Chapter 59
Chapter 59
Afeeyah ta hanyar zuba mata ruwan batir, cikin ikon Allah sai ta farka da addu'a nan take mai kowa mai komai ya tsareta ya mayar mata da kaidinta, mamaki suka dinga yi suna Allah wadai da oyizah dake ta faman ihu tana fisge fisgen gashin gabanta, godiya suka dinga yi ma tsohon har ya bace ma ganinsu sannan suka dawo akayi waje da oyizah dake zabura babu komai a jikinta, gudu ta dingayi tana ihu kamar mahaukaciya ta fada gidan Malam Atiku, suwaiba na zaune tana cin kosai tana hararar hajja taji an fado kanta ana ihu, da sauri suwaiba ta mike tana ihu ta fada daki ta datso tana leke tana haki, cikin kuka oyizah tace suwaiba nice, nice safiya, suwaiba tace safiya, safiyar alhj basheer, oyizah tace eh ita, ki bude min kofa, suwaiba tace Allah ya kyauta in bude ma matsafiya kofa, safiya ta kara sa ihu tace suwaiba na daina, wallhy na daina, nayi dana sani, ki yafe min, ni na kashe abulbait, ni na bashi sweet yasha ya mutu muka sha jininshi, suwaiba ta saki salati tayi saurin bude kofar tace ke kika kashe abulbait, oyizah tace nice ki yafe m--- ay bata karasa ba taji saukar tabarya a bakinta, wani ihun ta saki ga azabar konewar fuska gata jibgar tabarya, bugunta suwaiba takeyi baji ba gani tana kuka tana fadin kin cuceni, dakyar hajja ta hankada oyizah waje ta dawo bawa suwaiba hakuri, cikin kuka tace hajja ki yafemin na cuci kaina, dan ALLAH ki yafemin, hajja tace babu komai ai dama duk wanda ya hau motar kwadayi to babu a inda zata saukeshi sai tashar wulakanci, wannan ya zama darasi ga masu hali irin naki, daki suwaiba ta shige cikin nadama tana kukan mutuwar danta.... Kwanan oyizah huďu tana yawo akan titi babu wanda yake kulata bare yayi yunkurin taimaka mata, gaba daya ta gama cisge gashin gabanta da hannunta, ga ciwon jikinta da fuskarta yana mata radadi kamar zai tarwatsa kwakwalwarta, gurin wata kwata take zama ta dinga ďiban ruwan gefe tana watsawa a jikinta ko zata samu sassaucin azaba, a ranar kwana na biyar din ne tana zaune tana ihu tana fadin irin mugayen abubuwan da tayi taji an tsuguna a gefenta, da ido ďaya ta kalli gurin taga Afeeyah ce ta daga kanta taga fareeda tsaye tana kuka, mikewa tayi tana kokarin rungume farida tayi saurin ja baya tace karki tabani mummy, zuwa kawai nayi in ganki saboda an fada min hakkinki a kaina, Afeeyah tace a'a fareeda uwa uwa ce, kome tayi mahaifiyarki ce, oyizah tayi tsaki cikin azaba tace kece ma kike fada mata abinda zata min, ta kalli farida tace wannan ce take saki a hanya, zata kara magana ciwon jikinta ya mintsileta ta zaburah ta fara tsalle tana kokarin sosa jikinta, Afeeyah ta kalli farida tace kije ki kamota farida mu suturc--- bata karasa magana ba sukaji karar bugun abu, da sauri suka kalli gurin wata katuwar trailr ce tayi ciki da oyizah ta murje kanta, da gudu suka isa gurin mutane har sun taru ana kallon oyizah amma babu wanda yayi yunkurin taba ta, wasu daga sun kalleta suke barin gurin, sunfi karfin awa daya a gurin babu wanda ya taimakesu dakyar drivernsu ya dauketa aka nadeta cikin boot suka tafi da ita gida, saida zeenatu tasa baki sannan alhj basheer ya kira akayi mata wanka aka suturce ta, daga alhj bara'u sai alhj basheer sai malam atiku da masu aikin gidan kadai suka tafi kai oyizah gidan ta na gaskiya, gidan da kafa bata fitowa, gidan da ibadarka sune abokan hirarka, gidan da kudi ko mulki bazasu hanaka kwanciya kan kasa ba, gidan da babu fanka bare a.c babu iskar shaka sai in kayi aikin alkhairi, Allah kasa mu cika da kyau da imani...... Ameen Tunatarwa-- Ya yan uwana mata masu son mallakar namiji ta kowane hanya, shin in mun mallakeshi muna tunanin in mun mutu wannan mallakar bazata hana namiji ya manta damu yaje ya nemi wata ya aura ba, mallakar namiji itace biyayyarki in kikayi ma namiji biyayya tsakani da Allah wallahy kin gama mallakeshi duniya da lahira dan bazai taba mantawa dake ba, akwai matan da suke wanke najasar gabansu su sawa namiji a abin ci ko sha, wallhy, wallhy, duk macen da take wannan aikin in tazo mutuwa sai ta cisge gashin gabanta gaba daya da hannunta, shan najasa haramun ne, cutarwa ne ga dan uwa musulmi, in mallaka muke so to muyi koyi da matan manzon Allah s.a.w, akwai ayoyin saka soyayya a zuciya ko ita muka rike mun gama mallakar mazajenmu ba cuta ba cutarwa, saboda saida soyayya mallaka ke tafiya, Allah ya ganar da dukkan yan uwa musulmi baki daya, su kuma mazajenmu masu sa mu kauce hanya ta hanyar wulakanta mu Allah ka ganar dasu ka basu ikon kulawa da hakkokinmu Ameen thumma Ameen... In shaa Allah gobe zan gama muku gaba daya, kuyi mini afuwa na rashin posting da wuri Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:38] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣6⃣ By Aysha Ya'u kurah Rayuwa mai cike da so, kauna, nishaďi, farin ciki, da annashuwa shi akeyi a gidan alhj basheer, rayuwar mai cike da koyarwar addinin islama, Ni'imtacciyar rayuwa sukeyi wacce duk a da suka cire rai da samunta, Alhj basheer yana matukar kula da kowa a cikin gidan, duk wasu hidimdimu nasu yana kokari wajen daukeshi ba tare da sun kai ga bukata ba,, haka zeenatu kulawa sosai takeyi ma kowa har masu aikinta, bata bari kowa ya koka saboda matukar sanin darajar biladama, Fareedah ma rayuwa takeyi me dadi wacce take ganin ashe da can baya ba rayuwa takeyi ba saboda tana zaune cikin duhun kai ga rashin samun nutsuwar zuci saboda rashin ibada da batayi, yanzu kuwa wani nishaďi take ciki musamman in ta idar da sallah sai ta dinga jin kamar iskar wannan lokacin daban take saboda yadda take ratsa ko ina na jikinta... ( tabbas iskar wannan lokacin kam daban take ga wanda ya hankalta, duk wani musulmi da zaran ya idar da sallah to nasan a wannan lokacin zaiji kamar an sauke mishi wani nauyi akanshi kuma zai dinga jin yalwatacciyar iska mai dadin gaske, kaii musulnci yayi, Allah ka sa duk ibadun mu karbabbu ne, Alhamdulillah ala ni'imatul islam).... Soyayya da shakuwa su suka shiga tsakanin ma'auratan biyu, soyayya sosai suke gwadawa junansu haďe da mutuntawa, basa taba yarda su bata ran juna, komai nasu suna yinshi cikin so da kulawa gwanin ban sha'awa, Affan sam baya kaunar ganinta ita kaďai tana damuwa dan yasan damuwar akan jabeer ne, wani lokacin ma in ya sameta tana kuka in ya bata hakuri sam bata yin shuru har sai ya dangana da zeenatu sannan dakyar zasu hadu su rarrasheta tayi shuru, shima kuma duk ranar jumma'a sai ya kai ziyara kabarin amininshi bayan yasa an sauke qur'ani yayi sadaka sannan ya zauna a gurin ya dade yana mishi addu'a, haka cikin dare in sun idar da sallah addu'a ta musamman suke mishi da sauran yanuwa musulmai wadanda suka rigamu gidan gaskiya... Cikin ikon Allah cikin Afeeyah ya isa haihuwa yayi girma sosai dan ko mikewa bata iya yi in kuwa ta mike to sai tafi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61