Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 29

Chapter 29

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ďaki, oyizah ta boye tashin hankalinta tace sannu da gida "ya hajj" yace yauwa safiya kin dawo lafiya, tace lfy lau, ya kalli salma yace kun shiga gidan gaisuwan kuwa, suka turo baki suka ce yanzu zamu shiga da mummy, alhj basheer yace ya kamata bari in koma gurin zaman makoki, oyizah ta matso kusa dashi cikin kissa tace alhj ina ďana yake, alhj basheer yayi murmushi yace kice dan rigima, yana can wai shi bazai dawo gidannan ba sai an dawo mishi da abokinshi, oyizah bata san sanda tace to waye ya fitar dashi daga gidannan, alhj basheer cikin rashin fahimta yace ban gane ba, tayi dan murmushi tace naga ya ďade bai fita bane bana son ya fita shi kaďai wani abun ya sameshi, alhj basheer yace Ayya, baba ado mai gadi na fara turowa ya taho dashi saboda yazo yayi sallama da abokinshi duk da ba wani hankali gareshi ba, sai baba ado ya dawo yace wai yaki zuwa daga sunzo bakin gate sai ya juya a guje, shine naje da kaina na ďaukoshi dakyar yana ihu ya iya fitowa daga cikin gidannan, saida muka shiga gidan alhj bara'u sannan ya iya buďe idonshi, kuma kinsan ya gama tsorata da gidannan dan kiran namun daji kawai yakeyi wai gasu nan zasu cinyeshi a bakin gate, oyizah da gumi ya tsatsafo mata tace ayya my baby ni na faďa mishi in ya fita akwai animals da zasu cinyeshi saboda ina tsoron ya fita yaje wani abu ya sameshi, alhj basheer yace aiko ya tsorata sosai dan yace shi acan gidan alhj bara'u zai zauna nan gidan akwai lions da sauransu,, oyizah ta haďiye miyau tace yanzu zanje gidan ay sai mu dawo gida, alhj basheer ya ďaga kafaďa yace sai kinzo,, sama oyizah ta wuce tana huci, a zuciyarta tace alhj ya fara bata mata aiki, shikenan ya karya wannan kafin da ta daďe da yinshi, wanka tayi sauri tayi ta shirya suka wuce gidan rasuwa... Tun a kofar gida inda maza sukayi dafifi ana karbar gaisuwa gaban oyizah ya faďi saboda haďa ido da tayi da wani tsoho mai matsanancin kama da jabeer, saidai shi ya tsufa sosai, maida kanta tayi gurin Affan da ya lafe jikin tsohon yana tsotson hannu idonshi a lumshe, dakyar ta iya gaisar da mutanen gurin saboda irin kallon da tsohon nan ke mata, cikin gida suka shige ita da yayanta sai a sannan hankalinta ya kwanta, bayan tayi gaisuwa sama2 sai suka fito ta tsaya daga ciki ta aika farida ta kira mata Affan, farida ta wuce ta keta gurin mazan saboda rashin kunya tasa hannu zata fara bubbuga affan, da sauri tsohon nan ya tare hannunta yace ke lafiyarki, ta tsaya kerere tace mummy ce tace in kirashi mu tafi gida, ya kalleta sosai yace kice wai bacci yakeyi, farida ta turo baki ta juya taje ta faďa ma oyizah sakon wannan tsohon, hankalin oyizah ya kara tashi tace kuzo muje, suka fito, har ta fara tahowa gurin da suke sai ta canza hanya, farida tace mummy gasu can fa, oyizah tace kuzo mu tafi anjima zan sa a kirashi, sai a lokacin kaka liman ya ganeta, a zuciyarshi yace tabbas bazaki iya hada ido dani ba dan mugu na tsoron kwayar idona, ya shafa kan Affan a zuciyarshi yana kitsa abubuwan da zaiyi ta karkashin kasa ba tare da wani ya sani ba bare ta kara ajalinshi.... Oyizah na shiga gida ta fara safah da marwah tana sake2 a zuciyarta, fitar Affan daga cikin gidannan ba karamin tashin hankali bane a gareta, to wani tsoho ne wannan da ya firgita ganinta kamar wani aljani, yanzu shikenan Affan yana can gurin dubban mutane kuma tasan dole wasu zasuyi mishi addu'a, Noooo bazai yiwu ba ta fadi da karfi haďe da tashi ta kara fita daga gidan.... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣4⃣ By Aysha Ya'u Kurah Tun kafin ta karasa take kiran wayar alhj basheer bai ďauka ba saboda suna addu'a a gurin zaman makoki, tana karasawa taga maza sun kara yawa a gurin ta kalli gurin da tsoho da Affan suke bata gansu ba, cikin tashin hankali ta wuce cikin gidan kamar zata rusa ihu, a waje ta tarar da Amirah ta rako yan makarantarsu tace "ke" ina Affan yake, Amirah ta fara waige2 sannan ta juyo ta cigaba da magana da kawayenta, oyizah ta hassala tace ba da ke nake magana ba Amirah, Amirah tace ay bansan dani kike ba naji kamar "ke" kikace, yana ďakin yaya jabeer, oyizah ta harareta a hankali tace mara kunyar banza, ta wuce dakin jabeer, Kwance ta sameshi ya kura wa makeken hoton jabeer ido baya ko kiftawa, cikin fushi tasa hannu ta make kanshi da karfi, a zabure ya mike yana kallonta, hararshi tayi tace wuce muje gida, bai ďauke idonshi a kanta ba ya girgiza mata kai alamar baza shi ba, oyizah hassala matuka tace ni kake ma musu Affan, ya kara marairaicewa yace ni abokina nake jira, ta damko hannunshi tace dan ubanka wa ya faďa maka wanda ya mutu yana dawowa, wuce muje kafin in ji maka ciwo, ya noke wuya yace ni bazan tafi ko ina ba, ta janyoshi da karfi ta hankaďo shi waje, wani irin ihu ya saka ya ruga bayan Asiya da ke tahowa gurin, Asiya ta rikeshi tace me ya sameka Affan, Affan ya shige bayanta yana nuna mummy da ta taho tana huci kamar kumurci, tana karasowa ta kai hannu zata kara rikeshi ya kara sa ihun da ya maido da hankalin mutane da yawa gurinsu, Asiya tace me yayi miki ne wai, oyizah ta harareta zata kara rikeshi Asiyah ta rike hannunta tace wai me yake faruwa ne, ki kyaleshi mana ko dole ne, oyizah ta shaka sosai ta kalli yawan mutanen dake gurin zuciyarta na zafi saboda ganin Affan ya fara mata musu, ta kalli Affan fuskar nan babu annuri tace ka wuce muje gida, Affan ya noke wuya yace ni babu inda zani, Abida da rabon da tasa Affan a idonta tun kafin ya fara ciwo ta fito ta riko hannunshi tace zo muje ciki,, kaci abinci ko,? ya gyada kanshi tace to zo muje anjima abokinka zai dawo sai ya rakaka gida kaji, ya kara gyaďa kanshi cikin murna suka fara tafiya, da sauri oyizah tasha gaban Abida tace sakeshi tunda babu abinda kika haďa dashi, Abida tayi mata kallon banza tabi ta gefenta ta tura Affan gaba suka wuce yana waigen mummy dake mishi wani irin kallo, masifa ta fara yi tana zage2 kamar tababbiya dan gani takeyi zasu bawa Affan maganin da zai maido mishi da hankalinshi ya tona mata asiri, dakyar suwaiba ta rarrasheta suka wuce gida suna kulla munafurcinsu.. Kuka sosai oyizah keyi a gaban alhj basheer akan ita a dawo mata da ďanta, ta share hawayenta tace shekara uku kenan ina wahala dashi sai yanzu zaka barshi can wani guri kace ya kwana, wallhy alhj bazan iya yin bacci ba yau in affan bai dawo gida ba, alhj basheer ya juyo yace haba safiya, na yau dai kaďai sai kace wanda zai zauna a can dindindin, ta harzuka tace kasan abinda zasu bashi yau ďin,

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});