Chapter 52
Chapter 52
kaita, ya dade yana treatn dinta yiyi dressn ciwukan dake jikinta,, oyizah ma ta je wata nurse tayi mata dressn sannan ta wuce dakin da Afeeyah take, zaune ta samu Affan ya kwantar da kanshi akan hannun Afeeyah yana kuka alhj basheer na tsaye a kansu yana rarrashinshi, tsaki tayi a hankali ta karaso gurin tace alhj ya kamata kuje gida ni sai in kwana anan, Affan yayi saurin dago kanshi ya noke wuyanshi yace um um nima zan kwana, oyizah tayi dariya tace ya za'ayi mai jinya yayi jinya, kai da ba wani isashshen lafiya gareka ba ina kai ina jinya, Affan ya kara fashewa da kuka yace ni babu inda zani, alhj basheer yace to duk babu inda zamu a nan zamu kwana, oyizah ta ja baya cikin bacin rai ta watsa ma Affan harara a zuciyarta tace shege mayatacce ka kusa daina ganinta kwata2..... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:38] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣8⃣ By Aysha Ya'u Kurah A tsaye suka kwana a kanta babu wanda ya runtsa, oyizah taki runtsawa ne saboda tana jiran su alhj basheer su rufe idonsu ta ida mugun nufinta akan Afeeyah, alhj basheer kuwa yaki runtsawa ne saboda ganin Affan bai runtsa ba kuka kawai yakeyi wanda babu wanda a cikin su yasan dalilin yinshi har ni da nake dauko muku rahoto, karfe 6 doctor ya iso, dakin Afeeyah ya shiga suka gaisa da alhj basheer yace bata farfado ba har yanxu, alhj basheer yace ko motsi bata yi ba doctor da fatan dai ba wata gagarumar matsala bace, doctor musah ya bude idonta a hankali yace buguwa ce kawai tayi sai wadannan ciwukan, ya akayi ta samu wadannan raunin haka alhj, alhj basheer cikin damuwa yace ina ganin gamo tayi cikin dare dan ni ihunta kawai naji na fito na sameta a sume ina fatan dai bai taba lafiyar cikinta ba ko doctor, doctor musah yace dakyar ne alhj dan buguwar a kai tayi amma anjima zanyi scanning dan tabbatar da lafiyar shi, alhj basheer yace Allah yasa muji alkhairi, doctor musa yace Ameen alhj sannan ya fita, oyizah tace alhj ya kamata ku tafi gida kuje kuyi wanka sai ku kawo mana abin kari ko, alhj basheer ya dafa kan Affan yace tashi muje gida ka dan yi bacci ka huta anjima sai mu dawo, Affan ya ďago idonshi da ya kumbura ya girgiza kanshi yace kaje daddy, alhj basheer yace haba Affan baka ganin yadda idonka yayi nasan ka gaji kuma bacci kakeji, kayi hakuri kazo muje kaji, Affan ya mike yana murza idonshi ya fita ba tare da ya kalle su ba, saida alhj ya dan dade a ciki sannan ya fito ya samu Affan a mota ya daura kanshi kan murfin kofar, shiga yayi ya tada motar suka wuce... Suna fita oyizah rufo kofar ta dawo gurin Afeeyah tana dariyar murna, pillown kan Afeeyah ta cire tana fadin yau taki ta kare, yau zan karar da duk wata matsalata in huta da bakin ciki, tana daura pillown kan Afeeyah taji an murďa kofar, da sauri ta zauna ta zame pillown tana dariya tace doctor ka dawo, doctor musah ya kalleta sosai yace eh na dawo, nazo daukarta muje ayi mata scanning daga nan zata wuce resting room, zaifi kyau ki tafi gida hajiya saboda bama yarda kowa ya shiga dakin hutu in ba likita ko nurse ba, oyizah tayi mishi wani irin kallo tace kana nufin ita kadai xamu bari a asibitin babu wanda zaiyi jinyarta sai kace marar gata, doctor musah yace haka ka'idar take hajiya baki ga conditn din da take ciki ba, oyizah ta fara masifah tace wallhy baka isa ba, babu inda zaka kaita haka kawai zaka wani zo kayi min iyayi anan, to anan zaka barta tunda ko ina ka kaita Allah ne zai bata lafiya ba kai ba, yayi mata wani irin kallo sannan yasa aka shigo da wani gado yace hajiya aiki na nakeyi tunda ba ke kike biyana ba dan Allah ki barni inyi aiki na, ya kalli nurses din yace ku daura ta muje, suka kinkimeta suka daurata akan gadon, rike gadon oyizah tayi tana ta bala'i tana wallhy baza'a tafi da ita ko ina ba, mutane suka taru a gurin anata bata hakuri amma tace ita sam babu inda za'a tafi da ita, doctor musah da kanshi ya amshi gadon yasa iya karfinshi ya fara turawa oyizah na binsu tana bala'i kamar zararriya, dr musa bai tsaya a ko ina ba sai office dinshi, da karfi ya bude kofar ya tura gadon haďe da bangajeta ta fadi kasa yayi saurin shigewa ya datso kofar,, wani sabon bala'i oyizah ta dasa ta dinga masifa cikin daga murya, babu wanda ya kalleta a asibitin kowa harkar gabanshi yakeyi saboda su a ganinsu mahaukaciya ce in ba mahaukaci ba waye zaiyi wannan daga cewa za'a kai patient resting room, ita kuwa oyizah musabbabin tashin hankalinta shine yanzu Afeeyah tasan ita wacece in har tabar Afeeyah ta kara kwana a doron kasa to tabbas asirinta zai tonu dan zata iya farkawa a ko da yaushe, (oyizah bata san ba tun yau Afeeyah tasan ko wacece ita ba, kuma bata san bayan Afeeyah akwai mutanen da suka san ko wacece ita kuma suna nan tunkarota cikin kankanin lokaci ) sai da ta gaji da masifar dan kanta sannan ta wuce gida cikin kunan rai... Tana isa gida ta faďa ma alhj karya da gaskiya akan abun da doctor musah yayi mata, alhj basheer yace safiya mutumin nan fa aikin shi ne ya fiki sanin abinda ya dace, oyizah tace babu abinda ya sani alhj kawai mu canza mata asibiti, alhj basheer ya girgiza kanshi yace babu inda zan kaita a can zata zauna har Allah ya bata lafiya, in ma yace kar wanda ya kara zuwa gurinta to na yarda dan nasan zai kula da ita sosai, oyizah ta tsaya tana kallon alhj basheer tana huci kamar bakar zakanya, mikewa yayi ya fita daga gidan gaba ďaya ya barta tsaye kamar zata kurma ihu... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:38] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣9⃣ By Aysha Ya'u Kurah Kwanan Afeeyah uku a asibiti bata farfaďo ba, a cewar doctors buguwa tayi sosai kuma suna iyakacin kokarinsu gurin ganin ta farfaďo nan da yan kwanaki, babu wanda ke zuwa dubata daga gida sai alhj basheer da Affan da har wannan ranar bai bar zubar da hawaye ba, ba karamin damuwa alhj basheer yakeyi ba akan yawan kukan Affan, gani yakeyi kamar yin kukan yanada nasaba da ciwonshi, saida doctor musah ya kwantar mishi da hankali yace babu abinda ke damunshi may be ciwon matarshi ne ke sashi yawan kuka, alhj yayi dariya da dr musa ya fada mishi haka, yace yanzu wannan da kwakwalwrshi bata da amfani har yake iya yin kuka dan wani nashi baida lafiya, kenan yasan zafin ciwo kuma yasan meye damuwa,, doctor musah yace me zai hanashi yin kuka, alhj ni fa har yanzu kana bani mamaki akan wasu abubuwa da ka kasa fahimt-- wani irin kallo Affan yayi ma doctor musah nan da nan yayi saurin canza magana yace kamar ciwon Affan ka kasa fahimtar kullum yana samun cigaba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61