Kurah ★ 9:54pm ★ Tun bayan magriba hadari mai tsananin duhu ya taso yana kokarin haduwa a gabas, iska ce mai dadi taketa kaďawa a wannan lokacin har zuwa karfe 9:32pm, lokacin ne hadarin yamma ya kusa haďuwa da na gabas, iska mai karfin gaske haďe da guguwa da walkiya su keta tashi ta ko'ina kamar zasu tashi gidaje da motocin biladama, yaf yaf ruwan feshi ke busawa a cikin iskar, A wannan lokacin gudu jabeer yakeyi cikin motarshi yana Allah Allah ya isa kano kafin goma ko kuma goma daidai, wuce motoci yakeyi yana tafiyarshi cikin kwanciyar hankali yana wiping yayyafin dake sauka a kan glass din motarshi, karfe 9:50 ya rage saura k.m baifi 15 ba ya shigo garin kano, murna ya dinga yi dan yasan in shaa Allahu kafin 10:30 zaiga Afeenshi, har ya dauko wayarshi zai kirata sai ya fasa so yakeyi kawai ta ganshi kafin lokacin da ya daukar mata.. Wani haske ya gani ya gifta gabanshi hade da girgiza mai karfi wacce tayi sanadiyyar fitar tayar motarshi ta gaba, runtse idonshi yayi sosai yana kalmar shahada saboda yadda yaji shi a sama motar na juyawa sosai, wasu masu trailer sukayi parking gefen hanya suna salati cikin tsoro saboda yadda motar ke wulwulawa a sama, saida tayi minti

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});