Chapter 49
Chapter 49
nata da alhj yasa a fitar dasu daga cikin gidan, duuffffffff taji saukar mutane akanta suna maida numfashi, da sauri ta hankade farida da Afeeyah ta kalli su tanimu tace lafiya kuka shigo min parlour, a ruďe farida tace mummy kifayen nan sun bace a cikin kwanon da aka sasu....... Mrs tijjani shattima..... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣5⃣ By Aysha Ya'u Kurah Zaro ido oyizah tayi tace kamar yaya sun bace, Afeeyah ta kalli alhj basheer da ya fito yana gyara hula tayi saurin cewa wallahi bacewa sukayi mummy, haba shiyasa suke tsorata ni cikin dare ashe ba kifaye bane, alhj basheer ya karaso da sauri yace kifayen ne suka bace, oyizah ta galla ma su Tanimu harara sum sum suka fice ta juyo ta kalli alhj basheer tace iskancin su ne ni nace ma wanda ya kwashe kifin ya dauka na bashi shine dan basu gansu ba suke tunanin sun bace, to ina zasu, Fareeeda tace wallhy tall--- oyizah tayi saurin katseta tace dalla rufe mana baki, shekarun su nawa a gidannan kin taba ganin sun bace, dallah ku wuce ku ba mutane guri, Afeeyah ta ja hannun Affan da jikinshi ke kyarma suka wuce daki a zuciyarta tace 99days 4 the thief muje zuwa, Allah dai ya kara bani sa'a... Tun karfe hudu na yamma oyizah ke gurin chummy cikin matsananciyar damuwa tana faďa mata anyi destroying fishpond dinta na tsafi, dariya chummy tayi sannan ta buga kasa nan take ya tsage ruwa haďe da kifaye suka fara fitowa daga ciki, saida suka gama fitowa tsaff sannan suka haďe kansu guri ďaya, oyizah tayi murmushin jin dadi tace ashe suna nan, har hankali na ya kwanta, bacewarsu ba karamin daga hankali na yayi ba dan ba karamin taimako na sukeyi ba, chummy tayi dariya mai karfi tace fitarsu a gidanki tonan asirinki ne saboda haka kisan duk yadda zakiyi ki mayar dasu gidan nan Affan ya dinga ganinsu kullum, oyizah tayi tagumi tace ta yaya zan mayar dasu bayan alhj da kanshi yace a fitar dasu, yanzu ina komawa dasu zai fara zargin wani abu, chummy tace karki damu, akwai abun da zan baki kisa mishi a abinci daga yaci shikenan ko yagansu hankalinshi bazai kawo su bane, oyizah tayi dariyar jin daďi tana faďin thank u my lord,, mikewa oyizah tayi ta shigo da wani yaron da zasu sha jininshi a gurin meeting, da ganin yaron kasan mugun takadiri ne dan ko gezau baiyi ba idonshi a soye babu alamar hawaye, dakyar ya tsuguna a gabansu, chummy ta harareshi sannan ta umurceshi da ya miko mata kafafuwanshi, tirjewa yayi yaki mikowa, babu yadda batayi ba akan ya miko kafafuwanshi tayi wani aikin dasu yaron nan yaki, kwala kiran BULADUNA tayi nan suka shigo shida abokin aikinshi, cikin isa ta umurcesu da su kamo yaron su kawoshi gabanta, da karfinsu suka fara kokarin kama shi yana tirje musu yana tokarinsu da hannu, sai sun daukeshi sunyi sama dashi sai yasa iya karfinshi ya zille ya fado kasa, daukar da sukayi mishi na karshe ne yasashi wani irin kukan kura ya hankaďe buladuna yayi baya, tartsasssssss sukaji dukansu suka duba gurin da sauri, glass din da fanne da fanna ke ciki ne yayi tarwatse ya bullo tun daga bayan buladuna har cikinshi, nan take ya fadi kasa matacce, da sauri su chummy suka yo kanshi suna kiran sunanshi, su kuwa su fanne cikin azama suka fito cikin glass suka nufi gurin yaron da aka kamo da niyyar taimaka mishi ya gudu, cikin tausayawa yace ku meyasa bazaku zo mu tafi tare ba, fanne cikin sauri tace mu matattune gawar mu ta dade a rami kai kuwa ba'a riga an birne gangar jikinka ba kayi saurin komawa gida, da sauri yace waye ya kawo ku nan, fanna tace mahaifin mu ne Alhj sambo ministern Abuja na yanzu, kafin yaron yayi magana ya hango su chummy sun doso su suna kokarin kama su fanne, da sauri kurwar yaron tabi ta inda su fanne suka nuna mai ya bace daga gurin, cikin kunan rai chummy ta ciro sandar tsafinta ta fara nuna su fanne dashi, zagayen dakin suka farayi har suka kai inda kwalbar gunkin zeenatu take, da sauri fanne tasa hannu ta dauki kwalbar, wani irin ihu oyizah tasa tace karki fasa, karki fasa, zan taimakeku in maida ku gidan ku, fanna tace fanne fasa da sauri saboda mu dama a mace muke gurin wa zata maida mu, kafin chummy ta cimma fanne har ta fasa wannan kwalbar ta karya gunkin ciki, zama oyizah tayi a gurin tana girgiza kanta tana fadin shikenan, shikenan my lord, sai da nace miki mu gama da yaran nan saboda nasan zasu iya zame mana matsala, yanzu nasan duk inda zeenatu take ta farfado, chummy bata ba oyizah amsa ba saida ta tabbatar ta kwantar da fanne da fanna sannan tace yau dinnan zan gama dasu, ki kwantar da hankakinki dan sun fasa kwalbar a banza dan babu wanda yake tunata bare har yayi mata adduar da zaisa ta gama dawowa hayyacinta,, yanzun nan zan kara yin aikin da yafi wancan akanta, oyizah ta saki ajiyar zuciya tace nagode my lord.. Afeeyah na zaune tana lazumi, tunda ta idar da sallar la'asar bata tashi daga kan daddumar ba sai gurin biyar, shafa addu'ar tayi ta mike ta nade daddumar sannan ta zauna a kasa a gefen gadonta ta tura hannunta karkashin gadon ta zaro zanin da ta kunshe damon nan a ciki, a hankali ta warwareshi ta nade hannunta da leda cikin dakewar zuciya ta fara kakkabe kasar tana kokarin bude bakin damon, cikin sa'a ta budeshi sai wari yakeyi ta karkatar da bakin ta girgizah shi, nan wata katuwar laya ta faďo kasa, da sauri ta ajiye wannan damon ta naďeshi cikin zanin ta dauki layar ta warwareta, babu abinda ta gane a cikin rubutun sai sunan zeenatu, nade layar tayi ta mike ta fita da wannan damon ta kulleshi a leda takai main bolar gidan sannan ta dawo ta kona layar ta tattara tokar ta zubata a magudanar ruwa... ★ Magaryah Nijar★ Indo!!! tankaďen ne har yanzu baki gama ba, baki gudun malam ya dawo ya tarar ba'a gama abinci ba, wane irin shashanci ne wannan, nda tashi ki ban guri sai shegen Nawar tsiya, indo ta turo baki ta mike tayi hanyar waje, Sallamar da akayi ne ya tsayar da ita, da sauri ta rungumeta tana faďin "Tanti Gaje" sannu da zuwa, Gaje tayi dariya tace sakan ni yar Magaryah ya na same ku, indo tace kalau muke sai dai har lau Tanti Ayyu na nan da masifarta, Gaje tayi dariya ta karasa cikin gidan tanti ayyu ta mike tace maraba da gaje mutan jigawa, gaje tace ina wuni Ayyu, ayyu ta amsa tana shimfiďa mata tabarma tace ya jigawar, ay tun shekaran jiya muke zuba ido shuru, Gaje tayi murmushi tace mun yi sabga ne a kazaure dan haka baki ganni ba, ya kokari ya kuma mai jikin an samu cigaba kuwa--- kafin Ayyu tayi magana wani razananen ihu ya fito daga ďakin majinyaciyar ya ziyarci kunnuwansu, kallon kallo suka fara yi sannan suka mike da gudu suka shiga dakin har suna bige juna, zama
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61