Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 30

Chapter 30

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yace kamar yaya abinda zasu bashi, me zasu bashi kuwa, oyizah ta saita kanta tace ina nufin kasan baya cin komai in ba ni na bashi da kaina ba, ta kara fashewa da kuka tace yanzu Allah kaďai yasan yunwar da yakeji, alhj basheer cikin jin dadin kulawarta ga danshi yace karki damu safiya Affan na can cikin koshin lafiya kuma yaci abinci sosai dan abin har mamaki ya bani, kuma kinsan ďan zaman nan da yayi a gurin makoki yau har sallah yayi da kanshi saboda ganin mutane nayi, oyizah ta mike cikin kidima tace alhj kana yi wa Allah kaje ka dawo min da ďana, alhj basheer yace wai bakiji abinda nace miki bane, ki bari zuwa gobe mana, ta girgiza kanta ta wuce ciki tana kuka tana faďin dan kaga na damu dashi ne shiyasa kake nuna min ba ni na haifeshi ba, alhj basheer yayi murmushi a zuciyarshi yana kara jin son oyizah saboda yadda take nuna kulawarta ga Affan. .. Oyizah taci kuka a wannan daren dan ta hakikance wasu daga cikin abubuwan da tayi ma Affan sun warware, tunda har Affan ke iya mata musu kuma har yayi sallah, wani irin ihun takaici tayi da ta kara tuno da Affan na can gidansu jabeer kuma Allah kaďai yasan abinda zasu bashi..... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣5⃣ By Aysha Ya'u Kurah Washe gari tun asuba oyizah taje gurin alhj basheer ido luhu2 saboda kuka da rashin bacci, gaba ďaya ta rasa abinda zata yi a wannan daren saboda bata san ta inda zata fara ba tunda Affan baya gabanta, alhj basheer ya ďago ya kalleta cikin bacci yace safiya lafiya, tace alhj naga kai baccinka ma kakeyi baka damu da yaron nan ba, ko bacci banyi ba saboda nasan da kyar in ya iya yin bacci, alhj basheer yayi mika haďe da salati yace lafiyarshi kalau safiya yau a masallaci ma na samesu tare da kaka mahaifin alhj bara'u, rike ciki oyizah tayi hankali tashe tace a masallacin suka kwana? Alhj basheer yace a'a sallahr asuba suka je, oyizah ta zauna dabass a kan gadon ta marairaice tace alhj inda zaka san irin missing din Affan da nakeyi da baka barshi ya kwana a wani guri ba, wallhy jiya banyi bacci ba dan daga na rufe ido shi kaďai nake gani, kasan yadda na shaku dashi kuma nake jin tausayinshi, dan Allah ka tashi kaje ka dawo min dashi, alhj basheer ya tausaya mata dan yasan tana iya kokarinta akanshi yace to bari in yi wanka zanje in dawo miki dashi, ta saki wata dariyar murna tace nagode alhj bari in je in shirya mishi favourite break dinshi, alhj basheer yayi dariya ya koma ya kwanta, Daki oyizah ta koma cikin murna tace wannan karan mai gaba ďaya zanyi akan yaronnan dan bazai yiwu su dinga daga min hankali ba, gara in kashe shi ya bi abokinshi in huta da zulumi, wata zuciyar ta haneta da sauri tace in kika kasheshi yanzu tayaya zaki samu dukiyoyin da alhj ya mallaka mishi, sannan in kika kasheshi hankalin mutane zai dawo kanki su zarge ki, gara kibi komai a hankali ki kara tsaurarawa akanshi ki maida shi mara amfani, da wannan tunanin tayi yan tsaface tsafacenta na gaďo sannan ta wuce kitchen shiryawa Affan break... Karfe 9 da kwata alhj basheer ya iso gidan rasuwar, zaune ya samesu a cikin parlor sunyi shuru sai muryar Affan kadai akeji yana ma kaka liman hirar shirme, dariya kawai kaka liman keyi yana tausayawa halin da Affan ke ciki, da sallama alhj basheer ya shigo parlon ya tsuguna ya gaida kaka liman sannan suka gaisa da alhj bara'u, alhj basheer ya kalli Affan yace ka tashi lafy, Affan ya gyaďa mishi kai yace sosai ma tare da kaka mukayi bacci shi ya tashe ni yasa nayi wanka ya bani abinci ko kaka?, kaka liman yayi murmushi yace kwarai dan kaka, alhj basheer yace kace yau kai ďan gata ne, to tashi mu tafi gida mummynka na can tana missing dinka, Affan ya noke wuya yace ni bazan je gida ba, alhj basheer yayi murmushi yace meyasa? Affan yace saboda har yanzu abokina bai dawo ba, alhj basheer yace ay yana can gida yana jiranka kuyi wasa, Affan ya waro ido waje yace dagaske daddy, alhj basheer ya gyaďa kanshi yace dagaske nake, Affan ya kalli kaka liman yace wai haka kaka, kaka liman yayi dariya yace haka ne, Affan ya tashi da sauri yace muje daddy, alhj basheer ya mike ya rike hannunshi yayi sallama da su kaka liman suka fito tare da alhj bara'u, a bakin gate suka haďu da hajja rike da katuwar kular abincin sadaka, da gudu Affan yaje gurin ta yana kokarin karbar kular hannunta, kauda kular tayi tana dariya tace bazaka iya ba Affan, su alhj basheer suna dariya suka tsuguna suka gaisheta ta amsa haďe da kara yi musu gaisuwa, alhj Bara'u yace ina Afeeyah dafatan jikin nata da sauki, Hajja tace hmm sai dai addu'a tana can tun jiya take abu ďaya yanzu na baro mahaifinta yana mata rubutu, alhj basheer yace kuka fa dole ne hajja shakuwar zaku duba, kai mutuwa, mutuwa mai yankan kauna, Affan yace daddy Afeeyah ce ke kuka, alhj basheer ya gyada mishi kai, Affan ya bata rai kamar zaiyi kuka yace daddy tun jiya fa take kuka kaje ka rarrasheta kace tazo muje gidanmu taga abokina muyi wasa tare, alhj basheer yace to yanzu dai muje gida anjima zan je in rarrasheta sai in kawo maka ita gidan kaji, Affan yayi dariya sosai yace gaba daya zata dawo gidan mu ko?, dama jabeer yace zai bani ita in ya aureta kuma kaima kace zaka aura min ita ay ko,? sukayi dariya dukkansu alhj basheer yace eh zan aura maka ita wuce muje, ya fita yana tsallen murna, sun kusa karasawa gidan ya rungume daddy yace daddy ka goyani kar inga lions, alhj basheer yace babu abinda zaka gani buďe idonka nasa an cire su, a hankali ya buďe idon yaga babu abubuwan da ya saba gani a kofar gidan, a tsorace ya shiga gidan yana zazzare ido, jiki na rawa oyizah ta fito ta rungumeshi tana faďin oyoyo Affan ďina, nayi missing dinka ďana, alhj basheer yayi dariya yace ai da kyar ya yarda ya biyo ni saida na ce mishi jabeer na nan gidan sannan, oyizah tayi murmurshin mugunta tace muje ciki kaci abinci sai in nuna maka abokin naka, Affan yayi dariya ya bita suka shiga ciki, Special break ta haďa mishi wanda yaji magunguna, zaunar dashi tayi ta cika gabanshi da abinci ta diba a cokali zata fara bashi ya kauda kanshi yana rike ciki yace mummy munci abinci sosai tare da kaka har da kosai ma mai dadi, oyizah ta ajiye cokalin ta saci kallon alhj basheer da hankalinshi ke kan TV sannan ta kalli Affan tace haba baby na, baka so kaga abokin naka kenan Affan da sauri yace inaso mummy, tace oya open ur mouth kayi ko 1bs ne, ya buďe bakinshi ta ďebo zata zuba mishi ya kara kauda kanshi da sauri yace ina zuwa mummy kaka liman yace in zanci

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});