Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

damunshi ba amma yaki fadi, Afeeya har kuka tayi mishi duk dan ya fadi amma bata samu nasarar ya fada din ba, Oyiza kuwa rasa yadda zatayi tayi, ya akayi wannan mayen yaron ya shigo gidannan ya hayo har sama yaji sirrina, kallon affan tayi da ya fara bacci saboda tsoron abinda ya gani a gate, wani dogon tsaki taja a zuciyarta tana tunanin yadda zatayi da jabeer, yanxu tasan yama gama tona mata asiri saboda haka in ta dau mataki akanshi jama'a zasu zargeta gara tabi komai a hankali.. Kwana biyar da faruwar wannan alamari oyiza taji shuru babu Wanda ya tinkareta, sannan alhj basheer bai canza mata ba kamar yadda tayi tsammani, hakan ya bata karfin gwiwar fara aiwatar da duk wani mugun nufinta saboda a tunaninta tsafinta ne ya toshe ma jabeer baki ya ki fadawa mutane, Shi ko jabeer hankalinshi a tashe yake dan duk malaman da yasa su addu'a kowanne larura ta faďa mishi, daga wanda ya rasa ďanshi sai wanda yayi paralys sai kuma wanda ya rasa mata, cikin tashin hankali ya dawo gida yayi tagumi yana tunanin mafita, "Kaka liman" ne faďo mishi a rai nan da nan ya kira wayarshi, kaka liman yasa wayar a kunnenshi ba tare da ya duba wanda ya kirashi ba yace "malam dan boko dan Bara'u jikan limamin Daura ya ta dabo," jabeer yayi dariya yace lafiya lau kakan dan boko ta dabo na gaida Daura, ya kuma tsufa da tsohuwa, kaka liman yace tsohuwa tana can tana damun hura kasan bata son ayi mata kishiya, jabeer yace kai ka isa kayi ma Goggo kishiya, kaka liman yace kaji ja'iri kaima fa naga auren nan zakayi nima ina ga cikin satin nan zan nemo wata a cikin nan nijar auro, jabeer ya kwashe da dariya yace gara dai ka tafi can dan matan nigeria sun fi karfinka, kaka liman yace lallai baka san wanene Abdullahi ba, a gobe in matarka nakeson aure tana ganina shikenan kai kuma taka ta kare, jabeer cikin dariya yace dan Allah karka kasheni da sauran raina, bari in fada maka dalilin kiran da nayi maka, kaka liman yace inajinka, jabeer ya kwashe komai ya faďa mishi har larurar malamn duk ya faďa mishi, kaka liman ya ajiye goron hannunshi yace wannan ta shahara matuka jabeer, ka kirani zuwa karfe takwas na dare zanyi binciken duk wani kullin da sukayi dan sai an fara takanshi kafin a tsunduma cikin addua, a wannan karan bada malami zata gwabza ba da ni "liman dan Baba" zata gwabza jinina da duk na wani nawa ya fi karfin matsafa saidai idan abun yazo da karar kwana, jabeer yace to zan kiraka kaka nagode sosai, kaka liman yace ďan nema rike godiyarka in zaka taho ka siyomin shaddoji da kayan mata in haďa a lefe in auro sabuwar amarya, jabeer yayi saurin kashe wayar yana dariya... Duk wasu abubuwan tsafi da kulle kulle babu wanda kaka liman bai gani ba, abinda ya kasa ganewa shine na zeenatu gata nan dai an nuna mishi ita a baccinshi bata motsi kuma an nuna mishi tana nan kusa dashi saidai baisan takaimai gurin ba, ko da yayi ma jabeer bayani yace dole akwai hake haken da sai an haka sannan za'a warware abubuwa sai hayaki da wasu magungunan da zai haďa mishi, dan haka ya bashi kwana uku yazo ya sameshi sai suyi wanda zasuyi a daura sauran ya tafi dashi ya karasa a kano, jabeer yaji daďi sosai ya dinga ma kaka godiya saboda yasan ko ba komai abokinshi zai samu lafiya kuma zaayi punishing oyiza 4 her deeds, Tun daga ranar kaka liman yake aiki babu dare ba rana duk da ana yawan kawo mishi farmaki cikin dare haka suke gwabzawa har su hakura su tafi su barshi, ranar kuwa da ya gama haďa magungunan saida gidanshi ya kusa rushewa saboda girgiza, bai wani tsorata ba saboda shima hatsabibin bafulatani ne, a cewarshi shi a duniyar nan baiga abin tsoro ba banda Allah shi kadai yake tsoro a ko dayaushe amma mutum dan adam wanda Allah ya ara ma lokacin tsafi ko wani abu to ba abun tsoro bane dan idan Allah ya tashi tarwatsasuu a lokaci daya zaiyi ba tare da bata lokaci ba... Mrs tijjani shattima... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣8⃣ By Aysha Ya'u Kurah Sati ďaya ya rage bikinsu, lokacin yayi daidai da kammala jarabawar su Afee, Fitowarsu kenan daga exam hall ita da safnah kowannensu sai share zufa yakeyi, skul mosque suka wuce sukayi sallah suka zauna bin inuwar gurin saboda gajiya, hira sukeyi duk akan jarabawar da suka zana yau kuma ta karshe, sai da suka fi minti talatin sannan suka mike da niyyar tafiya gida, a dai2 gate din fita makaranta suka tsaya ganin anyi cincirundo kan wani yaro ďan ss2, Afeeyah tayi tsaki tace dadina da skool dinnan son gulma dan Allah ji yadda aka wani zagaye yaron can kowa so yakeyi yaji abinda ya sameshi, safnah tace may be abin da ya sameshi babba ne dan kuka yakeyi sosai gunin ban tausayi, Afeeyah tace to Allah ya kyauta muje ko, safna tace ga "Zulaikha Sambo" can tahowa bari tazo muji me ya faru, Afeeya tayi tsaki tace dan Allah safnah mu tafi wato kema kin fara son jin abinda bai shafeki ba ko, kafin safnah tayi magana zulaikha ta karaso gurin su, safnah tace Zully me ke faruwa a can gurin, zully tayi fuskar tausayi tace wallhy mahaifiyar waccan yaron ce ta rasu yanzu aka zo aka faďa mishi, safnah tace ayyah Allah ya jikanta mutuwar mahaifiya ay babbar cuta ce tanada zafi sosai walhy, Afeeya da jikinta yayi sanyi tace Allah ya rahamsheta mu kuma yasa mu cika da imani, suka amsa da ameen, safnah tace ay mune abin tausayi Afee, gara ke tun kina karama kika rasa taki yanzu zaiyi wuya wata mutuwa ta girgiza ki, zully tace kwarai kuwa,, Afeeyah tayi murmushi tace har gobe ina tunawa da mamana duk da bawani daďewa mukayi tare da ita ba, wallhy kullum na kalli hotonta sai na zubar da hawaye, mutumin dake debe min kewar tunaninta tun ina karama shine wanda bana fatar rasa shi har karshen rayuwata, ta kalli safnah tace kikace babu mutuwar da zata girgiza ni, to wallhy kinji na rantse da Allah bana fatan mutuwa akan yaya Jabeer amma ni nasan duk ranar da aka ce min ya mutu to nima binshi zanyi in kuwa lokacina baiyi ba to walhy ko in haukace ko in zama marar amfani, dariya suka saka sosai safnah tace ay ke baki da hankali, da in mutum na mutuwa ana binshi kuma Allah baya sa dangana da duk wadanda suka rasa makusantansu suma sun dade da mutuwa, Afeeyah tayi tsaki tace dan Allah ya isa haka maganar mutuwar Allah yasa mu cika da imani, suka amsa da ameen sannan suka wuce zuciyar Afeeyah a dagule dan ta tsani zancen mutuwa... Ranar haka Afeeyah ta wuni sukuku, wasu irin muggan tunanin mutuwa takeyi, da taga abin bazai fishsheta ba sai ta ďauki qur'ani ta fara karantawa, a haka jabeer ya tadda ita, gaisheshi tayi haďe da ajiye alqur'anin a mazauninshi, kusa dashi ta dawo ta zauna

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});