Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 45

Chapter 45

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da sauri ta diro daga gado tana mamakin baccin da ya dauketa har ya hanata zuwa shan jinin matsiyaciyar yarinyar nan, karar shigowar kira wayarta ne yasata saurin dagawa tace morning esther, jiya bacci ya hanani zuwa meeting, esther tace haba ay ni tunda naga ban ganki nasan kina can kina shegen baccinki, amma oyeee meyasa kikayi haka, meyasa kika bada jinin yari---- oyizah tayi saurin katseta tana dariya tace badai an gama komai kuma kun riga kun koshi da jinin ba, to ay shikenan, esther cikin damuwa tace oyizah me tayi miki haka da zafi har kikayi sacrificn dinta 4 no reason, oyizah tace meye ma bata min ba yarinyar nan, kedai zamuyi magana bari inje mu fara shirye shiryen jana'izah, esther tace to sai munyi waya, oyizah ta kashe wayar ta shiga bayi ta wanke fuskarta cikin farin cikin ta yar da kwallon mangwaro ta huta da kuda, a zuciyarta tace yanzu ne zan kara daure alhj da Affan ta yadda su da dukiyarsu zata dawo karkashin iko na gaba ďaya, bazan kara yarda a auro ma affan mace ba bare ma har ta zame min damuwa, Tana fitowa ta wuce parlor inda alhj basheer ke kallon news, saida ta gaisheshi sannan tace bari inje in dubo lafiyar Su Affan sai in kawo maka break ko, yayi murmushin jin dadi yace ya kamata kam saboda mai larurar ciki, ta shafi fuskarshi tana dariya tace su alhj ana ji da wannan jikan, yace sosai ma, Allah dai ya fito min da ita ko shi lafiya, oyizah ta kaurara dariyarta tace ya Hajjjj kenan sannan ta wuce side din su Affan.. Da izzarta ta buďe kofar tana murmushi, bata samu kowa a parlon ba dan haka ta tura kanta bedroom ďin, zaro ido tayi cikin firgici saboda ganin Affan kishingiďe da towel a jikinshi Afeeyah na zaune da night gown a gefenshi tana mishi gyaran fuska suna kallon juna suna murmushi, A-f-e-e-yah oyizah ta faďi bakinta na rawa, Afeeyah ta mike tana gyara gashin kanta tace naaaam ina kwana mummy, oyizah bata iya amsawa ba sai ma fita da tayi dasauri kamar zararriya, tana gab da shiga dakin alhj basheer dan daukar wayarta ta kira esther taji ihun farida a ďakinta, da sauri ta juyo ta karaso ďakin dan ganin abin da take ma ihuu..... Mrs tijjani shattima..... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣1⃣ By Aysha Ya'u Kurah Cikin ruďewa ta isa gaban gadon tana fadin ke lafiya, ihun me kikeyi, Fareedah ta kasa magana sai nuna salma takeyi da hannu tana kuka sosai, a firgice oyizah ta fara girgiza salma tana kiran sunanta, wani irin ihu ta saki haďe da zama a kasa tana faďin wayyyo salma, da gudu alhj basheer ya shigo ďakin yana faďin me ya faru, oyixah cikin ihu tace salma, salma--- yace salma me, tace salma ta mutu alhj, karasawa gaban gadon yayi kirjinshi na bugawa da karfi ya ďagota yana dubata, sakinta yayi da ya tabbatar bata rai ya shiga fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun, oyizah ta mike kamar zararriya tace alhj ka tasheta wallhy karka bari ta mutu, wayyyo na shiga uku na lalace, alhj basheer ya daka mata tsawa yace wani irin hauka ne wannan, waye ya isa da dawo da matacce, oyizah ta kara rusa ihu tana faďin wallhy sai ta dawo salma bazata mutu yanxu ba, tsaki alhj basheer yaja ya tashi ya fita daga ďakin hankali tashe, ihun suka cigaba dayi ita da farida suna kuka suna jijjiga salma suna faďin ta tashi, Ihun da sukeyi ne ya janyo hankalin Afeeyah dake zaune suna karyawa ita da Affan, da sauri ta mike tace ya karasa bari ta duba taga ihun me akeyi, tana fita tayi hanyar dakin mummy dan nan takejin ihun, sankarewa tayi da ta shigo dakin ta hango salma kwance inda ta shimfida wannan farin kyallen, innalillahi kawai take maimaitawa a zuciyarta, sam ta kasa karasawa gurin saboda tsoro, a zuciyarta tace yanzu da ni ce zan mutu, meyasa matar nan takeso ta kashe ni, wani irin kuka ta fashe dashi ta ruga dakinta da gudu a zuciyarta tana dana sanin sa farin kyallen a gurin, da tasan na mutuwa ne da ta daukeshi ta konashi bata shimfiďa wani ya hau ya mutu ba, kuka sosai takeyi tana fadin shikenan nayi kisan kai, da sauri Affan ya matso kusa da ita yana tambayarta abinda ya faru, bata bashi amsa ba ta shige can cikin daki ta dauki wayarta ta kira kaka liman, ringing biyu wayar tayi ya dauka, cikin muryar kuka ta gaisheshi ya amsa yace lafiya me ya faru, ta kara fashewa da kuka tace kaka nayi kisan kai, wallhy bansan abun mutuwa bane, na dauka wani tsafin tayi dan ta nakasa mu ashe na mutuwa ne, kaka liman yace nutsu ki fada min komai yadda yake dan bana fahimtar abin da kike fadi, nan ta tsagaita kukanta ta faďa mishi duk abinda ya faru, kaka liman yayi ajiyar zuciya yace kwantar da hankalinki Allah baya kama mutum da laifin da bai sani ba, lallai Allah na tare dake Afeeyah shiyasa har ya nuna miki wannan mummnan alamarin ya kuma baki basirar ki mayar mata da kaidinta, wannan aya ce Allah ya saukar gareta in har tana da hankali, har gurin Allah baki da laifi dan ba ke kika kasheta ba uwarta ce ta kasheta, ki dage ki cigaba da addu'a saboda yanzu ne zata kara karfin tsafinta in har tasan kaikayi ne ya koma kan mashekiya, Afeeyah ta share hawayenta tace to nagode kaka dan Allah ka cigaba da yi min addu'a dan wallhy abubuwan tsoro suke bani, kaka liman yace babu komai jikata addu'a kullum munayi saidai akara bude wuta, Allah ya dauraki bisa kanta, Afeeyah tace ameen sannan ta kashe wayar ta fita ta wuce gurin gawar salma.... Kafin karfe 10 angama shirya salma cikin suturarta za'a kaita gidanta na gaskiya, har lokacin oyizah bata bar ihu ba sai sambatu takeyi tana fadin wallhy babu inda za'a kai mata ya, babu wanda ya isa yaje ya binne mata 'ya a rami, sosai ta fita hayyacinta tun kukan na fitowa har ya daina fitowa, dakyar aka fita da gawar salma daga gidan, sai da oyizah ta suma sai uku saboda tashin hankali, tana farfadowa ta shiga tsine ma mutanen gurin tana fadin ita fa yarta bata mutu ba dan ko ciwon kai batayi ba, Da mutane suka ga abin nata jahilci ne sai suka watse suka barta da kukan takaici, Bayan azahar esther ta kara kiran oyizah, cikin kuka oyizah ta ďauka tana faďin esther salma ta mutu, batayi ciwon komai ba, ko mura ba tayi ba lafiya lau muka rabu jiya da daddare,, esther tayi dariya tace kin iya acting oyizah halan kina cikin taron mutane ne, oyizah cikin ihu tace wane irin acting ina fada miki yau da safe mun tashi ba salma shine har kike dariya, esther tace to ay abin naki ne, ki bada yarinya da hannunki sannan kizo kina kuka, oyizah ta zaro ido tace wace yarinya, esther tace salma mana, salma kika kawo jiya, kinsan kuwa saboda hakan da kikayi har mukami aka kara miki saboda kin kawo yarki wacce kika fi

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});