Chapter 41
Chapter 41
ko runtsawa baiyi ba, ana kiran sallar asuba yaje yayi sallah ya wuce gidan malam atiku, hajja a firgice ta fito idonta ya ciko da kwallah tana tambayar wane asibiti, alhj basheer yace ki kwantar da hankalinki hajja, safiya na can zaune da ita ba sai kin je ba, hajja tace inaaa aiko sai naje wallhy, ai kowane aiki da wakilinshi bazamu daura mata nauyin jinya ba, malam atiku yace Baba ay tunda yace kar--- tayi saurin katseshi tace walhi danbaba babu abinda zai hanani zuwa gurin hajara, alhj basheer yace to shikenan hajja muje, tayi saurin sa takalmi jiki na rawa ta bishi, Suna isa asibitin suka tarar oyizah na bacci Afeeyah kuma bata farfaďo ba har lokacin, gefenta hajja taje ta zauna tana kuka tana tofa mata addu'a, alhj basheer yace ki kwantar da hankalinki hajja babu abinda zai sameta bari muje gida a kawo muku abinci, hajja tace to sannu alhj an gode, alhj basheer yace haba ai yiwa kai ne nima ay yata ce, ya kalli gurin da oyizah ke bacci ya dan bubbugata tayi firgigit ta farka tace "an gama komai ko" alhj basheer yace me aka gama, oyizah ta fara goga ido tace na dauka doctor ne, alhj basheer yace bashi bane ki sameni a mota mu wuce gida, dakyar ta gaida hajja sannan tabi bayan alhj basheer suka wuce gida... Alhj basheer na shiga parlor ya tarar da Affan zaune a kasa ya haďe kai da gwiwa yana kuka sosai, da sauri ya karasa kusa dashi ya dagoshi yace meya faru dan gidan daddy, Affan ya kwanta kan jikinshi yace daddy tun dazu nake neman Afeeyah ban ganta ba na duba ko'ina bata nan naje gurin mai gadi yace kai ka dauketa ka fita da ita, daddy ina kuka kai ta? Oyizah tayi saurin matsowa kusa dashi tace sorry my baby Afeeyanka taje siyo maka abun dadi zo muje kayi wanka kafin ta dawo kaji, cikin rashin gamsuwa da kalamanta yace mummy karfe nawa zata dawo, oyizah tayi murmushi tace 10 zata dawo kaji, Affan ya gyada kanshi, tace yauwa baby muje kayi wanka kasha magani ko, taja hannunshi suka wuce zuciyarta wasai dan jiya kadai Afeeyah ta kusa daura mata hawan jini yanzu kuwa zata ci karenta babu babbaka tunda ta tafi 4 good.... Goggo ta kalli kaka liman bayan ya gama karyawa tace sai tafiya ko, ya goge bakinshi yace in shaa Allahu ai yau "ta dabo' tayi kirah, goggo tace da ka bari sai gobe saboda akwai daddawa da dawo da zaka tafin ma da Abida dashi, kaka liman yace ai ciwo ko mutuwa ne kadai zai hanani isa ta dabo yau, Ke bazan ma iya bacci ba in banje ba, tace to Allah dai ya tsare wannan tafiyr ta gaggawa, yace ameen ke kike ganinta haka ni kuwa a guri na ba gaggawa bace saboda na dade ina sa rana banje ba, mafarkin da nayi jiya shi ya tabbatar min da wannan lokacin ne lokacin sa'a a garemu, Goggo tace to Allah ya bada sa'ar wannan sirrintaccen aikin da ko ni kaki yarda ka fada min, kaka liman yayi dariya yace ameen ta liman, aikin ne saida sirri, tace haka ne ai sirri a komai ma yana da kyau Allah ya dawo daku gida lafiya, ya mike tsaye yana faďin ameen ameen, har zaure ta rakashi inda drivernshi da alhj bara"u ya ajiye mishi yake jiranshi, saida suka sha mai a filling station sannan suka dauki hanyar KANO TA DABO TUMBIN GIWA..... Mrs tijjani shattima....... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: [7:13PM, 05/04/2016] Ummu Nan: ◆◆ RABO AJALI◆◆ 4⃣7⃣ By Aysha Ya'u Kurah Tiryan tiryan abubuwan ke dawo mata cikin kwakwalwarta, a hankali ta fara motsa jikinta tana girgiza kanta, wadannan halittun ta dinga gani kewaye da ita suna kokarin shigewa jikinta, wani irin ihu ta saki haďe da faďin hasbunallahu wa ni'imal wakil, hajja dan Allah kizo ki taimakeni zasu kasheni, zasu kasheni, wayyyo Allah nah, Hajja tayi saurin katse sallar da takeyi ta yo kanta da gudu ta riketa, nan fa ta kara fasa wani ihun a firgice tana fisge jikinta, addu'a hajja ta fara karantowa da karfi tana tofah mata, a hankali ta bude idonta, ganin hajja ce zaune a gabanta yasa ta faďa jikinta tana kuka tana faďin kasheni zatayi hajja, wallhy kasheni zasuyi, dan Allah ki gudu dani gida, a firgice hajja tace wacece zata kashe ki, kafin Afeeyah tayi magana doctor musah ya shigo dakin da sauri nurses na biye dashi a baya, karasowa kusa da gadonta yayi yace sannu mama, yanxu nurse take fada min taji tana ihu, hajja tace wallhy farkawa tayi a firgice tana ihu bansan takamaimai abinda ke damunta ba, doctor musah yayi gwaje gwajen da zaiyi yace dan Allah mama kice mata ta kula sosai ta daina yawan firgita saboda cikinta baiyi kwarin da zai dauki hakan ba dan bai wuce sati uku ba, Allah ma ya kiyaye cikin bai samu matsala ba, saboda haka dan Allah a kiyaye, Hajja cikin mamaki tace ciki doctor, doctor musah yace kwarai mama, hajja tayi murmushi tace ikon Allah, To Allah ya inganta mana, yace ameen mama ya bata magani yace in taci abinci a bata tasha, hajja ta amsa ta mike da sauri ta hado mata tea, saboda murna hajja bata kara bi takan zancen da Afeeyah ke mata ba,, Tana bata magani ta mike ta kabbara sallah, kafin ta idar su alhj bara'u suka shigo, Amirah ta ajiye basket din abinci tayi gurin Afeeyah ta zauna tana mata sannu, Abida ma ta karaso cikin dakin tace ashe ta farfado alhj, alhj bara'u yace saidai in yanzu ta farfado amma dazu da muka zo da alhj basheer bata farfado ba, Abida ta karasa kusa da ita tace sannu Afeeyah ya jikin, a hankali tace da sauki ummi, Abida ta karasa kusa da hajja da ta idar da sallah ta tsuguna suka gaisa, tace hajja me suka ce yake damun ta, hajja tace to nidai har yanzu bansan dalilin firgicinta ba amma likita ya tabbatar tana dauke da karamin ciki na sati uku, Afeeyah tayi saurin runtse idonta saboda takaicin fada musu da hajja tayi, Allahu akbar alhj bara'u ya fadi yana murmushi, Abida tace lallai Allah da iko yake, Allah ya fito mana da wannan zazzafan rabon lafiya, Hajja taji tausayin Abida sosai a hankali tace Ameen, nan suka cigaba da yar hirarsu ta manya duk akan cikin, Afeeyah dai tunda ta runtse idonta bata bude ba har suka tafi,,, Alhj basheer ma da yazo doctor musah ya faďa mishi ba karamin farin ciki yayi ba,, bai wani dade a asibitin ba ya wuce gida dan kai ma su safiya albishir,,, Da murnarshi ya shiga gidan, tun kafin ya karasa cikin parlon yake kwala ma oyizah kirah, da sauri ta fito tana faďin alhj lafiya, yayi dariya yace lafiya lau safiya albishirinki, gabanta ya faďi da taga yana dariya dan ta dauka kiran fađin mutuwar Afeeyah yakeyi mata, a hankali tace goro, yace kin kusa samun miji ko kishiya, cikin rashin fahimta tace ban gane ba alhj, yayi dariya yace ay dama bazaki gane ba tunda ba bahaushiya bace ke, to ina nufin kin kusa samun jika, oyizah ta haďiye
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61