Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yana bude gurin, fitowa yayi da sauri kamar wanda akayi ma albishir da gidan aljanna, karasawa yayi yana kiran yaron, john ya juyo rai a bace saboda yadda yaji ana kiranshi ganin alhj basheer yasa john jindadi ya fito da gudu ya tsuguna a gabanshi ya gaishe shi, alhj basheer ya amsa suka shiga ciki, ya kalli john yace ina madam dinku, john ya raunana fuska yace madam is no more alhj tun ranar da kazo washe gari ta mutu, alhj basheer ya girgiza kanshi cikin tausayin oyiza yace Allah ya jikanta to ina yarta oyiza, john yace tana gida dama tace idan kazo in kaika can gida, alhj basheer yaji dadi sosai a ranshi dan a tunaninshi kafin mahaifiyarta ta rasu tayi mata bayanin komai, tashi yayi suka fito shi da john suka shiga mota suka wuce gidansu oyiza... Bayan ya gama yi mata gaisuwa yana rarrashinta saboda kukan munafurcin da take yi ita a dole tayi rashin uwa, tausayinta sosai ne ya ratsashi ya tambayeta ko mahaifiyarta tayi mata bayaninshi, tayi kasa da murya tace eh a daren ranar ta fada min komai kuma tace in ka dawo zata yarda ka aureni, ta fashe da kuka tace ashe bazata ga auren ba, alhj basheer zuciyarshi ta kara narkewa yace kin yarda to zaki aureni, tayi kasa da kanta tace ko banaso zan yarda tunda shine last will din mahaifiyata, alhj basheer yace haka ne naji dadi sosai da kuka amince dani, yanzu ina son cikin satin nan a gama magnar komai muyi aure in tafi dake, wani daďi ya ratsata tace to ba matsala bari in turo maka kanin babana kuyi magana, mikewa tayi ta shiga ciki ta turo mishi kanin babanta da wan mamanta, Kudin da alhj basheer ya wankesu dashi da kuma nuna yanason ya auri oyiza saboda yana tausayinta shi kadai yasa suka yarda da auren suka sa rana ya biya sadaki da komai, sannan ya tafi cikin farin ciki, A daren ranar ya fita da oyiza yawo ya siyo mata duk wani abu da mace zata bukata na aure,, sun daďe tare har suka saba sosai kafin su rabu, Tana shiga gida ta dinga tsalle tana murna nan ta shirya ta wuce gurin chummy yin godiya.... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:32] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 9⃣ By Aysha Ya'u Kurah Cikin satin aka ďaura auren alhj basheer da Safiya oyiza a okene, shiri na musamman chummy tayi ma oyiza ta haďata da special kayan tsafi a cewarta su zasu taimaketa ta zauna lafiya saboda wannan matar tashi mai yawan addu'a, Washe garin daurin auren ne ya dauki matarshi da kawayenta biyu suka kamo hanyar kano, tunaninshi ďaya shine yadda zai fara tinkarar zeenatu da maganar ya auri oyiza saboda sam duk wainar da ake toyawa bata sani ba, ita dai taga ana ta aikin gyaran part din gefenta sama da kasa amma sam bata kawo aure yayi a ranta ba, sai gurin bakwai suka shigo garin kano, kallon garin oyiza da esther keyi har suka kawo kofar dankareran gidan alhj basheer dake zoo road, a kofar gidan alhj bara'u ya hango su tsaye shi da malam atiku suna hira, ganin motarshi yasa suka mike suka karaso gurinshi da saurinsu, ya leko ta cikin glass cikin fara'a suka gaisa, yace ga amarya fa ku gaisa, alhj bara'u yayi dariya yace wace amaryar kuma, alhj basheer yace amaryata da aka ďaura min aure da ita jiya, malam atiku yace shine ko labari ranka ya daďe to Allah ya sanya alkhairi sannu amarya, oyiza ta gyara gyalenta tace yauwa, alhj bara'u ma yayi mishi addu'a suka ja suka tsaya shi kuma ya danna kai cikin gida kirjinshi na duka sosai, parking yayi suka fito duka su ukun suna mika gasu ďirka2, sannu alhj basheer yace musu sannan ya fara tafiya suna binshi a baya, yana buďe kofar main parlon yayi arba da zeenatu cikin kyakykyawar shigar material dinkin stone work fatar nan tata sai kyalli takeyi ga wani kamshi da sanyin dadi ko'ina a cikin parlon, da sauri ta karaso tana mishi sannu da zuwa,, gabanta ya faďi sosai da ta hango su oyiza amma sai ta kara fadada fara'arta tana musu sannu da zuwa, karasawa sukayi cikin parlon suna yabawa da kyau da tsarin parlon ga kuma kula da yake samu ta musamman, zeenatu ta nuna musu guri suka zauna ta wuce kitchen cike da tambayoyi a zuciyarta, kayan shaye2 ta kawo musu da snacks tanata yake, ta kalli alhj basheer da ya dafe kanshi tace yallabai gajiyar ne, tashi muje ciki kayi wanka, oyiza cikin kishi ta watso ma zeenatu harara, alhj basheer yace zauna zeena akwai maganar da nakeso muyi dake, ta nemi guri kusa dashi ta zauna, a hankali ya fara magana yace sai kuma kika ganni da baki, tayi murmushi tace eh,, yace dafatan zaki fahimceni zeenah, kinsan komai nufi ne na Allah kuma matar mutum duk inda take sai ya aureta, ya nuna oyiza yace wannan matata ce jiya aka ďaura min aure da ita bawai dan inci mutuncinki ko kuma dan bana sonki ba, "a'a" wannan auren ki ďaukeshi kaddararre ne daga Allah kuma babu mamaki safiyya na tafe da alkhairai masu yawa cikin gidan nan, zeenatu da tayi mutuwar zaune tayi maza ta saita kanta ta kirkiri murmushi tace kaii barka Allah ya sanya alkhairi nayi maka murnar samun karuwa, ay aure cigaba ne yallabai Allah ubangiji ya bayyana alkhairan dake cikin wannan auren kuma alkhairan ya wanzu a tsakaninmu, yace ameen yar albarka zeenatu nagode sosai da kika fahimceni, tace ba komai yallabai bana jayayya da abin da Allah ya kaddara Allah ya bamu zaman lafiya, yace ameen, nan yayi introducn zeenah a gurin oyiza da irin muhimmacin da take dashi a gurinshi, oyiza ranta ya baci da irin praisn zeenah da yakeyi a gabanta da kawayenta, bayan ya gama maganganun da zaiyi yace ma oyiza su tashi ya nuna mata part dinta, suka mike kamar samudawa suka rataya jakunkunansu suka wuce, zeenah da kiris ya rage ta fashi da kuka ta danne kishinta ta shiga kitchen ta hado musu abinci ta kai musu dakinsu ta fito tayi nata dakin ta rufeshi da key ta faďa gado tanata rusa kuka, Can dakin oyiza kuwa bin ko'ina sukeyi ita da kawayenta suna tsalle suna murna ganin irin dukiyar da alhj basheer ya zuba a ciki, zama sukayi a kan gado esther tace oyee baby sai kinyi da gaske da wannan matar dan da ganinta ta iya munafurci, evelyn tace green snake kenan, gata very pretty, gaskiya akan matar nan na kara yarda black is beauty kuma suna kama da bash, oyiza tayi tsaki tace trust mee mana ai matar nan sai mai aikina ta fita daraja bari dai in haihu, kunsan bata haihuwa kuma na riga na gano abinda alhj yafi so a rayuwarshi kenan haihuwa, ta shafa cikinta tace baby boy zan haifa maka alhj a lokacin ne zan nuna karfin ikona a gidanka,, duk suka kwashe da dariya evelyn tace shegiya a ina kika san baby boy zaki haifa, oyiza tace bansani ba amma dat's wat I want kuma zan samu kinsan ni duk abinda nake so sai na samu, suka kara kwashewa

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});