Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 38

Chapter 38

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dai inaso insan ko kayi wankan tsarki, yace eh nayi wanka sosai jikina yanata kumfa, yanata kumfa, yanata kumfa na koma fari sosai, tayi dariya tace to sallah fa, nan ya kirne fuska yace ai ni bana sallah, Afeeyah ta kwalalo ido waje tace la haulu, baka sallah, saboda me,? Kafin yayi magana sukaji muryar oyizah a bayansu tana cewa saboda ubanki bai koya mishi ba..... Mrs tijjani shattima... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣3⃣ By Aysha Ya'u Kurah Afeeyah ta sunkuyar da kanta da sauri kirjinta na dukan uku2, Affan ya kalli oyizah yace mummy dama saboda babanta bai koyamin ba shiyasa bana yi, oyizah ta mika mishi cup din hannunta tace amshi maganinka kasha rabu da wannan kinibabbiyar, Affan ya karbi ruwan asirin da ya saba sha kullum ya fara sha ya miko ma Afeeyah yace kema zaki sha, Afeeyah ta girgiza kanta ta mike zata wuce oyizah ta janyo hijabinta tace dawo nan ban gama dake ba, ta kalli Affan tace tashi ka kai cup din kitchen sai kaje kayi wasanka, Affan ya mike yana yafito Afeeyah da hannu yana cewa zo muje ki tayani buga game, oyizah tace a'a jeka kayi wasanka zata zo ta sameka, ya wuce da gudu yana dago ma Afeeyah hannu, Wani irin kallo oyizah tayi ma Afeeyah sannan tace jiya me nace miki game da Affan,, Afeeyah ta sunkuyar da kanta kasa tace dan Allah kiyi hakuri, oyizah taja kunnenta da karfi tace hakurin uban me kike bani, bance miki kar ki shishshige ma Affan ba? bance miki karki shiga rayuwarshi ba, ohhh wato kema zaki fara tursasashi akan sallah kamar yadda ďan iskan saurayinki yayi ko? Afeeyah ta runtse idonta zuciyarta na zafi saboda kiran jabeer dan iska da oyizah tayi, Rankwashi mai karfi ta sakar mata akai tace zan miki kashedin karshe, kashedin da idan kika ďauka kin tseratar da kanki daga fushi na, anyi na farko anyi na karshe tsakaninki da Affan, kin fahimci abinda nake nufi ko sai na warware miki? , Afeeyah tayi shuru kirjinta na tsananta bugawa, oyizah tace to ina nufin kwana ďaki daya ke da shi, anyi ta yanke ta gille tsakaninku, wallhy kinji na rantse duk ranar da kika kara yarda Affan ya shigo dakinki har kika barshi ya kwana, hmmm faďin hukuncin da zan miki ma bata baki ne kina jina ko? Afeeyah ta gyaďa kanta tace eh inaji, oyizah ta saki hijab dinta ta kara kai mata duka a kai tace bace min a gaba ko in illata ki, da sauri Afeeyah ta wuce daki tana kuka****** Bayan hajja ta gama rarrashinta ta zuba mata abinci ta karba ta fara turawa da sauri saboda azabar yunwar da takeji, cikin tausayawa hajja ta fara bata baki cikin hikima da kalamai masu taushi, sai da ta tabbatar da hankalinta ya kwanta sannan ta tashi tafi gida cike da tausayin yar jikarta da ta fara dandana rayuwar duniya, dan da sam Afeeyah bata san bacin rai ba kullum cikin farin ciki take in ka ganta tana kuka to na shagwaba ne, babu wanda zai taka ta ta barshi bare har ya daura mata bacin rai duk wanda yayi mata take zata mayar mishi ta wuce hankalinta kwance.. Haka rayuwar Afeeyah ta kasance cikin kunci da bauta, wulakanci kala2 babu wanda bata gani, sam bata bari Affan ya ganta ko yazo yana bubbuga kofarta bata budewa, ba karamin tausayi yake bata ba in ya fara buga kofar dan baya bugun hankali yana bugata yana ihu wani lokacin ma harda kukanshi, abinci kuwa saidai hajja ta kawo mata dan bata nasu, duk wannan wainar da ake toyawa alhj basheer bai sani ba saboda baya gari, A ranar da ta cika sati uku a gidan tana tsaye tana mopping dining room, oyizah da suwaiba suna zaune cikin parlon suna gulmarta, suwaiba tace lallai yarinyar nan ashe duk iskancin da take mana guri ta samu, ji yadda take muku bauta kuma duk zagin da kuke mata ta kasa tabuka komai, oyizah tayi dariya tace ay wargi ma guri ya samu, ni yaushe kamar wannan yarinyar zata tsaya min a gaba, ai wallhi kema suwaiba harda laifinki, suwaiba tace ai da dinma daurin gindi ta samu to yanzu mai shagwabatan ya mutu shiyasa shegen bakinta ya mutu, oyizah tace ai ko shugaban kasa ne ya tsaya mata bata isa ta min ba bare wannan tsinannan yaron mai shegen girman kan tsiya.. Afeeyah ta yar da mop din hannunta ta runtse idonta zuciyarta na tafarfasa, muryar salma taji a bayanta cikin isa da gadara tace kee.. je kiyi min pepper soup mai yaji sosai yanzu nan ki kawo min, Afeeyah bata juyo ta kalleta ba ta tsalleke ruwan da take mopping dashi ta kama hanyar side dinta, da sauri salma ta bita tana huci taja rigarta ta baya har saida wuyan ya yage tace ke dan uban--- Afeeyah ta juyo cikin azama ta dauketa da gigitaccen marin da ya hanata karasawa yasata sakin Afeeyah bata shirya ba.... Mrs tijjani shattima..... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣4⃣ By Aysha Ya'u Kurah A firgice oyizah da suwaiba suka yo kan salma dake rike da kunci idonta yayi jajur, fuskarta oyizah ta ďago tana shafawa ta kalli Afeeyah murya a sarke tace m-ari, suwaibah ta jinjina kai a munafurce tace tabdijam, lallai yarinyar da tsaurin ido kike, ki kalli girman salma ki dauketa da irin wannan marin, Afeeyah taja tsaki ta juya zata wuce oyizah ta saki salma ta janyota da karfi tana huci, ihun da Afeeyah ta saki yayi daidai da shigowar alhj basheer parlon, da sauri ya karaso yace subhanallahi lafiya safiya, me tayi miki, oyizah ta saki Afeeyah da sauri ta juyo ta fara hawaye tace alhj ace kamar yarinyar nan ta dubi salma ta tsinka mata mari, Afeeyah ta durkushe ta fashe da kuka tace dan Allah daddy ka kaini gurin hajja, wallhy kasheni zasuyi, dukana sukeyi kullum, yanzu ma dukana suka gama yi har suka yaga min riga, dan Allah ka kaini gurin hajja, kafin alhj basheer yayi magana mahmud dan suwaiba ya shigo rike da kular abinci a hannunshi, ta gefen ido Afeeyah ta hangoshi cikin muryar kuka tace mamu kai min daki ka dauko kular jiya, alhj basheer cikin mamaki yace meye a cikin kular nan, Afeeyah tace abincin rana na ne, alhj basheer cikin tashin hankali yace duk abincin dake gidan nan sai an kawo miki abinci daga gida, oyizah da ta gama tsurewa tace umm al--- Afeeyah ta katseta da sauri tace sunce abincin gidan nan ba na talakawa bane wai ban saba cin irin shi ba saboda haka kar in taba musu, oyizah ta sankare cikin mamakin sharrin da Afeeyah ta lafto musu, alhj basheer ya juya ya kalleta cikin tuhuma tayi saurin cewa wallhy karya take min alhj, ya za'ayi in hanata abinci, alhj basheer ya kalli mahmud yace kai tun yaushe kake kawo ma Afeeyah abinci, mahmud yace kullum nake kawo mata da safe da rana da daddare, alhj basheer ya saki salati yace kin kasheni safiya, kin tozarta ni a unguwar nan, yanzu kowa ya gama sanin sirikata daga gidansu ake kawo mata abinci, oyizah tace wallhy alhj kar---rufe

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});