Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 61

Chapter 61

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 931 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta mike kafarta tana tsinkar ayayo, yara kuma na gefenta suna wasa, jabeer kuwa yana zaune yana shan cornflakes yana kallon cartoon, Amirah ce ta shigo gidan tana ma jabeer wakar tsokana, hararrta yayi ya cigaba da kallonshi, kanshi ta taba tace su jazuli ba tayi, ya buge hannunta ya turo baki yace kece jazuli, Amirah tayi dariya ta zauna kusa da Afeeyah ta dauki sandar ayayo daya tace har yanzu su umma basu dawo ba, Afeeyah tace kedai bari ina missing dinsu wallhy ko dan wancan dargozon, Amirah tayi dariya tace ummi ce ta aikoni tace ki tambayi yaya Affan gobe zanje kaduna wai su Nawwara su shirya mu tafi tare, Afeeyah tace to ba matsala amma banda jabeer ko, Amirah tace wake gaba in ba shi ba, kin san anty asiya in bamuje dashi ba sai munsha query, Afeeyah tace wallhy masifarshi ce bana so, gashi in sun hadu da irfan dinta suyi ta fada kamar jakai, Amirah tace ay duk daya suke mugun rashin jin tsiya, Afeeyah tace ay inaga ke zamu hadawa kuje can ku karata ke da angon ki, Amirah ta rike baki tace akai singa market, ta ina zan fara dasu, Afeeyah tayi dariya tace hanyoyi da dama, Amirah ta mike takai ayayo kitchen tace bada ni ba sa lallen hen, Afeeyah tayi dariya ta mike ta bita kitchen... Karfe 12 na rana driver ya kwashesu suka tafi kaduna, dawowa ciki Afeeyah tayi tace yau zan huta da fitina, dakinta ta wuce ta kwanta tayi bacci, karfe biyu da kwata ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan ta fara gyare gyaren gidan kafin mai gidan ya dawo, Karfe 6 suka gama komai ita da mai aikinta, ta wuce tayi wanka tayi sallah ta shirya cikin free gown mai shegen kyau, parlor ta dawo ta zauna ta canza tashar zee world ana sacred ties, nan tayi paying attention saboda tana matukar son film din, a hankali ya shigo gidan bata san ya shigo ba, ta baya ya tsaya ya ziro macijin roba ta saitin kafarta yana mata waiwayi, a gigice ta kalli kasa, wani irin tsalle ta daka hade da ihu tana fadin na shiga uku na lallace wayyo hajja, wayyo kuzo ku taimakeni, rungumeta yayi ta baya yana dariya sosai yace matsoraciya kawai, ďanewa tayi kan jikinshi ta kankameshi tana faďin maciji, wallhy maciji na gani, dariya sosai yakeyi ya sa macijin a saitin kunnenta, wani ihun ta kara sawa tayi saurin turashi baya cikin masifa tace wannan ay mugunta ne, kasan inada larura kuma kake tsorata ni, yanzu fisabillilahi da karamin ciki ne na haka zakayi min, wurgo mata macijin yayi ta goce ta dauko shi ta fara buga mishi tana masifa, chakk ya ďauketa yana dariya yace am sorry sweety, tasa baki a kunnenshi ta cijeshi da karfi yayi saurin direta yana ihu, daki ta gudu tana dariya sosai tace gobe ma ka kara, bin ta yayi yana dariya yace wallhy sai na rama yau sai jikinki ya faďa mishi, zaki san kin cijeni, da sauri tasa ma kofar key tana dariya tana faďin sai dai ka rame a nan, yayi dariya yace zaki ga rama zaki fito ki sameni ya wuce ďakinshi... Haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya cikin farin ciki, Afeeyah ta kara haihuwar ďa namiji wanda yaci sunan Basheer, abba suke ce mishi, yanxu haka tana final year ďinta a "international relationship" dan tana matukar kaunar course ďin.. To ALHAMDULILLAH, Nan zan tsaya da wannan kagaggen labarin nawa, Godiya ta musamman ga Allah s.w.t da ya bani ikon farawa kuma na gamashi ba tare da na gaza ba, alkhairin da muka fada ciki Allah ka bamu ladanshi, sharrin dake ciki ya Allah ka yafe mana.. Allah ya kara muku tsawon kwana mahaifana waďanda sukayi sanadiyyar zuwana duniya, Allah yayi muku sakamako da gidan aljanna firdausi,,, Allah ya barmu tare mijina, ya kauda duk wata fitinar dake cikin auren mu, Allah ya raya mana zuri'armu kan tafarkin Addinin musulunci,,, Jinjina ga kungiya mai albarka. HANNU DA YAWA WRITERS, Allah ya kara haďa kanmu ya kauda fitina a tsakaninmu... Godiyah ta musamman gareku yan fcbk nagode sosai da soyayyarku gareni, ... Aysha kurah novels... Khaleesat haydar novels... deeja abdul novels.... Mu sha karatu.... Dama sauransu.... Banda kamarku... kawata ta da da yanzu 😀 Badiyya Aliyu umar, Namcy Dangusau, $ Aneesah Abdulsalam.... Godiya ta musamman gareku yan uwana masoyana yan "world of Hausa novels 1 nd 2," bansan wanda zan tsame in kira sunanshi a ciki ba MAXXY, NI'MA NAKOWA, NABAYI, BIEBEE, SADEE, NAMSY MISAU, HASKE, ASMEE YA'U, SOFTIE, DEEBOX ku fito ku tayani lissafo sunansu,,, thanks for ur support dearies Allah ya barmu tare... jinjina gareku yan uwana yan group ďin Ruffy na classic ladies novels nd ROF novels, Allah ya barmu tare ameen, Godiya gareku.. Yan group din kawalli ummu abdool, Taskiraa.. ku ma Allah ya barmu tare, Hausa novel group na sheedat.. Hausa novel group na Raff... Zauren karatu... Feenat jaafar novels... Excellent writers... Wisdom writers... Perfect writers... M jabo novels... Only hausa novels.... Fasahar marubuta.... Matan kwarai.... Hausa novels na Pherty.... Hausa Novels na chuchu Ammani.... Zarah bb novels.... Meesha love novels.... Fillin takarddun hausa.... Khadija candy novels..... Taskar ya'ya mata.... Sahaf's novel ... Best hausa writers.... Kamshi novels..... Haima fans.... Autar hajiya novels.... Da duk sauran groups ďin da ban anbata ba kuna raina Allah ya bar mu tare cikin Aminci da kaunar juna.. Ga masu bukatar littafai na, kuyi searching blog ďina ayshakurah.mywapblog.com ko kuma facbuk group dina Aysha kurah novels Mrs tijjani shattima kema dukkan masoyanta fatan alkhairi Allah ka hada fuskokinmu a cikin aljanna firdausi...

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});