Chapter 22
Chapter 22
Afee dakyar suzo gurin Affan, in Affan ya ganta to fa aranar murnarshi ta karu kenan saboda ya dinga mata shirme kenan yana kwaso kayayyaki yana bata wai ta tafi dasu gida, a cikin yan kwanakin suka dan fara sabawa kadan2, dakyar jabeer ya fahimtar dashi cewa an kusa daura mishi aure da Afeeya, dariya kawai yayi yace to in kukayi aure zaka barmin ita anan gidan, jabeer yace sosai ma ai anan zata zauna, Affan yayi dariya ya kalli afeeyah yace wai haka, ta gyaďa mishi kai tace eh, wani irin ihu yasa ya mike wai zaije ya fadama mummy, da sauri Afeeyah ta riko hannunshi ya tsaya chakk yana jin wani irin abu a rikon da tayi mishi, juyowa yayi kamar me hankali ya kalleta itama shi take kallo haka jabeer kallonsu kawai yakeyi, jikinta ne ya bata jabeer na kallonta tayi saurin sakin hannun Affan tace karka faďa ma mummy zatace kar abaka ni ko yaya jabeer, jabeer ya gyada kanshi yana kallon Affan, zama Affan yayi yana murza hannun da Afeeyah ta rike yace to babu abinda zatamin in ta sani, Afeeya ta gyada mishi kai tace baza ma tasani ba, jabeer yayi mamakin yadda affan yaji maganar afeeya, mutumin da magana in dai akan mummy ne to babu wanda ya isa ya tsayar dashi, kallonsu ya cigaba dayi yadda yake mata hira tana biye mishi suna kyakyata dariya sai yaji daďi a ranshi dan ko ba komai zai yi amfani da Afeeyah ta dinga dawo dashi hanya, sam baiji kishin komai a ranshi ba dan yasan Affan baida hankali kuma ko yanada hankali ma bazaiyi kishi ba saboda yasan irin son da afeeyah take mishi.. Safiyyar monday jabeer ya shirya da wuri saboda zai kai Afeeyah makaranta ranar zasu fara jarabawa, a kofar gidansu ya sameta tsaye tayi kyau sosai tana jiranshi, kusa da ita ya kai motar ta bude ta shiga suka gaisa, yace da fatan kinyi karatu ko, tace sosai ma banyi bacci sosai ba, yace kedai fadi gaskiya kodai kin boyo xpo, ta turo baki tace kaima kasan wuce nan duk da bana zuwa 1st kasan dai ban taba wuce 10th ba, yayi dariya yace 3rd term ss2 dakyar na roka fa aka barki a 10th din shine zaki wani cika min baki a faďa da dambe ne dai ake baki A1, ta harareshi tace eh naji ďin, yayi dariya ya tada motar suka wuce yana cigaba da tsokarta, kan titin "hausawa" ya hango motar gidansu Affan, bai bi takanta ba bare yasan su waye a ciki, ya wuce ya sauke Afeeyah a skool haďe da yi mata adduoin samun nasara.. Yana fitowa daga layin skull dinsu ya kuma hango motar, wannan karan Affan ya hango a gaba da baloon a hannunshi yana dariya mummy ta hakimce a baya, bin motar yayi dan yanason yaga Affan kafin ya tafi aiki, asibitin da ake mishi check up suka tsaya, saida suka shiga ciki Jabeer yayi parking, saida ya gaisa da wani abokinshi da suka dade basu haďu ba sannan ya shiga, sam oyizah bata ganeshi ba saboda hankalinta a tashe yake da result din check up din, jabeer yaji doctor na cewa gaskiya an gode Allah dan zai iya dawowa normal cikin kwanakin nan saboda mun samu improvement sosai, ya mika mata magani yace wannan maganin shine maganinshi na karshe in shaa Allah in ya kare komai zai zama normal, jabeer saboda murna zaiyi magana ya bugi wata nurse kayanta suka zube ya durkusa ya kwashe mata yana bata hakuri, yana ďagowa yaga har sun fita sun shiga mota, binsu yayi a baya har gida, a waje yayi parking motarshi saida ya tsaya a waje ya kirah office ya dau excuse sannan ya shiga ciki da sauri, babu kowa a parlon gidan hakan yasashi hawa sama saboda tsananin murna, tsayawa yayi jikin wata kofar da yakejin magana da karfi haďe da huci kamar zakanya, lekawa ya fara yi ta gurin mukulli, ya hango Affan zaune kan wani jan kyalle, da sauri ya dago kanshi jikinshi na rawa ya ďeka ta window, oyizah ya hango da wata halitta suna magana suna zagaye Affan, suna gamawa yaga an bawa oyiza wani ruwa ance ta bawa affan muddin yasha to bashi ba samun sauki kuma haukarshi zata fi ta da, oyizah tayi dariyar jindadi tayi sujjada ga wannan halittar nan da nan yaga ta bace,, jabeer sai mutsike idonshi yakeyi a tsorace kamar a mafarki, muryar oyizah ce ta dawo dashi hayyacinshi waya takeyi da esther tana faďa mata duk yadda tayi ta mayar da Affan haka har abin da tayi ma zeenatu, a kidime jabeer ya fara fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun, jin tayi shuru ne yasa ya leka da sauri ya hangota ta mike zata bawa Affan wannan ruwan, cikin zafin nama ya murda kofar ya kabe ruwan ya zube a kasa, oyizah ta kalleshi a firgice tace j-a-b-e-e-r, ya dago Affan ya rikeshi yana mata wani mugun kallo yace asirinki ya tonu, muguwa azzaluma, matsafiya mai shan jinin alumma, naga duk abinda kikeyi yau in shaa Allahu karshenki yazo, yaja hannun Affan zasu fita oyiza tace jabeer ka dawo, ka rufa ma kanka asiri dan wallhy babu wanda ya isa yaga karshena, ka dawo ka fadi nawa zan biyaka ka rufa min asiri, jabeer bai saurareta ba ya fita dan a tsorace sosai yake, suna zuwa gate Affan ya fisge hannunshi yasa ihu yana faďin mummy kizo ga su lion nan zasu kamani, ihu yakeyi yana ja baya ya ruga ciki da gudu, jabeer ya kalli gate din cikin mamaki dan shi baiga komai ba, har zai koma ciki sai kuma ya fasa ya fita a fusace, Police station ya nufa yana zuwa kofar gurin ya fara tunanin to ina evidence yake, Affan shi kadai ne evidence kuma bashi da hankalin da za"a saurareshi, shuru ya zauna a motar yana tunanin mafita, can ya fara tunanin yadda zaiyi affan ya samu sauki, a zuciyarshi yace malamai zan tara suyi ta mishi addu'a ita kuma oyizah zan mata lamfa in nuna mata kamar bazan fadama kowa ba har sai nasan yadda nayi har Allah ya bawa Affan lafiya,... Mrs tijjani shattima... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣7⃣ By Aysha Ya'u Kurah Juya kan motarshi yayi ya nufi gurin wani babban malami dake zaune a Tarauni, saida ya jira malamin ya gama da almajirai sannan ya shiga suka fara zantawa, Bayan malamin ya gama jin bayanin jabeer sai ya jinjina kai yace tabbas imani yayi karanci a wannan zamanin, na dade banji rashin imanin da har yakai wannan ba, ya kalli jabeer yace in shaa Allahu zamu hadu mu fadawa Allah nan da kwana uku zuwa hudu komai zai dai2ta kai dai ka dauke kafarka daga gidan ka barta cikin tunanin baka fadama kowa dinba sannan kayi taka tsan tsan da ita, jabeer yace to malam nagode sosai ya ajiye musu kudin sadaka sannan ya mike ya fita, Gurin malamai uku yaje a ranar duk yayi musu bayani suma sun dauki alkawarin yi mishi addua ba dare ba rana,, ranar jabeer ya yini cikin bakin ciki babu yadda ummi da Afeeya da hajja basuyi ya faďa musu abinda ke
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61