Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 33

Chapter 33

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tana kuka sosai tana hango rayuwar da zatayi a gidan su Affan tare da su mummy masu kirar samudawa, yaya zatayi ta iya zama da Affan a wannan halin da take ciki, bata tunanin zata iya taimakonshi domin itama neman wanda zai taimaketa ya tausheta takeyi, babu irin rarrashin da hajja batayi mata ba akan ta dauki auren a matsayin kaddara, ita kanta hajja tsoro abin yake bata domin tasan jikarta zata shiga wata irin rayuwa mai cike da jarabawa,, saida tayi kukan ta gaji dan kanta ta bingire da baccin wahala a takure gurin,,, Karfe uku da kwata na dare hajja ta jiyo muryarta cikin bacci tana sambatu hawaye da zufa sun jika fuskarta da wuyanta, a hankali ta matso kusa da ita ta kama hannunta zata fara mata magana taji ta matse hannun sosai tana faďin "bazan iya ba yaya jabeer, bazan iya ba,,, dan Allah ka dawo gareni, kasan a irin wahalar da kabar zuciyata, dan Allah karka kara tafiya ka barni, hajja ta fara cire hannunta cikin nata ta kara matsesu da karfi tana faďin "bazan kara barinka ka tafi ka barni ba,"" hajja ta share hawaye ta janyota jikinta tana karanto addu'a tana tofa mata a hankali, cikin ikon Allah tayi lamo jikin hajja tana ajiyar zuciya,, hajja bata koma bacci ba saida ta tabbatar Afeeyah ta daidaita sannan ta kwantar da ita itama ta kwanta tana kallonta.... Mrs tijjani shattima... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣8⃣ By Aysha Ya'u Kurah Washe gari karfe 10am aka ďaura auren "Afeeyah da Affan" banda Hajja, Abida da Asiyah babu wanda yasan da maganar auren, alhj basheer ba karamin farin ciki yayi ba dan ji yayi kamar ya goya malam Atiku dan murna, godiya kuwa yayita har yana neman tsugunawa saboda acewarshi wanda zai dauki ya' kamar Afeeyah ya bawa mahaukaci ay ba karamin jihadi yayi ba, kaka liman kuwa zan iya cewa yafi su murna dan a ganinshi ya jefi tsuntsu biyu da dutse ďaya, yasan in Affan ya samu sauki Afeeyah zatayi alfahari da kasancewarshi mijinta dan yasan babu yadda za'ayi Affan ya wulakanta Afeeyah tunda yasan muhimmacinta a rayuwar Jabeer, Bayan an gama daura auren da adduoi suka danyi ciye ciyen da alhj basheer yayo ordr sai kowa ya wuce gida cikin farin ciki,, A kofar gida alhj basheer ya hadu da masu furnitures din daya kira dan gyara side din Affan da rabonshi da shiga tunda ya fara ciwo,, , karasawa ciki sukayi ya nuna musu inda zasu gyara nan da nan suka fara aune aune da gwaje2, karan mashin din aikinsu oyizah ta jiyo ta fito da sauri tana fadin karan meye wannan, tsayawa tayi tana kallonsu tace kaiiii daga ina kuke? Ganin alhj basheer tayi ya fito daga bayi da mai gyaran bayi suna magana tace alhj gyaran me akeyi haka,? ko Affan zai dawo nan da zama ne, alhj basheer ya bawa mai gyaran bayin kudi sannan ya kalleta yace eh nan zai dawo, oyizah ta haďe rai tace saboda me, kasan fa bazai iya kwana shi kadai ba shiyasa na bashi daki daya a cikin nawa, alhj basheer yayi murmushi yace nan din ma bashi kaďai zai dinga kwana ba, oyizah tace kamar yaya,? Alhj basheer yace surprise nakeso in baki, naso sai an kawota sannan zaki ganta amma tunda kin dan fara dagowa bari in fada miki, yanzu aka daura ma Affan aure, oyizah cikinta ya ďuri ruwa tace aure alhj? Yace kwarai aure, zanso kiga farin cikin dake raina game da wannan auren safiya, oyizah ta share gumin fuskarta tace da wa aka daura mishi auren, wayarshi ta fara ringing yayi saurin ce mata da Afeeyah yar gidan malam Atiku, ina zuwa bari muje mu dawo zanyi miki bayani ya fita da sauri saboda wayar ta sake kara alhj Bara'u ke jiranshi zasuje yi mata siyayya tare da Asiyah, ,, tsaye yabar oyizah baki sake tana kallon masu aikin gurin, dakyar ta iya ďaga kafarta ta wuce parlor, wani irin zama tayi akan kujera har saida kujerar ta amsa, da sauri farida ta mike a kujerar tace haba mummy wannan ay sai kisa muyi kasa, oyizah da idonta yayi jawur tace mukai kasan mana, farida ta dawo kusa da ita tace mummy lafiya, oyizah tace hmmm aure aka ďaura a cikin gidannan, farida cikin kidima tace daddy ne yayi aure, oyizah tace gara min shi yayi aure dan nasan duk wacce zatazo baza tayi karko ba, farida tace to waye yayi aure, dai2 lokacin Affan ya wurgo kwallo yana bugawa cikin farin ciki ta kalleshi tace wancan saunan aka daura ma aure, fareeda ta kwashe da dariya tace ita kuwa wannan wace dakikiyar ce ta yarda ta aureshi, mummy tayi tsaki tace mune dai dakikan da tuntuni banyi tunanin nemo mace sakarya na haďashi da ita ba,, Farida tace ban gane ba mummy, oyizah tace ay kwakwalwarki bazata gane ba amma nasan in na faďa miki amaryar zata gane, Ay kwakwalwarki tasan Afeeyah yar kishiyar suwaiba ko?, farida ta dafe kirji tace farin sani mummy ita ya aura, tace aka daura mishi dai, ta kalli Affan taga ya kara mata nuri sajenshi ya kwanta luff" yayi matukar kyau kamar yasan yau zai angwance, da karfi ta kira sunanshi ya taho da gudu ya zauna kusa da ita, ta kalleshi tace u luk very happy my son, ya kara gyara zamanshi cikin murna yace am happy mummy yau za'a kawomin Afeeyah, ta kalleshi sosai tace waye ya faďa maka, yace ni nace daddy ya kawomin ita mu dinga wasa ba jiya nazo zan fada miki ki mata girki mai dadi ba kika koreni, oyizah tayi saurin dafe kanta da ya sara mata tace tashi ka tafi, ya mike tsaye har ya fara tafiya sai kuma ya juyo ya tsuguno saitin kanta yace mummy zakiyi mata girkin, a hassale ta dago ta daka mishi tsawa tace ubanka zan girka mata, wuce ka bani guri, Affan ya wuce cikin tsoro yana waigenta kamar zaiyi kuka.. Farida ta dafata a hankali tace mummy meyasa kike damuwa naga Affan is under ur control dole itama in ta shigo ta zama a karkashinki, ni mummy kin bani mamaki wannan small girl din kike damuwa akanta, duka fa bata wuce 17 to 18, oyizah tacee uhmm kawai ta mike tayi sama tana tunanin yadda zata fara bullo ma wannan alamarin... A can gidan Malam Atiku kuwa tunda suwaiba ta samu labari take bala'i tana zaginshi, wai akan me za'a boye mata maganar auren saida aka daura za'a fada mata dan anga ba ita ta haifeta ba, malam Atiku cikin fushi yace sannu uwata, wani abun zaki tsinana min in na fada miki, ko nairah dari bazaki kawo kice a siya mata cokali ba to niko saboda me zan faďa miki, aure ne an daura shi babu wanda ya isa ya warwareshi, nan fa suwaiba ta cigaba da bala'i tana aibata auren harda kuka saboda bakin ciki, acewarta ita bata bakin ciki da auren musaki amma can cikin zuciyarta takaici ne dankare saboda tasan ko Affan zai dawwama cikin ciwon hauka Afeeyah ta gama warkewa, hangowa ta dinga yi da kausar ce da tuni yanzu alhj basheer ya fara jikata da

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});