Chapter 7
Chapter 7
Allah dan annabi ku maida mu gurin mammi ta waiga ta kalli mahaifinta tace papa kaji tsoron Allah, Oyiza cikin Fushi tace chummy lord yaran nan na bata mana lokaci gashi har asuba ta gabato ga kuma mum can daure gara ayi mata abinda za'ayi in wuce gida, Fanne ta waigo ta kalleta a hankali tace mum? U mean mum dinki kika bayar saboda--- wannan karan chummy ce da kanta ta kai mata duka a baki, chummy tace bazan kashe yaranka yanzu ba alhj sambo dey wl be under my control, zan watsasu duniya saboda naga za'a dama dasu, fanne tace karya kikeyi jininmu ne yafi karfin ki,,, chummy tayi murmushi tana girgiza kai,, Alhj sambo cikin tsoro yace my lord ina tsoron kar suyi min illa, chummy tace babu kai babu su saboda zaku binne gangar jikinsu a grave so ka kwantar da hankalinka, yayi ajiyar zuciya yana kallon hararar da fanne take musu shi da oyiza,,, dafa kansu chummy tayi da wata sanda mai kyalli nan da nan suka bace,, Mum din oyiza kuwa kuka ta dingayi ganin ďiyarta ce ta bada ita, gaba daya magana ma kasa fita tayi a bakinta sai girgiza kai kawai takeyi tana tunano rayuwar da tayi da yarta, cikin minti goma aka gama da maman oyiza suka gama shaye shayensu sannan kowa ya bace, ,, Kuka oyiza takeyi a bakin gadon da mum ke kwance tana ihu makotan da ta aika mai gadinsu ya faďa musu suna kanta suna bata hakuri, ta kira can kauyensu ta fada musu suma suka dinga ihu suka shirya suka kamo hanyar abuja, Guraren karfe biyu akayi mata sutura da kyar dan yan uwanta sunce saidai su kaita can okene a binneta ita kuma oyiza ta kafe saidai a binneta anan saboda tsoron kar asirinta ya tonu dan tasan kakarta na ganinta zata san abin da ya kasheta dan itama mayyar kanta ce, saida malamai sukayi ma yanuwanta nasiha sannan suka yarda akayi mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya... Washe gari ta kira john a waya tace yaje ya buďe shago in alhj basheer yazo ya kawoshi gidansu, haka kuwa akayi yaje ya bude shago amma har dare babu alhj basheer, washe gari ma haka, oyiza hankalinta in yayi dubu ya tashi tana ta kai kawo saboda rashin zuwan alhj basheer gashi har an kusa sati daya, a daren ranar ta bayyana gaban chummy da matsalolinta, chummy ta gama incantation dinta tana girgiza kai tace yana karkashin kulawar matarshi, ta nuna mata wata kwarya, bakar mace ta gani a ciki sanye da hijab tsaye gefen gadon mijinta dake bacci tana sallar dare in ta idar sai tayi adduoi ta tofeshi dashi sannan ta mike ta kara tada kabbara, chummy tace kin gani da idonki ko? Oyiza ta haďe rai tace na gani amma ay ni babu ruwana da wannan, mum na bayar saboda haka so kisan duk yadda zakiyi, chummy tayi dariya tace dadina dake wutar ciki, trust me Oyee cikin satin nan za'a daura miki aure da alhj basheer, cikin farin ciki oyiza tace yanzu naji magana..... Mrs tijjani shattima..... [15/12 09:32] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 8⃣ By Aysha Ya'u Kurah Alhaji basheer tsugune yana gyara canvas din kafarshi cikin shigar blue nd white track suit, mikewa yayi bayan ya gama ya kalli matarshi zeenatu dake gyaran gadon da ya tashi yace to ni na fita training, tace to a dawo lafiya yallabai, yace Allah yasa sannan yasa kai ya fita, Zagaye ya dinga yi yana jogging cikin farin ciki saboda yadda sanyin safiyya ke kaďashi, yayi zagaye na tara yana yi yana hutawa, a zagaye na goma ne ya hango wani shima jogging din yakeyi dai2 gurin wata katuwar kwata kafarshi ta gurďe ya tafi zai faďa alhj basheer yayi saurin rikoshi yana fadin subhanallah sannu, mutumin ya ďago yana gyara kafarshi yace yauwa nagode sosai gaskiya ka taimake ni, alhj basheer yayi murmushi yace mu gode ma Allah, mutumin ya mika ma alhj basheer hannu yace sunana Bara'u ina nan zoo road, "BB close" opp gidan alhj Basheer Balarabe, Alhj basheer yayi dariya yace ni kuma sunana Basheer Balarabe (BB) nima ina zaune a zoo rd BB close cikin gidan Alhj Basheer balarabe, Alhj Bara'u yayi dariya sosai yace ikon Allah alhj basheer, kaga yadda Allah ke abunshi ko, . alhj basheer yayi dariya yace kai gaskiya bamu fitar da hakkin makobtaka in ba haka ba ga gida ga gida ace bamu san juna ba,, Alhj bara'u yace ko 1week banyi da tarewa ba kuma nasa ayi min magana da duk makota na kai kaďai ne Allah baiyi zamu hadu ba saboda ance min baka gari, alhj basheer yace kwarai kuwa ban daďe da dawowa ba, to ya unguwar tamu da fatan dai baka samun matsala, Alhj bara'u yace walhy babu matsala unguwar cike take da mutanen kwarai naji dadin kasancewata cikin ku, Alhj basheer yayi murmushi suka fara tafiya yace to ya iyalin fa, Alhj bara'u yace tukunna dai har ansa rana jiranta nakeyi ta karasa skull zuwa nan da 3monts sai ayi in shaa Allah, Alhj basheer yace Allah ya nuna mana kai kadai ne a cikin gidan kenan, alhj bara'u yace eh ni kadai ne amma weekends a daura nakeyi saboda rashin iyali, alhj basheer yace hakan yayi Allah ya taimaka yace ameen har suka karaso gida suna hira cikin kankanin lokaci suka saba da juna, a dai2 kofar gida sukayi sallama kowa ya shiga gida, kanshi tsaye yake tafiya cikin gidanshi yana amsa gaisuwar masu musu hidima, yazo gab da shiga parlo yaji wata muguwar faďuwar gaba, juyawa kanshi ya fara yi sosai ya dafeshi ya karasa parlon dakyar ya zauna kan kujera, zeenatu na can kitchen bata san halin da mijinta yake ciki ba, runtse idonshi yayi siffar Oyiza ta dinga mishi yawo a cikin kwakwalwar kanshi, buďe idonshi yayi da sauri da ya tuno da oyiza gaba daya yaji wani abu ya tokare mishi kahon zuciyarshi, ga wutar son ganinta da ta ruru a zuciyarshi kamar wacce aka iza da petur, mikewa yayi da sauri ya shiga bayi yayi wanka sharp2 ya fito ya shirya da gaggawa ya feshe jikinshi da turare ya debi kudi a sv dinshi na gida masu yawan gaske sannan ya wuce kitchen ya sami zeenatu, Cikin rashin fahimta tace tafiya weekend kaiko ina zaka, yace abuja zeena alheri ne yake kirana, tayi murmushi tace to Allah ya kawo mana alkhairin tare, yace ameen yar matata sai na dawo, tace to Allah ya tsare ya kuma kiyaye hanya, yace ameen ya fita da sauri, biyoshi tayi da gudu tace na manta ban fada maka ba, dan Allah zan shiga gidan Malam atiku gurin Ma'u tayi min kitso, yace to adawo lafiya tayi miki mai kyau fa, tace karka ji komai in dai kitson ma'u ne, yayi murmushi ya fita ya tafi... Da kyar ya gane restaurant din, yana isa ya fito cikin farin ciki,, tsayawa yayi turus saboda ganin gurin da yayi a rufe, jingina jikin motarshi yayi ya rasa me ke mishi daďi yanzu wa zai fara tambaya inda take anan gurin, ya kusa 30mins kafin ya shiga motarshi da niyyar tafiya, kamar daga sama ya hango john
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61