Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 31

Chapter 31

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

abinci in dinga yin bismillah, da karfi yace "bismillah", oyizah ta buge bakinshi da karfi ba tare da tasan tayi ba, washhhh Affan ya faďi da karfi yana kallonta idonshi ya fara kawo ruwa yace mummy me na miki, ta dafe kanta tace Affan wadannan mutanen sun koya maka abubuwan da zai kasheka, Affan ya fito da ido waje yace "kasheni" mummy? Ta rage murya tace yess, kaga wannan bismillahr da yace kayi, to daga ka kuma yinta zaka mutu, Affan yace to ai jiya munyi sosai harda wani karatu ma duk munyi kuma ban mutu ba, oyizah ta mike ta riko hannunshi tace zo muje in fada maka wata magana, ya mike ya bita daki ta zaunar dashi gefen gado ta fara tsoratar dashi sosai akan sallah da wasu abubuwan da kaka liman ya koya mishi sannan tace mishi kasan inda abokinka yake, ya girgiza mata kai cikin tsoro tace to ya mutu kaga irin mutuwar da akeyi a cikin film mutum ya fadi ya daina motsi, Affan yace ehh, tace to shima ya tafi bazai kara dawowa ba saboda halin shi bashi da kyau, mugu ne so yakeyi ya kasheka shiyasa yake yawan zuwa yace kuje kuyi sallah, Affan yayi narai narai da ido yace mummy ba mugu bane, yana kawo min cwts, baya dukana kuma baya min ihu kamar yadda su anty salma suke min, oyizah tace muguntar kenan ay saboda yanaso ya kasheka wata rana shiyasa yake maka haka, amma kaga saboda am wit u gashi yanzu ya mutu har an kaishi rami, ka manta dashi kaji Affan din daddy, Affan ya gyaďa kanshi hawaye suka sauka a kuncinshi wanda shi kanshi baisan yanda akayi suka fito ba, maganganu ta cigaba da yi mishi tana kara tsoratar dashi har saida ta tabbatar ya tsorata sannan ta kaishi ďaki ya kwanta tababbiyar zuciyarshi na karyata maganganunta akan jabeer,, Daki ta koma tana sauke ajiyar zuciya dan ba karamin yaki tayi gurin sanyawa Affan tsoro a ranshi ba, a zuciyarta tace tabbas sai tayi da gaske dan mutuwar jabeer na neman karya duk wasu alkadarinta..... Mrs tijjani shattima...... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣6⃣ By Aysha Ya'u Kurah Da sassafe alhj basheer ya shigo dakin ya tarar da Affan zaune a lallausan gadonshi yayi tagumi, a hankali ya cire hannun da yayi tagumin dashi yace me ya sameka dan daddy, Affan ya kwanta kan cinyar daddy yace daddy Afeeyah tana can a gida tana kuka, ya ďago kanshi da ya ciko da kwalla yace daddy abokina ya zo yace in je in rarrasheta, alhj basheer yayi murmurshi dan ya dauki maganarshi shirme yace in ji wa yace maka tana kuka, Affan yace jabeer ne ya faďa min, alhj basheer yace a ina kaga jabeer din, Affan yace ana ruwan sama na ganshi a window na, alhj basheer ya shafa kanshi cikin mamakin yadda akayi kwakwalwar Affan ta fara rike mafarki yace tashi kaje kayi wanka zan je in rarrasheta anjima, Affan yace to daddy yaushe zata dawo nan gidan sai in dinga rarrashinta, Alhj basheer yayi hanyar waje yace kayi wankan kazo ka karya tukunna, Affan ya mike yayi hanyar bayi yana kallon window inda yaga jabeer cikin baccinshi amma shi ya kasa gane mafarki yayi dan ya hakikance a zahiri yaga jabeer, bayi ya shiga yayi wanka ya jika ko ina kamar yadda ya saba har ya bude pampo zaiyi alwala kamar yadda kaka liman ya nuna mishi sai kuma ya fasa saboda tuno kalaman oyizah, da sauri ya fito daga bayin ya shirya cikin matsatsun kaya... Alamarin Affan ya fara bawa alhj basheer tsoro saboda kullum sai yayi mishi magana akan ya dawo mishi da Afeeyah gidansu, abinda yake fin bashi tsoro bai wuce yadda yake haddace mafarkan da yakeyi akan jabeer ba, yawan mafarkin da yakeyi ne ma yake hanashi tambayar inda abokinshi yake saboda yana ganin kamar a zahiri yake ganinshi,,, duk wannan mafarkin da Affan yakeyi bai taba faďa ma oyizah ba dan ko yazo zai faďa mata sai ya fasa ya kama harkar, daga shi sai mahaifinshi kadai suka sani... A ranar da za'ayi sadakar bakwan jabeer kuka sosai Affan ya tsare mahaifinshi dashi akan shi gobe in ba'a kawo mishi Afeeyah gidan nan ba bazai kara cin abinci ba, hankalin alhj basheer ya tashi matuka saboda yadda Affan ke kuka harda majina, dakyar ya lallabashi yace gobe in shaa Allahu zan dawo maka da ita gidannan kaji, Affan ya share hawayenshi ya rungumeshi cikin jin dadi yace bari inje in faďa ma mummy sai tayi mata abinci mai dadi ko, alhj basheer ya gyaďa kanshi, Affan ya tashi ya fita yana ihun murna, binshi alhj basheer yayi da kallo a zuciyarshi yana tunanin yadda zai tinkari alhj bara'u da mahaifin Afeeyah da maganar auran mahaukacin danshi dan in ba aure ba babu abinda zai kawo Afeeyah gidanshi ta zauna, dakinshi ya wuce yana jiyo ihun Affan a waje yana yi yana tsallen murna.... Da wuri aka idar addu'ar bakwai akayi sadaka sosai mutane suka watse, alhj basheer zaune a parlon alhj bara'u suna yar hirah jefi2, alhj Bara'u ya kalli alhj Basheer yace alhj tun a gurin addu'a na lura da yanayinka kamar wani abu na damunka, alhj basheer yayi ajiyar zuciya yace wallhy alamarin yaron nan ne ke matukar bani tsoro, alhj Bara'u cikin damuwa yace alhj Basheer kenan ay cuta kaffara ce, ka dinga godewa Allah da lalurar da ya ďaura mishi dan shi kadai yasan sirrin dake cikinta, gara kai ma zaka kalleshi a haka kaji dadi, yayi murmushi mai ciwo yace Allah ya kai rahama kabarin jabeer, alhj basheer yace "ameen" amma ni ba ciwon Affan bane ya dameni, wani abu yake so inyi wanda a ganina son zuciya ne in har na yarda na biye mishi, alhj bara'u yace menene shi alhj, nan alhj basheer ya faďa mishi duk abinda Affan ke faďa mishi game da mafarkinshi, alhj bara'u yayi ajiyar zuciya zaiyi magana kaka liman ya shigo da sallama, da sauri suka mike suna mishi sannu da zuwa dan ya koma Daura tun ranar uku, zama yayi a gajiye yana amsa musu, bayan sun gaisa Amirah ta kawo mishi abin kari ya zauna kamar ba gidan ďanshi ba dan baida wannan kauyancin akanshi yaci abincinshi son ranshi yana ci suna hirah, alhj basheer ya kalli alhj bara'u yace bari in tafi anjima ma karasa maganar, kaka liman yayi maza cikin wasa yace zauna tare za"a karasa maganar dani in dai ba ta gulma bace, suka kwashe da dariya suka ce bata gulma bace kaka, yace to a cigaba mana, daga ganina sai ku bari, alhj bara'u yace to Baba bari mu cigaba kaima sai ka bada shawararka, yayi murmushi yace to inaji, alhj bara'u ya fada mishi komai kamar yadda alhj basheer ya fada mishi, kaka liman yayi murmurshin jin daďi a zuciyarshi yace ikon Allah kenan jiyan nan nake tunanin yadda zanyi a karasa burin jabeer sai gashi cikin sauki wacce yakeso ita zata karasa aikin da ya dauko na amininshi, tabbas akwai wani boyeyyen alamari a cikin wannan auren in har ya ďauru, ya kalli alhj basheer yace to meye abin son zuciya anan, aure fa kace bawai

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});