Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

saita daura a kan cibiya da marar jaririn tana karanto adduoi tana tofa mishi, juyawa oyiza tayi da sauri da ta tunkaro dakin da wasu magungunan tsafinta wanda chummy tace in har ta shafi babyn da maganin a hannunta to tabbas jininshi zai kafe ya mutu, jin hayakin tayi kamar zai tafi da ranta, ta shiga daki da sauri ta datso kofa tana haki haďe da kakarin amai, ta dade sosai a haka kafin wani irin murdaddan ciwon mara ya dawo da ita daga duniyar azabar shakar hayakin habbatis sauda, ciwon da oyiza taji ne yasata sakin ihu tana karawa kamar zararriya, babu wanda yajita dan su yadikko suna can suna hira dasu hajja da suka shigo a lokacin sunata preparation din suna washe gari, sai da ta galabaita sosai tana ihu tana faďin "ohh my lord" "chummy wr are u," Ma'u ce ta fara jin ihun saboda zagayawa baya da tayi dan kwaso shanyar baby, da sauri ta zagayo ta faďa musu suka mike sukayi dakinta suka murďa sunata bugawa yaki buduwa saboda tasa key, kiran alhj basheer zeenatu tayi lokacin har oyiza ta suma saboda azaba, cikin yan dakiku ya baro inda yake ya dawo gida ya dauko spare key ya bude dakinta, kwance cikin jini suka sameta, da sauri suka karasa suka kamata suka sata a mota sai asibiti, dakin theater aka wuce da oyiza, cikin gaggawa likitoci suka shiga ceton ransu ita da babyn, cikin nasara suka samu fitowa da baby mai kyan gaske gata katuwa dan da sukayi wghn dinta ta kai 6.2kg, doctor yayi ma oyiza "PS" nurses suka shirya baby suka fito ma alhj basheer da ita, cikin murna ya karbeta yana kallonta yana mata addua, ita kuwa oyiza sai can cikin dare ta farfado tana ihun kuka dakyar,,,, wata nurse ce a gefenta da yadikko suka matso suka riketa suna fadin sannu, ta kwanta lamoo tana shafa cikinta dakyar tace na haihu ne, yadikko ta daga mata kai tace eh kin haihu, tayi murmushin da bata san ya fito ba saboda azabar ciwo tace ina yaron yake, yadikko ta fito da babyn cikin gadon jarirai tace gata nan, oyiza cikin rashin fahimta ta gwalo dasassun idanuwanta tace gashi nan ko gata nan, yadikko tace gata nan dai inaga bakiji da kyau bane, oyiza ta waigo a hankali ta kalli babyn ta juyar da kanta tana kuka sosai tace "why chummy" why? Meyasa zan haifi mace, kin manta alkawarin da kikayi min, meyasa zeenatu zata haifi namiji ni mace, meyasa zanyita haihuwar mata, magana oyiza takeyi cikin zaucewa tama manta da wata yadikko a kusa da ita, saida tayi kuka sosai nurse tazo tayi mata allura sannan ta samu bacci, Yadikko komawa tayi ta zauna tana kallon oyiza tana mamakin furucinta, tabbas sai sun mike tsaye akan zeenatu da ďanta saboda wannan furucin na oyiza ba karamin ďaga hankalin yadikko yayi ba, '"CHUMMY" kalmar da ta dinga maimaitawa kenan a ranta, wacece kuma chummy? tambayar da yadikko tayi ta ma kanta kenan ta kasa samo amsa daga karshe ta mike ta shiga tayi alwala ta fara nafilar nemawa jikokinta tsari daga sharrin makiya... Ranar suna jariri yaci suna AFFAN, anyi taron suna na gani na fada mutane sunzo sosai tayasu murna, faďin farin cikin da duka su biyun suke ciki bata lokaci ne domin bazai taba misaltuwa ba, oyiza kuwa tana can cikin bakin ciki dan tunda ta farka anyi anyi ta bawa baby nono taki, kuka kawai takeyi tana tufka da warwara, maimakon isharar da Allah ya nuna mata yasa ta saduda tasan babu wani mai yi sai shi taki ta gane, sam batayi gv up ba sai ma wani karin mugunta da zuciyarta ta naďo, babu abinda yafi daga mata hankali sai cewa da doctor yayi mahaifarta bazata kara rike kwai ba saboda ta samu gagarumar matsala, a wannan lokcin likitoci sunga bori saboda tsine musu kawai takeyi tana zaginsu, dakyar alhj basheer ya lallabata da kalamai masu kwantar da hankali,,, Kwananta hudu a asibiti aka sallameta ta dawo gida da muggan kudirai a cikin ranta, a zuciyarta tace wannan karan ita zata zama shaidaniyar kanta dan taga yanzu aikin chummy baya tafiya mata yadda ya kamata, haka ta cigaba da jinyar jikinta da kula da yarta wacce taci suna FAREEDAH, oyiza kullum idonta na kan side din zeenatu taga ko sun bar Affan shi kaďai amma bata samun wannan damar saboda yadda yadikko ke manne dashi a ko dayaushe, sai da yadikko tayi wata biyu a gidan tana kula da zeenatu, tun ana saura sati ďaya ta tafi kullum dare bata aikin da ya wuce yi ma zeenatu faďa akan ta kula da kanta da ďanta da kuma adduoi, zeenatu saidai tayi dariya dan abin na yadikko ya zame mata kamar waka tunda kullum sai anyi maimaicinshi.. Cont 14 Salma ta kalli mahaifiyarta tace mummy kika ce wannan nawa wannan na affan ko, oyiza tace a'a wannan ne naki, ki kula fa sosai, ta gyaďa kanta ta fita da gudu fareeda na binta a baya, Affan zaune suna bin karatun lptp din yara na "alifun ba'un" shi da jabeer lokacin shekararsu biyu da rabi shi da fareeda ita kuma salma ta kusa 6, dafashi salma tayi yayi saurin ďago kanshi, a razane ya matsa dan mugun tsoronta yake ji saboda dukkan da take mishi, zama tayi kusa dashi ta kara duba ice cream din dan ta tabbatar da wanda mummy tace na affan din ne, mika mishi tayi tana murmushi tace gashi inji mummy, farida cikin gwaranci tace "wanshan ne naci," salma ta harareta tace wannan ne, farida ta dage akan dayan ne saboda tafi salma wayau, kuka ta fashe dashi da taga alamar salma bazata bashi wanda mummyn tace ta bashi ba, da sauri zeenatu ta fito tace lafiya me aka miki farida, salma tace ice cream mummy ta bani in kawo ma affan kuma wannan ne nashi wai ita dole sai dai in bashi Nawa, farida cikin kuka tace "wanshan ne mummy ta kaya mici sugar" kuma "cha kiji" , gaban zeenatu ya faďi sosai tace to duk bari in raba muku gardama ke salma je ki kara tambayota wanne ne na affan din, da gudu suka fita suka bar zeenatu cikin jimamin maganar farida, innalillahi kadai take fada tana kara rokon Allah ya tsare mata ďanta da a kullum sai an kawo mishi harin kisa tun yana karaminshi, shafa kansu tayi shi da jabeer tace ma jabeer tashi kuje gidan Antie Ma'u kafin umminka ta dawo kaji, ya gyada mata kai ya kama hannun affan dan yafi affan wayau, har sun fita ta tuna da kar su hadu da su salma ta bashi ice cream din yasha, binsu tayi da sauri tace ku dawo bari Gaje ta dawo daga kasuwa sai ta kaiku kunji, ta kamo hannunsu suka shigo ciki dai2 lokacin su salma suka dawo da ice cream daya suka ce gashi wannan ne nashi, zeenatu ta amsa tace to kuce ya gode sosai, salma tace mummy tace yasha a gaban mu sai mu tafi, zeenatu tace to an gama yaran kirki bari in raba musu shi da jabeer, ta mike ta shiga kitchen, Allah ya taimaketa akwai nashi na jiya a fridge, daukowa tayi ta

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});