Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a dai2 kofar dakin inna suwaiba kausar ke zaune tana ganinsu ta shiga wakar habaici tana fadin Allah wadai da halin yan iska sai a shige daki afi karfin awa wai da sunan ana hira, ran Afiya ya baci matuka jabeer ya lura da hakan ya rike hannunta gam ta fisge, tace da uban wa kike , kausar ta mike tace da ubanki nake kinji na kira sunanki, in ba tsarguwa kikayi ba meye na jin haushi shegiya marar kunyar banza, Afeeya ta kuma hassala tayi kanta da sauri jabeer ya riketa da iya karfinshi ya jata da kyar suka fita, kukan bakin ciki ta fashe mishi dashi tana ta tirje hannunta, murmushi yayi dan yasan in bata tsaya ta mayar da martani ba bazata taba hucewa ba, hakuri ya shiga bata amma ko kalma daya bata iya rikewa ba saboda zuciyarta cike take da bakin ciki gani take idan basuyi fada da kausar ba yau sai tayi ciwo mai tsanani, matsowa sosai yayi kusa da ita yace haba afee nah, ba nace kiyi hakuri ba, kinaso inyi fushi ne, ta turo baki tana kuka tace ko zaka fashe yau bazanyi hakuri ba, ya hade rai yace to ni kuma in bakiyi hakuri ba mun bata garin ma zan bari gaba daya, cikin dakewar zuciya tace ka tafi gaba da birnin sin ma dan wallhy bazan hakura ba, sakin hannunta yayi yace ni ko? Ta juya mishi baya tace eh ďin, yace to shikenan bye yasa kai ya fita, ko ajikinta a lokacin saboda zuciyarta na azalzalarta taje gurin kausar....... Mrs tijjani shattima..... [15/12 09:32] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣ By Aysha Ya'u Kurah Tana shiga ta tarar da kausar na buga k'ullun alale, sam kausar bata kula da shigowarta ba sai saukar wata sanda taji akanta da karfi, zafin ya gigita ta sosai tasa ihun da ya fito da inna suwaiba da hajja daga ďaki, cikin rudewa inna suwaiba ta kama kausar tace kausar meya faru, kausar ta kasa magana sai kuka takeyi hannunta rike da gurin jini na fita, hajja ta kwace sandar hannun Afiya tace yanzu ke saboda tsabar mugunta wannan murďaďďiyar sandar kika buga mata, Afiya ta turo baki tace hajja fa baki san abinda tayi min bane shiyasa, inna suwaiba cikin fushi ta saki kausar tace uban me ta miki, Afiya ta murguďa baki tace gata nan ki tambayeta, inna suwaiba tace lallai yau za'a haifi ďa mara ido a gidannan wallhy, Afiya tace a haďa harda mara hanci ma a haifa, hajja ta bige bakinta tace ke wai wace irin yarinya ce da baki jin maganar kowa, Afiya tace to wai hajja ita baki tambayeta me tace mana ba, ce mana fa tayi yan iska, inna suwaiba tace ay kunfi karfin ya'yan iska saidai na guguwa, wallhy yau saina miki shegen duka a gidan nan sai na tabbatar wannan tsinannan bakin naki yayi laushi, Afiya tace Allahn da halicci baki na shi kadai zai iya sashi yayi laushi ba wata ca--- hajja ta toshe mata baki tace na shiga uku ni Giďe, yanzu ke Afiya bazan miki magana kiji ba, inna suwaiba tace hajja ki wuce daki ki barni da yarinyar nan wallhy yau sai na mata lahani a gidannan, Hajja tace kiyi hakuri suwai--- karki bani hakuri ki cuceni hajja kullum mu kenan a cuce mu a taushe mu, to wallahi bazan dauka ba, ji yadda jini ke zuba a kan kausar ay dan tasan kuna daure mata gindi ne ke da malam shiyasa take abinda takeso, in ba ta raina mutane ba ay kausar ba sa'arta bace, hajja tace kiyi hakuri dai nace suwaiba, Afiya ta harari hajja tace wai hajja hakuri kike basu ni baki bani hakuri ba sai su da babu abin ma da nayi musu, inna suwaiba ta hassala sosai tayi kan Afiya ta cakumota, hajja ta riketa tace wallhy suwaiba karki taba min marainiyar Allahn nan, wallhy kika kuskura kika sata kuka sai ranki yayi matukar baci, inna suwaiba tace ay ko sai dai ya baci ta kaima Afiya duka ta goce tana kicikicin kwacewa, kausar dake jin kanta kamar dutse ta mike tazo ta bayan Afiya ta kai mata duka, Afiya tayi kukan kura ta kwace jikinta a gurin inna suwaiba ta haye kan kausar inna suwaiba na jibgarta ita kuma tana jibgar kausar, hajja na gefe tana kuka ita sam bata ma ga dukan da afiya kema kausar ba ita dai tafi jin dukan da akema Afiya, dakyar da taimakon shigowar malam faďan ya rabu kowa na maida numfashi, kausar bayan inna taje ta boye tana kuka sosai saboda taji jiki, Malam Atiku cikin bacin rai yake ma inna faďa itama cikin fushi take mayar mishi, yace yanzu in banda ke babbar kwabo ce meye na shiga faďan yara, wai ke in an barki ga mai ýa ko, kin gama zubar da mutuncinki a idon karamar yarinya, inna cikin fushi tace faďa min mai mutunci a idon wannan shegiyar yarinyar, hajja ta fashe da kuka tace wallhy ba shegiya bace, Danbaba ni na gaji da zaman gidan nan kullum sai sun tsokani yarinyar nan ita kuma Allah bai ďiga mata hakuri a ranta ba gara muyi nesa dasu su zauna su kadai a gidan, malam Atiku yace babu inda zaku hajja, baku da inda yafi nan, zan dauki tsatstsauran mataki akan wannan alamarin, inna suwaiba tayi tsaki ta hararesu tace ka daďe baka ďau mataki ba, wannan yarinyar wata rana saita dauko muku na barin gari, ta kama hannun kausar suka wuce ciki tana masifa zuciyarta na ķuna saboda Afiya, ta rasa dalilin da yasa ta kasa samun nasara akan Afiya, zama tayi bakin gado idonta yayi jajur dan ba karamin caza mata kwakwalwa Afiya keyi ba, Can kuma dakin hajja fada sosai suke ma Afiya akan rashin hakuri, malam atiku yace ni wallhy na rasa inda yarinyar nan tayi gadon wannan halin hajja ko kadan bata da hakuri komai aka mata tace saita rama kuma rayuwa bazata taba tafiya haka ba, Allah na tuba kayi hakurin ma ya ka kare a wannan zamanin bare kuma bakayi ba, hajja tace ay ni yanzu inaga nawa ido tsakanina da Afiya dan gani sukeyi kamar goyon bayanta nakeyi ni take ďaura ma bakin jini dan kawai taga banason abinda zai bata mata rai shiyasa takeson a dinga ci min mutunci, Afiya ta fashe da kuka tace dan Allah hajja kuyi hakuri in shaa Allahu ko duka na zasuyi bazan kara tanka musu ba, hajja tayi tsaki tace ke ďin ce zaki faďi magana in yarda, malam atiku yace hajja muyi mata addua babu mamaki bazata kara ba, Afiya tace Allah abba bazan kara ba, hajja tace to Allah yasa da gaske kikeyi, duk suka ce ameen, nan suka cigaba da yi mata nasiha akan rayuwar duniya cikin dabara suke mata nuni da illar rashin hakuri, Afiya jinsu kawai takeyi dan ita bataga rashin hakurin da aketa ikirarin tana dashi ba ita dai tasan ko manzon Allah s.a.w yace in aka bata maka ka rama dai2 yadda akayi maka, to ita kuwa akan me zata yarda tanaji tana gani a taka ta, bazai yiwu ba,, har suka gama nasiharsu Afiya tana gyada kai kamar taji

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});