Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 35

Chapter 35

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

saurin rufeta dan kar wani ya ganshi ...... Mrs tijjani shattima..... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣0⃣ By Aysha Ya'u Kurah Kallonshi Afeeyah ta tsaya yi har ya rufe kofar ya waigo yana mata murmushi, kau da kanta tayi ta janyo hijab dinta tasa ta zauna a gefen gado, karasowa yayi yana kaďa kanshi yana dariya ya tsuguna a gabanta ya daura hannunshi kan nata yace barbie yau kin dawo gidan mu ko,, ta juyar da kanta gefe, ya taso ya zauna kusa da ita yayi narai2 da ido yace abokina ya faďa min kullum kina kuka da daddare meyasa kike kuka? Afeeyah da idonta ya ciko da kwalla ta kasa ce mishi komai sai kallonshi da takeyi, hannu yasa ya share hawayen da ya digo a idonta yace ki mayar da hawayen nan dan Allah karkiyi kuka abokina zaice ni nasaki kuka in yazo, Afeeyah ta kara fashewa da kuka a zuciyarta tana mai tausayawa ranar da Affan zai san jabeer ya bar duniya, kukan shima ya fara yi kamar karamin yaro yana share mata hawaye, wata tsawar aka sake saki mai firgitarwa kamar zata rusa gidan saboda kararta, da sauri Affan ya shige jikinta ya kankameta haďe da runtse idonshi, wani abu mai wuyar faďuwa yaji ya tsarga mishi a cikin kwakwalwarshi, wani irin shauki ya dinga ji a can cikin jikinshi, shi kanshi ya kasa fassara yanayin daya shiga a wannan lokacin, Turashi Afeeyah ta farayi tana kokarin mikewa tasa kaya, kara kankameta yayi dan bayason ya daina jin abinda yakeji, kallon fuskarshi tayi a hankali taga idonshi a lumshe yana fitar da wani irin numfashi, tausayi ya bata sosai saboda yadda ya koma cikakken mutum a haka kafin anjima ya birkice ya koma tababbe, a hankali ya bude idonshi da ya fara canza kala ya saukesu kan nata, da sauri ta kauda kanta tace dan Allah ka sakeni in sa kaya bacci nakeji, sakinta yayi cikin muryar lafiyayyan mutum yace "muje in tayaki sawa" cikin mamaki ta zaro manyan idanuwanta tana kallonshi, murmushi yayi mata ya mike tsaye ya bude drawer ya dauko mata cotton night gown ya mika mata, kasa amsa tayi tana mishi kallon mamaki, ajiye rigar yayi a jikinta ya hura iska cikin idonta yace ko ni zan sa miki da kaina, tayi saurin kauda kanta ta ďauki rigar ta faďa bayi tana tunanin canzawarshi lokaci Guda, tsaye ta sameshi gaban mudubi yana zana kanshi yana dariya, ta mudubin ya hangota ya juyo da sauri ya janyota yace zo kigani na iya drawing mutum a mudubi, tsaya anan kigani, Afeeyah ta girgiza kanta tace bacci nakeji, ya girgiza kai a shagwabe yace ni sai kin tsaya, Afeeyah ta haďe rai ta juya ta wuce kan gado ta kwanta, zama yayi a kujerar dressing mirror yana kumbure2 yana kunkuni shi a dole an mishi laifi, Ko kallonshi batayi ba tayi kwanciyarta ta shige bargo tana karanto adduoi, muryarshi taji saitin kunnenta yana faďin Niko? Niko? Ya faďi haka yafi sau goma Afeeyah tayi tsaki ta yaye bargon zata fara masifa hawayen da ta gani kwance a kuncinshi ya hanata, ta kalleshi murya a tausashe tace me nayi maka kake kuka, ya kwanta kan cinyarta yace bake bace kika ki tsayawa inyi drawing dinki ba kuma kika tafi kika barni baki bani hakuri ba, sai na fadama abokina ince barbien shi ta daina kirki yanzu, Afeeyah tasa hannu ta share mishi hawaye tace kayi hakuri gobe zan tsaya yanzu bacci nakeji, Affan ya ďago kanshi ya kalleta cikin ido yace ni bana jin bacci zaki rarrasheni inyi bacci, Afeeyah ta dafe kanta kwalla ta cika idonta a zuciyarta tace ni kuma kaddara ta kenan, kwanciya tayi ba tare da ta bashi amsa ba tana hawaye tana hango da yanzu fa tana gidan masoyinta abin kaunarta jabeer, hawa gadon Affan yayi ya kwantar da kanshi a bayanta, nan ta fashe da wani irin kukan da yasashi saurin kankameta yana rarrashinta, runtse idonshi yayi yana sake jin abin da yaji dazu, a hankali kwakwalwarshi ta fara daukar caji ya shiga shinshina jikinta yana lumlumshe ido, kara matseta yayi lokacin da hannunshi ya sauka kan kirjinta a take ya saki ajiyar zuciya yana wani irin nishi, cire hannunshi ta fara kokarin yi ta kasa saboda irin rikon da yayi mata, yafi minti biyar a haka yana sauke ajiyar zuciya yana sauraron kukanta da yake jinshi kamar waka a wannan lokacin, mirginowa yayi ya ďago fuskarta idonta a rufe ya fara share mata hawaye haďe da bata hakuri, bata bude idonta ba kuma bata tsayar da hawayen ba, kwantowa yayi ya haďa fuskarshi da tata yana gogawa a hankali, cikin kuka ta bude baki zata fara masifah yayi saurin tura bakinshi cikin nata, duk yadda taso fitar da bakinshi ta kasa saboda sam ya hanata damar hakan, wani irin rikitaccan alamari ta dinga gani a tare da wanda tasan bashi da isashshen lafiyar kwakwalwa, Shi kuwa Affan sam baya cikin hayyacinshi bare ya tantace a tsakanin duniyar mahaukata ko a ta lafiyayyu yake, babu inda baya rawa a jikinshi, gani yakeyi kamar duk cikin wasa yakeyin abinda yakeyi sam ya kasa tsayawa da wannan wasan saboda ba kananan abubuwa yakeji na shauki a cikin jinin jikinshi ba, a wannan lokacin duk iya kokarin turashi hade da kukan da Afeeyah takeyi bai sa ya daina ba saima shiga yin wasu abubuwa na daban da yayi dan a yadda yakejin kanshi in har ya daina wasannan da yakeyi to tabbas zai iya rasa ranshi, wani irin kuka Afeeyah takeyi na takaici da bakar azaba tana kiran sunan jabeer dan abubuwan da Affan yake mata sun zarce tunaninta, "Ni kaina danake dauko rahoto saida na tsorata nayi fitar da babu shiri harda buge kafa saboda sauri dan Affan ya matukar tsoratani yadda ya dinga sarrafa Afeeyah kamar cikakken mai hankali" A bakin kofar na tsaya ina jiyo muku kukan Afeeyah wanda takeyinshi kamar ana yankata, sai karar ruwan sama da ake tsugashi kamar da bakin kwarya,, barin kofar ďakin nayi na juya gurin da nake jiyo magana kasa2, a hankali na karasa side din mummy wacce ta fito daga dakin alhj basheer, tsaye na same ta a bakin kofar dakin da ta bawa Affan tana magana ita kadai tana fadin ina yaron nan ya shiga, kardai yaron nan gurin yarinyar nan ya tafi, cikin bacin rai tayi kwafa ta kama hanyar side din Affan....... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣1⃣ By Aysha Ya'u Kurah Muryar alhj basheer taji da karfi yana faďin ina tea din yake ne safiya, sai a sannan ta tuno da abinda ya fito da ita daga dakin har taga kofar Affan a bude, hanyar kitchen ta nufa cikin gaggawa ta hado mishi tea ta koma dakin ta mika mishi, ya dafe kanshi yace ina maganin, da sauri tace ba kai ka ajiyeshi ba, yayi tsaki yace na manta inda na ajiyeshi duba min ko cikin drawer ko kan mudubi, cikin bacin rai oyizah ta fara duba maganin da kyar ta ganoshi a drawer gefen gadonshi ta mika mishi da sauri, ya kalleta yace yau ko ballo min maganin baza'ayi ba, ta amsa ta babbalo mishi

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});