Chapter 1
Chapter 1
[◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣ By Aysha Ya'u Kurah بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين والصلاة والسلام على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه وسلم. ..... Affan... Affan... Affan.. sau uku saurayin dake tsaye a kanshi ya kira sunanshi amma ko waiwayowa baiyi ba bare ya amsa,, hankalinshi na kan ruwan dake malale cikin wani katon ramin kiwon kifin dake cikin gidansu yana kallon yadda suke wuntsil wuntsil ciki yana girgiza kanshi da jikinshi hakoranshi waje yana dariya da karfi, duk wanda ya ganshi yasan hankali sam bai isheshi ba, dafashi saurayin yayi hade da zama gefenshi ya watsa ma kifin abincinsu nan take suka kara hautsinewa suna yawo cikin ruwan gwanin ban sha'awa, ihuu Affan yasa yana kaďa kanshi yana kokarin kai hannunshi cikin ramin kuma yana nokesu alamar tsoro, saurayin yayi murmushi ya kara watsa abincin,,, affan ya cikwikwiyeshi cikin murna yana fadin yeeehhh Jabeer kara zuba musu yunwa suke ji dama, jabeer ya shafa fuskarshi cikin tausayin halin da amininshi yake ciki yace affan lokacin sallah yayi muje muyi sallah mu dawo sai in cigaba da basu abincin, affan ya no'ke wuyanshi kamar karamin yaro yace um um ba yanzu zanyi sallah ba mummy tace ko da yaushe nayi sallah dai2 ne saboda ni ba a rubuta min zunubi, Jabeer da idonshi ya fara canza kala dan ya riga ya saba da jin hakan a bakin affan kullum in yayi mishi maganar sallah, cikin dabara yace waya fada maka ba a rubuta maka zunubi Affan, to bari kaji kasan wutar nan da ake kunnawa mai zafin nan? Affan cikin firgici yace eh na santa wanda ake dafa min indomie mai zafi ko, jabeer yace of course ita ay kasan tafi indomie zafi ma ko, affan ya gyada kanshi, jabeer yace to wutar da Allah ke kona waďanda basa sallah tafi wannan zafi sau "dubu malala gashin tinkiya" affan ya mike a firgice idonshi zuru2 yace tafi wutar dake dafa ruwan toilet heater ma wanda yake kona ni in zanyi wanka, jabeer yace sosai ma ay wannan ruwan kamar ruwan sanyi ne akan wutar Allah, affan ya fara ja baya yace karya kakeyi sai naje na tambayi mummy, jabeer ya mike da sauri dan yasan yana zuwa ya tambayi mummy to fa bazata taba bari yayi sallah ba, da sauri ya rike hannunshi yace affan ni ke karya, ya fizge hannunshi yace eh mana kaine kake karya ya juya ya ruga cikin gida da gudu jabeer na kiranshi yayi banza dashi, dafe kai jabeer yayi cikin damuwa sai da yafi minti 5 tsaye sannan ya wuce ya tafi masallaci,,,, Jabeer ďinne ya fada maka haka, affan ya gyada kanshi yana daďa kwanciya jikinta alamun tsoro yakeji kar wuta ta kona shi, mummy tace rabu dashi makaryaci ne na fada maka ka daina kulashi kullum burinshi ya tirsasa maka yin abinda da bakayi niyya ba kuma ko a musulunce babu takura a addini, rabu dashi kaji affan din daddy tashi kaje kaci abinci kayi wasanka kaji, ya daga kanshi ya mike yana tsalle har ya karasa gurin cin abinci yana kiran sunan Hansa'u mai aikinsu tazo ta zuba mishi abinci, murmushi mummy tayi hade da ajiyar zuciya, Salma babar diyarta ta ajiye laptop dinta tace mummy wannan tsinannan jabir din so kawai yake ya ruguza miki plan dinki, kullum shi kenan maganar sallah sai kace wani sallau, mummy tayi dariyar mugunta ta kalli gurin da affan ke cin abinci duk yayi kaca2 da gurin amma ko digo bai diga a rigarshi ba saboda tsananin tsaftarshi, tace barni dashi ummu, jabeer yana wuce gona da iri tabbas zan san duk yadda zanyi in rabasu da affan in ba haka ba wata rana zai sa kwaba ta tayi ruwa, Fareedah tace wallhy I so much hate him sai ya dinga wani ďadďaga kai kamar kadangare shi a dole ga kyakykyawa mtsww taja tsaki, mummy tace ku barni dashi dani yake magana in yasan wata ay bai san wata ba..... Mrs tijjani shattima...... [15/12 09:32] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣ By Aysha Ya'u Kurah Da gudu ta shigo gida ta tarar da jarababbiyar kishiyar uwarta a tsakar gida tana fiffita, sannu da gida kawai tace bata jira amsa ba ta wuce ďakin kakarta Hajja Giďe, fadawa dakin tayi babu ko sallama ta cire skul Bag ďinta tayi wurgi da ita a kan gado sam bata kula da mutum a kan gadon ba ta fita da sauri ta shiga toilet, Hajja ta idar da sallah tayi tsaki tace wannan yarinya saidai Allah ya shirya yi hakuri jabeer, ya mike zaune yana murmushi yace zata sani ay bari ta dawo, hajja tace ay kai baka iya yi mata faďa sai dai kullum kace zata sani kullum kai ke kara sangarta ta, kafin yayi magana ta shigo ta ďane kan cinyar hajja tace hajjanah" sannu da gida, hajja ta tureta tace dalla ni sauka karki karya ni, sai a sannan idonta yakai kan jabeer dake kallonta baya ko kiftawa, da sauri ta mike tana murmushin jindadi ta zauna kusa dashi kamar zata shige jikinshi tace dama kana cikin dakin nan, ta shagwabe fuska tace shine kana kallon hajja tana tureni ko kayi mata magana kalli fa hannu na saura kaďan taji min ciwo, Hajja tace Allah ya kiyaye dai banji miki ciwon ba ko, ta turo baki tace kinso kiji min mana inaga ma dan kinsan yaya jabeer na nan ne shiyasa baki ji min ciwon ba, hajja ta kwashe da dariya tace to yau dai sharrin kaďan ne ko Allah nagode maka ma yana cikin dakin da yana zuwa nasan ce mishi zakiyi yau da kyar na barki da rai, jabeer ya kwashe da dariya, ta kwabe baki ta fashe da kukan shagwabe harda buga kai a gado, jabeer yace subhallahi me kuma akayi miki, hajja ta mike tace tabarar fa, ni bari kaga in fita dan in ina dakin nan zane yarinya zanyi, cikin kuka tace kaji ko wallhy bulala takemin kullum yauma dan ta ganka ne, jabeer ya haďe rai yace gaskiya hajja zamu kai kararki can kotun karshe a yanke miki hukunci, hajja tayi dariya tace mu fara shariar daga yau ma in dai akan AFEEYAH ne, afiyah ta dago kai ta harareta, jabeer yayi murmushi ya ciro hndky dinshi yana share mata hawaye, yace so sorry babynah, ya dago fuskarta ya kalli cikin idonta yace baki san kin girma da kuka ba, ta kara marairaicewa kamar karamar yarinya tace to baka ganin abinda takemin, yace to nace kiyi hakuri kinji, ki daina yarda suna saki kuka kinaso a dinga ce miki ruwa2, ta noke wuyanta tace ah'ah, yace to sai kin zama mai hakuri kin daina yawan kuka kinji, tace tam zan daina, yace yauwa wifey nah,, ya dakko ledar gefenshi ya fito dasu biscuits da chocolates, rungumeshi tayi cikin murna ta mishi peck a kumatu tace I love u so much hubbynah, wani abu yaji yana mishi yawo cikin kwanyarshi, a hankali cikin rashin kuzari yace more than u do babynah,, ta sakeshi tana dariya, nan suka cigaba da hirah cikin jindadi tana shan chocolates, sai da aka kira la'asar sannan ya fito zai tafi, rakoshi ta fito yi bayan yayi sallama da hajja,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61