Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

Chapter 21

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kallo, fuskarshi ya fara shafawa yana share mishi hawaye yace naji maka ciwo ne, ya ďaura hannunshi a kan jabeer yace yi hakuri kadaina kuka zo muje kaga kayan wasa na, kaima kana so ko? jabeer ya gyada mishi kai hawaye na fita a idonshi, Affan ya ďan bata fuska yace to ka daina kuka zan baka wasu sai ka tafi dasu kaji, Jabeer ya kasa daurewa ya saki hannun Affan ya fita daga gidan da gudu yana kuka sosai, Affan ya bata rai sosai kamar zaiyi kuka ya kalli daddy yace daddy kaga ya tafi yana kuka ko, kuma ay na bashi hakuri bansan zaiji ciwo ba, ka bishi ka dawo min dashi muyi wasa kaji,, alhj basheer ya share kwallar da ta zubo mishi yace zai dawo yanzu affan yaje ya siyo maka abin dadi ne, Affan ya daka tsalle yace daddy kace mishi ya taho min da sweets dinnan masu dadi, alhj basheer yace karka damu affan je ka cigaba da wasanka, Affan ya gyaďa kai cike da murna ya koma gurin kayan wasanshi.. Salma da fareeda suka mike kunshe da dariya suka wuce daki, suna shiga suka saketa kamar tababbu, fareeda tace salma kiga yadda affan ya koma kamar dan yaye, salma tace ni ba karamin dariya yake bani ba, ji wani kwallin da mummy tasa mishi a ido dan Allah, fareeda tace ay ni yanzu na samu film din kallo wanda zai dinga sani nishadi, salma tace ke ko ni, suka kara kwashewa da dariya... Jabeer bai dawo gidansu affan ba sai can da yamma, idonshi a kode saboda tsabar kukan da yaci, a waje ya sameshi yana buga kwallo, affan na ganinshi ya rungumi kwallonshi ya rugo da gudu zai rungume jabeer sai kuma yaja ya tsaya saboda tunanin kar ya kara sashi kuka irin na dazu, jabeer yayi murmushi ya buďe hannunshi, affan ya kwashe da dariya sosai ya shige jikinshi yace yanzu banji maka ciwo ba ko, jabeer yace ehh friend, Affan ya ďago kanshi yace ina abin dadin da daddy yace zaka siyomin, jabeer yasa hannu a aljihu ya fito da chocolates ya mika mishi, tsalle yayi ya dane jikin jabeer yana murna ya karba yace bari in nuna ma mummy dan tace duk wanda ya bani abu in nuna mata kafin in ci, bai jira jin abinda jabeer zaice ba ya ruga ciki da gudu, jabeer ya rungume hannunshi yana girgiza kanshi a zuciyarshi yana kara jin tsoron Allah mai maida bawanshi yadda yaso a kuma lokacin da yaso,,, Tun daga ranar kullum jabeer ya taso aiki zai tsaya a gurin affan suyi hirarsu yayi ta mishi shirme, in lokacin sallah yayi duk yadda zai buga ya raya affan yazo suje zaiki yace sai ya tambayi mummy, daga yaje ya tambayeta zata hanashi ta tsoratar dashi sosai, da taga kullum jabeer na matsama affan akan sallah sai ta bijiro da kokarin rabasu, da farko tayi nasara dan kuwa ko jabeer yazo bata barin affan ya ganshi, da affan yaga har sati daya baiga abokinshi ba ya ďaga musu hankali sosai a gidan duk irin tsoron da mummy ta bashi bai shigeshi ba shidai kawai a kira mishi abokinshi abinda yake fadi kenan, da taga kullum bashi da aiki sai kuka kuma baya cin abinci sai tasa masu gadi su nemo mata jabeer dan in alhj ya dawo ya tarar dashi a haka to bazai mata da kyau ba.. Duk irin tururuwar da mutanen unguwa keyi a kofar gidan zuwa gaida affan basu samu shiga ba dan ko kofar masu gadi basu buďe musu, hakan yasa mutane suka hakura da zuwa gaisheshi saidai in sun hadu da alhj basheer suyi mishi jaje a waje, maganar zeenatu kuwa banda yan'uwanta da su Abida babu wanda ke tunawa da ita addu'a kuwa kullum yinta sukeyi akan Allah ya bayyana ko gawarta ne.. Oyizah kuwa likkafa taci gaba don ba kananan kudi takeci da ciwon affan a guri alhj ba , duk bayan sati daya da kudin da yake bata da sunan ana ma Affan saukar alqur'ani da rubutu, amma bai taba maida hankali gurin ganin affan yasha rubutun a gabanshi ba saboda ya yarda da oyizah 100%, haka in malam Atiku ya bashi rubutu a bawa affan ko jabeer ya amso mishi sai dai daddy ya bata yace ta bashi yana fita zata zubar dasu tayi ta musu tofin Allah tsine... Abinda yafi ďaga mata hankali yanzu shine ta rasa inda Affan ya ajiye takardun kadarorin da alhj ya bashi, kullum zata zaunar dashi a siyasance tace ya dauko mata takardun da alhj ya bashi, cikin rashin fahimtar abinda take nufi zai tashi yaje ya tattaro duk takardun dakinshi ya kawo mata, babu irin duban da batayi ma dakinshi da na zeenatu ba amma sam bata gansu ba,, gashi tana tsoron tambayar alhj basheer dan kar ya harbo jirginta, haka ta saduda da tunanin in alhj ya mutu dukiyar duk nata ne da ya'yanta dan ko Affan ma mallakinta ne.... Wannan shine mafarin ciwon Affan da yanzu yake cikin shekara ta uku cikinshi, a wannan shekarun ko sau ďaya affan bai taba fita da kafafuwanshi ba sai dai a kaishi checkup a mota tare da oyizah amma fita shi kadai sam bata yarda dashi ba dan ba karamin kafi tayi mishi ba, Salma da farida kuwa maidashi sukayi kamar toy haka zasu tasashi a gaba suyita dariya in yana shirmenshi... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣6⃣ By Aysha Ya'u Kurah ☆ cigaban labari ☆ Gida jabeer ya tafi bayan sun gama hira da hajja da Afee akan lalurar Affan, yana shiga ya wuce parlon mahaifinshi, zaune ya samesu da ummi ya gaisar da babanshi ya amsa fuskarshi dauke da fara'a yace ya jikin abokin naka, jabeer yace alhmdullih baba, Abida ta kalleshi tace ina Afeeyar take shine ta tafi babu ko sallama, jabeer yace ai ummi taga kina bacci ne shine muka shiga gurin affan tare, Alhj bara'u ya kalleshi sosai yace jabeer yaushe Afeeya zata fara jarabawa, Jabeer yace next uppr week zasu fara, alhj Bara'u yace hasashena ya zama gaskiya kenan, mun zauna da malam atiku mun tattauna game da maganar aurenku ni in sona ne ma ayi kafin ta zana jarabawar, Abida tace haba alhj ay gaggawa ba namu bane ina laifin in sun gama da sati ďaya, alhj bara'u yace to koma yaushe ne Allah ya kaimu dan na kosa in aurar da jabeer, Abida tace kace dai ka kosa kaga yan jikokinka, alhj bara'u ya kwashe da dariya yace ma jabeer ya tashi ya tafi, jabeer ya fita shima yana dariya.. Cikin ikon Allah aka tsayar da ranar Afeeyah da jabeer kamar yadda Abida tace, murna a gurinsu ba'a cewa komai babu wanda zai iya gane wanda yafi murna a cikinsu, shiri jabeer yakeyi sosai da planning din yadda zasuyi rayuwarsu da Sweet Afee dinshi da ya'yan da zasu haifa tare, duk shirin da yakeyi bai hanashi zuwa gurin Affan ba kullum suna tare da yamma kuma kullum sai Affan ya tambayeshi ina barbie dinshi, jabeer shirme yake maida abin saboda yasan bayi da isashen hankali, da jabeer yaga abin na Affan bana karewa bane sai yake zuwa ya dauko

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});