Chapter 40
Chapter 40
Afeeyah ta kauce tace toh fah!!, ashe dai rashin aure ba masifa kadai yasa ku harda harkar dabanci, fisabillihi ku ko kunya bakwa ji, ni bansan meyasa kuke bakin ciki dani ba dan nayi aure at dis age of mine, dan Allah ku barmu muci soyayyarmu ni da mijina zan muku addua' kuma Allah ya kawo mashinshini nan bada dadewa ba dan rik'ar da kukayi a gida ta isa haka, abun ma ni har tausayi yake bani, babu wanda ya iya cewa komai sai kallon mamaki da suka bita dashi, cikin karfin hali salma tace ina mijin yake anan da zamuyi bakin ciki, ke nan har wani miji ne, wannan tababben da baisan kanshi ba ma bare mace, Afeeyah tayi saurin cewa tabdijam,, ke kike ganin tababbe, ta rungumoshi tace ni nan namiji nake gani wanda a cikin maza ma sai an tona kafin asamu irinshi, dan Allah ku fitar mana a ďaki dan naga alamar baku san wannan lokacin na hutawar ma'aurata bane, fareedah ta harzuka matuka ta ajiye maganin hannunta tayi kan Afeeyah zata duketa oyizah tayi saurin dakatar da ita da hannu, tace barta fareedah wallhy sai tasan ta faďa muku wadannan maganganun, kuzo mu tafi, Afeeya tace to sai da safenku Allah ya aurar daku ku huta da kunci, amma fa mummy baki nuna min yadda zan bashi maganin ba, oyizah kamar ta rusa ihu tasa kai ta fita ba tare da ta bata amsa ba, Afeeyah ta bisu da li'ilah fi quraish ta datso kofar ta dawo ta kalli Affan da ya gama tsurewa tace matsoraci to sai ka zauna tunda dodonka ta tafi, Affan ya zauna murya a sarke yace mummy tayi fushi dani ko, Afeeyah tace batayi fushi ba bari in kawo maka abinci kaci sai kasha magungunanka kayi bacci kaji, Affan ya gyaďa kanshi, Da kanta ta bashi abinci yana gama ci yasha ruwa da drink ta dauko magungunan da oyizah ta kawo, saida ta karance su tsaf ta kalli wani ruwan jarka shi ba ja ba shi ba maroon ba, daga kafadarta tayi tace may be na gargajiya ne, na asibitin ta fara bashi duk wanda ta kai bakinshi sai tace yayi bismillah sannan zata zuba mishi, tana bude na jarkar taji wani karni karni, da kyar ta tsiyayya a cup tace wa'iyazubillah wannan irin karni haka, ta mika mishi tace kayi bismillah, yana yin bismillah ya kai bakinshi yaji hannunshi na rawa sosai, da kyar da taimakon Afeeyah ya shanye maganin, boye magungunan tayi ta gyara gurin ta dawo ta zauna tana mishi hirah yana kyakyata dariyah harda buga kai a pillow, sun shagala sosai cikin farin ciki Afeeyah taji ana buga musu kofa, mikewa tayi tana mita a zuciyarta, tana budewa taga oyizah tsaye kamar gunki, Afeeyah taja baya tace kin dawo ne mummy, Oyizah ta kalleta tace tambayar da ya kamata kiyi min kenan ni da gidan mijina, Afeeyah tayi dariya tace to ai wannan tambayr tafi da inyi miki shuru in kyaleki, kuma nima nan turakar mijina ce, oyiza tace wallhy zan babbalaki a gidan nan in bawa karnuka kasusuwanki su cinye, Afeeyah tace waii ay ko da sunci kashi da wahala dan wallhy kashi na taurin tsiya gareshi, oyizah tayi shuru dan taga abinda ke neman fin karfinta tace kin bashi magungunan, Afeeyah tace wannan dole ne tunda inason mijina ya samu sauki, oyizah tace akwai wani a jarka ki tabbatar yasha dama dan in jaddada miki ne yasa na dawo, Afeeya tace karki damu in ma akwai wani ki karo bazan gajiya ba, oyizah tayi tsaki ta wuce ranta a bace, ta riga ta gama kudirawa a ranta a daren nan zata lalata rayuwar yarinyar nan, wallhy yau sai tasan ta tabo ni, dan bazan barta ba abinda ta dinga fadi kenan,,,,, To oyizah sarkin sa'a muna miki fatan nasara akan Afeeyah... ... Mrs tijjani shattima.... [PM, 05/04/2016] Ummu Nan: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣6⃣ By Aysha Ya'u Kurah Tun sha biyun dare Afeeyah ke jin wasu irin sautittika masu ban tsoro ta windon ta, kallon Affan tayi yana baccinshi hankali kwance, cikin dabara ta cire hannunshi a jikinta ta gyara mishi kwanciya ta mike a tsorace saboda sautin karuwa yakeyi, cikin karfin hali da dakewar zuciya ta ďaga labulen windon dakin, sakin labulen tayi da sauri taja baya tana maimaita "HASBUNALLAHU WA 'NI'IMAL WAKIL" saboda ganin wasu halittu masu ban tsoro kewaye da windon,,, wani kara taji an saki nan take taji ďakin da suke ciki yana girgiza ta ko'ina, runtse idonta tayi tana karanto adduo'in neman tsari, da dai taga kamar kara girgiza ďakin akeyi sai tayi karfin halin buďe kofarsu cikin sauri tayi hanyar da zata sadata da ďakin oyizah, Tana zuwa kofar dakin ta kama murfin xata bude taji sautin magana da karfi wanda ya sata sakin kofar bata shirya ba, sunanta taji sosai ana kira a ďakin ta kuma ji wannan sautin na windon su ya dawo nan inda take tsaye, a gigice ta leka ta windo don jin mai ambaton sunanta cikin wannan sigar a kuma wannan talatainin daren, tana lekawa ta hango oyizah cikin jajayen kaya tsugune gaban "chummy," sai wani bakin basamude a tsaye a gafensu rike da wani bakin kare, Afeeyah bata kara firgita ba sai da taga oyizah ta dauki kwaryar jini ta shanye tass sannan ta kara daukan wani ungulu tana kiran sunanta dashi, fitsari ta saki nan take saboda ganin duhu ta ko'ina bata iya hangen gabanta, lalube ta fara yi tana addu'a da karfi tana kiran sunan hajja dan ta tsorata matuka da abin da idonta ya gane mata, ga wannan girgizar har lokacin bata bar jinta ba, a cikin laluben taji hannunta ya taba mutum, nan take ta tsandara ihu haďe da faduwa kasa sumammiya, A gigice alhj basheer da ya fito dan ganin abinda ya samu wutar gidan ya haskata da torch light, cikin kidima ya fara kiran sunanta yana fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun, safiya, safiya, oyizah ta tsorata matuka da jin muryar alhj basheer dan tasan yayi bacci, cikin azama ta tattara kayan tsafinta ta cire na jikinta ta mayar da night gown din jikinta ta fito tana mutsika ido, alhj basheer yace safiya zo ki kama min yarinyar nan mu kaita asibiti ko numfashi bata iya yi na rasa me ya fito da ita cikin daren nan, oyizah ta matso da sauri tace wace yarinya, alhj basheer yace Afeeyah ce, kamata da sauri dan Allah, oyizah cikin murna ta kama Afeeyah dan a tunaninta tsafinta ne ya kamata, suna fitowa wutar gidan ta kawo alhj basheer ya bude motar suka tura Afeeyah ciki, oyizah ta koma ta dauko hijab dinta suka wuce asibiti, Tunda aka kaita asibiti a wannan daren likitoci ke iya kokarinsu suga ta farfaďo amma abin yaci tura, oyizah cike da murna ta nemi guri ta zauna a zuciyarta tace yarinya ai tunda kika shiga gona ta sai kinyi noma wallhy, alhj basheer kuwa hankalinshi ba karamin tashi yayi ba dan baisan meye ya sami yar mutane ba, safa da marwa kadai yakeyi a cikin asibitin, dakyar doctor musah ya lallabashi akan in shaa Allahu zuwa gobe zata farfado in kuma bata farfado ba sai musan abin yi, alhj basheer akanta ya kwana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61