Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 20

Chapter 20

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kwallar munafurci hakuri yace bamu san akwai adduar da za'a bashi bane da bamuyi gangancin bashi ruwa ba, tace babu komai doctor, yanzu zan iya bashi kenan, doctr musah yace eh hajiya, nan oyizah tayi murmushi ta gefe ta zauna ta bude bakin Affan ta tsirara mishi ruwan da yasa shi sakin razananen ihu, da sauri ta mike da ta tabbatar da ya hadiye ta matsa baya tana kuka tana fadin doctr dubashi, da kyar doctor musah ya samu yayi mishi allurar da tasashi bacci ihun ya lafa, ya waigo ya kalli oyizah yace hajiya I think ruwan adduar nan yasashi ya farfado gaba daya saidai kuma yanzu ne za'a fara jinyar, yasa kai ya fita.. Oyizah tayi dariya sosai tace ba dole ya farfado ba, na daďe ina jiran wannan ranar, ta kalli ruwan sosai tace nasan har yakai inda nakeso yakai, ta harari affan ta fara shafa mishi ruwan a fuska tace kai da samun sauki har abada Affan.. Tun daga ranar ciwo ya dawo sabo, saboda kullum da ihu yake farkawa sai an mishi allurah ake samun saukin abun, ciwon kanshi kuwa ya fara warkewa, dan gurin da yayi rami ya ciko sosai, saida yayi sati ďaya kullum ya farka da ihu yake farkawa, daga ya farka kafin ayi mishi allura oyizah zata bashi maganin da tace ruwan addu'a ne, Watanshi ďaya a asibiti ana fama da lalura ďaya, saidai a kawo babban likitan mahaukata gurinshi ya dinga mishi treatment saboda ciwon da ke kanshi, yanzu kam ciwon yayi sauki sosai dan haka doctor musa ya bada shawarar a kaishi "psychiatric" alhj basheer sam yaki yarda yace saidai ya fita dashi waje, doctor musah yace hakan ma zaifi Alhj, gara ka kaishi wajen, akwai wani asibiti a "New Toronto, Canada" sunanshi "LAKESHORE PSYCHIATRIC HOSPITAL" asibitin sun kware sosai alhj, in dai waje zaka fita dashi gara ka kaishi can, kuma anan nigeria ma fa akwai psychiatric masu kyau kuma ana kula sosai, kamar su "FEDERAL NEURO PSYCHIATRIC" dake kaduna da kuma na Lagos, da ma sauransu, amma tunda hankalinka yafi ga fita dashi din gara ka fita dashi, mudai fatanmu a koda yaushe shine ya samu lfy, , alhj basheer yace hakane doctor, nagode sosai in shaa Allah gobe zamu fara processing tafiyar,, doctor musah yace to Allah ya kaimu alhj shi kuma Allah ya------- doctor musa ya kasa karasawa saboda datse harshenshi da yayi, ya kalli alhj basheer ya mika mishi takardun sallama da reports din ciwon Affan tare da magunguna... Watan Affan biyu a canada, oyizah ke zaune dashi saboda yawan tafiye tafiyen da alhj basheer keyi, jikinshi yayi kyau sosai saidai duk wanda ya ganshi yaga mai tabin hankali, komai na yara yakeyi, ga yawan son wasa, kallon ruwa da kifaye da sauransu, a cikin wata biyun nan oyizah ta mallake Affan sai abinda tace yayi, sam bata nuna mishi hanyar kwarai saidai ta nuna mishi mara billewa, magungunan tsafi kuwa su ke ďawainiya dashi tun zuwansu canada, doctors sunyi mamakin yadda akayi magungunan da suke bawa Affan bai mishi aiki ba, sudai sunsan larura indai ta haukace to wacce tafi ta affan ma sun warkar bare tashi da suke ganinta minor, basu san duk magungunan da suke zuwa bashi oyizah ta karba tace zata bashi zubar dasu takeyi ba, wani lokacin ne ma take bashi ba bisa ka'ida ba, A ranar da suka cika wata biyu da sati biyu aka sallamesu saboda haukar affan ba ta barna bace kuma sunga in oyizah tace ya zauna nan to bazai tashi ba har sai tace ya tashi, wannan dalilin yasa suke ganin kamar in suka basu isassun magunguna nan da wasu yan watanni zai samu sauki.. Ranar oyizah tayi murna saboda dama ta kosa ta koma gida, yawo ta fita da Affan tayi mishi siyayyar kayan wasa da uban yawa tana zaba tana mishi dariyar mugunta shi kuwa banda murna da tsalle babu abinda yakeyi, a daren ranar suka hawo jirgi tare da alhj basheer sai kasar mu ta gado... Cikin dare suka iso gida a gajiye, kowanne daki yaje ya kwanta banda Affan da shi a gurinshi ma safiya ce, zama yayi a parlor yana wasa sosai gaba daya ya hargitsa parlon, in ya kalli hanyar dakin zeenatu sai ya runtse idonshi wasu abubuwa su dinga gifta mishi kamar rayuwar cartoon, kuma sai yaga kamar harda shi a cikin cartoon din, tashi yayi yana kokarin zuwa kofar dakin yaji muryar oyizah ta daka mishi tsawa, da sauri ya dawo bayanta ya tsaya yace mummy wannan kofar wanene, kamar na taba zama a ďakin, kin gani kofar ma kamar ta drawing ko, oyizah ta shafa kanshi tace my baby kasan meye a kofar nan, ya girgiza mata kai, ta ja hannunshi ta fara nuna mishi kofar har zuwa hanyar steps din can saman da ya faďo tace duk nan gurin zaman macizai, da namun daji ne, kana son su cinye ka, ya noke wuyanshi ya make a bayanta, tace to karka kara zuwa arean gurin kaji, yace to mummy, ta kama hannunshi ta wuce side dinta dashi ta sashi a wani daki ta rufe tana kyakyata dariyar mugunta da jindadi.. Tun karfe 12 jabeer keta fama da masu gadin gidan akan su bude mishi kofa sunki, dan oyizah tace kar a kara barin kowa ya shigo saida izininta, ran jabeer ya baci sosai idonshi yayi jawur, yace yanzu Halilu har ni ma sai ku hana shiga in an saku, halilu yace kwarai kuwa saboda ina mutunta aikina, jabeer yayi kwafa kamar zai juya sai ya dawo da karfinshi ya tura halilu ya ruga ciki da gudu suna binshi a baya, da sauri alhj basheer ya fito jin hayaniyar tayi yawa, tsawa ya daka ma su halilu yace lafiya kuke binshi kamar wani barawo, halilu yace ranka ya dade madam ce tace kar abar kowa ya shigo, alhj basheer yace jabeer ne kowa, baku san matsayinshi a gidannan bane, oyizah ta fito da sauri tace yi hakuri alhj mantawa nayi in ce musu kar su hana jabeer shigowa, alhj basheer yace to su sauran mutanen kuma fa meye dalilin hanasu shigowa, ta fara matsar kwallah tace bana son a shigo a dinga yi ma affan dariya na fi son sai ya warke mutane su ganshi, alhj basheer ya jinjina kai cikin damuwa yace na gamsu da bayananki, share hawayenki Allah yayi miki abinda kikayi mana na alkhairi, tace ameen haďe da hararar jabeer, alhj basheer yace jabeer ka shiga ciki mana abokin naka yana ciki ai, jabeer yasa kai ya shiga cikin parlon da sallama, Zaune ya tarar da Affan da wasu kayan wasa a hannunshi, wuyanshi yasha hoda idonshi kuma kwalli, kallon jabeer yakeyi sosai wasu abubuwa na mishi yawo a kwakwalwarshi, sai da yayi minti biyar yana kallonshi sannan ya zubar da kayan wasan ya rungumeshi yace daddy wannan abokina ne sosai tare muke wasa dashi, kaga fuskarshi ma shima drawing dinshi akayi kamar waccan kofar, Salma da fareeda suka kwashe da dariya harda rike ciki, yayin da jabeer ya fashe da kuka haďe da kankameshi...... Mrs tijjani shattima... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣5⃣ By Aysha Ya'u Kurah A hankali Affan ya saki jabeer yana mishi wani irin

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});