Chapter 54
Chapter 54
rabeshi tace to naji sannan ta wuce daki tace wallhy taliya zan kwaba ma tsinannun.. Har bayan magriba baki ba su zo ba sai da akayi isha'i sannan motarsu tayi parking a kofar gidan Alhaji Basheer Balarabe (BB), su hudu ne suka fara shigowa, mata biyu maza biyu, a parlon suka zauna alhj basheer ya tsuguna ya gaisar da baffa da dayan bakon cikin girmamawa, sannan ya kalli matan suka gaisa ya kure daya daga cikinsu da ido yace kamar nasanki, tayi dariya zatayi magana oyizah ta fito tana ya tsina, dakyar ta gaida baffa shima dakyar ya amsa dan kar ace bai amsa ba, sannan tabi matan da kallon raini tace sann--- muryarta ta sarke saboda ganin Gaje da tayi, cikin mamaki tace gaje, gaje ta dago tace na'am, oyizah tace long time ina kika shiga haka tsawon shekaru uku babu ko zuwa duba mu, Gaje tace walhy kuwa aure nayi shiyasa, oyizah ta tabe baki tace na miki murna, bari a kawo muku abinci, Baffa ya kalli alhj basheer yace labarin zeenatu har yanzu shuru ko? Alhj basheer yace wallhy kuwa baffa, amma mun baza addu'a ana nan anayi kuma muna sa ran in shaa Allahu zata bayyana, oyizah tayi murmushi a zuciyarta sannan a fili tace alhj in ta mutu fa, shekara uku mutum ya bace har yanzu babu labari ay ni ina ganin ta mutu, Baffa ya galla mata harara yace bashiru ina ganin Allah ya amsa addu'armu dan kuwa na samu labarin inda zeenatu take, saboda firgici oyizah saida ta kusa karya kujerar da take kai, zaro ido tayi tace kana da labarinta, Baffa ya kalli cikin idonta yace kwarai kuwa inada labarinta mai karfi ko kuma ince ina tare da ita ma, alhj basheer ya dafa kafar Baffa cikin rawar murya yace tana ina Baffa, kafin baffa yayi magana an murďa kofar palourn an shigo, da sauri alhj basheer da oyizah suka daga idonsu ya sauka kan zeenatu da tayi wata irin muguwar rama, da sauri ya mike yana fadin z-e-e-natu, Abida da yadikko dake rike da ita suka nemi guri suka zauna, gabanta ya karaso ya kamo hannunta saboda ya gasgata ita din ce, murmushi Abida tayi tace ita ce alhj zeenatun ka ce matarka kuma uwar danka, Allah yayi zaku kuma ganawa, alhj basheer ya tsuguna a gabanta idonshi ya ciko da kwalla yace ina kika shiga zeenatu, idonta ya ciko da kwalla ta kalli gurin da oyizah ta sankare a tsaye tace na shiga cikin ukubar da bawa baya iya fitar da danuwansa bawa saidai Allah ya fitar dashi, an so kasheni amma da yake shan ruwana bai kare ba sai gashi Allah ya dawo dani bayan mutuwar danayi ta dan lokaci, mikewa tayi a hankali kamar zata fadi saboda rama, ta karasa kusa da oyizah tace ribar me kikaci a wannan izayar da kikayi mana, me kika samu mai amfani bayan tafiyarmu, meyasa zuciyarki ta zabi ta dinga kisan kai akan abun duniya da zaki tafi ki barshi a duniyar, meye ribarki dan na mutu ni da ďana ke kuma kina rayuwa keda yayanki, ki sani safiya Allah na kare wanda yaso a lokacin da yaso, kin---- oyizah tayi saurin katseta cikin tsawa tace duk wadannan maganganun na menene, ina ruwana dake da zan kasheki, me kikayi min, ta fara kukan munafurci ta matso kusa da alhj basheer tace sharri zatayi min dan kawai ta shiga duniya ta kwaso cutar kanjamau shine zata ce ni nayi niyyar kasheta, alhj inda zan kasheta da Affan shekararshi nawa ina kula dashi ban kasheshi ba, ba'ayi min godiyar kula dashi ba sai dai a bini da sakayyar sharri, kan alhj basheer ya ďaure sosai yace wai meke faruwa ne, zeenatu zata fara magana "Affan ya fito yace ni zan faďa maka duk abinda ke faruwa daddy" cikin mamaki suka mai da kallonsu kan Affan, karasowa yayi ya rungume zeenatu yana faďin baki mutu ba umma, ta dago fuskarshi tana shafawa tace kaima baka mutu ba, ashe kana nan da ranka Affan, kuka sosai suka dinga yi na tsawon mintuna, alhj basheer ya janyo Affan cikin mamaki yana shafa kanshi yace kaji sauki ne Affan, Affan ya gyaďa kanshi yace na dawo cikin hayyacina daddy, Allah ya kwatoni daga hannun wannan azzalumar da take kiran kanta matarka, farida da shigowarta parlon kenan ta karaso da sauri ta buge hannun Affan tace karka kara zagar min mahaifiya, Affan yayi mata wani irin kallo yace kice kar in kara zagar miki matsafiyya ba mahaifiyya ba, oyizah ta sa kuka tace alhj kanajin sharrin da danka yake min, ko da yake bazan ga laifinshi ba dan nasan mahaukaci ne shi baya cikin hayyacinshi, alhj basheer dai kanshi ya ďaure yace dan Allah karku rikirkitani, ku fada min abinda ke faruwa, Baffa ya kalli Affan yace zauna Affan bari mu fara jin komai daga bakin mahaifiyarka sai muji naka.. Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:38] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣1⃣ By Aysha Ya'u Kurah A hankali zeenatu ta fara jawabinta kamar haka... Ranar asabar bayan sallar isha'i ina zaune a daki sai naji kamar ana ihu acan sama gurin shan iska, da sauri na mike na isa gurin dan duk tunanina Affan ne a gurin shi da jabeer dan mun rabu dashi zaije gurin jabeer, ina isa gurin naga wasu kartin maza zaune kan wani jan kyalle da wani jan kaya a jikinsu, juyawa nayi da sauri zan koma daki saboda sun matukar bani tsoro, ina juyowa naga safiya cikin jajayen kayan itama tana dariya, da sauri naja baya ina ambaton sunanta sai naji saukar sanda a tsakiyar kaina, dishi2 na fara gani ina salati ina neman dauki gurin Allah, cikin karaji naji muryar safiya tana fadin kunji ko addu'a takeyi na faďa muku wannan sai kunyi da gaske saboda nasha yin aiki akanta yana lalacewa, jin haka yasani sake bude wani shafin na addu'a, sai naji sun ďaga ni, daya ya bankareni yana faďin zo ka shake mata wuya muga ta inda addu'ar zata fito, da sauri ya matso ya matsemin wuya inata kakari na hango wata katuwar wuka a hannun safiya tana faďin wannan gara kawai mu kasheta sai mu kaita asha jininta, tana kokarin daura wukar a wuyana muka ji ihun Affan, da sauri ta yar da wukar su kuma suka sakeni na faďa kan wani farin kyalle, daga nan ban kara sanin inda kaina yake ba saida na ganni gaban wata mata wacce halittarta kaďai ta isa ta tsoratar da mai rai, ajiyeni tayi a wani daki tana faďin yau dake zamuyi dinner, tana fita naga wasu yara su biyu sun shigo dasauri suka tanbayeni wa ya kawo ni nan, cikin rawar murya na ce musu kishiyata ce, daya daga cikinsu tace nasan oyee ce dan bata da mutunci tunda ta kawo uwarta kowa ma zata kawo, dayar tace har wani karamin yaro ma ta kawo lokacin da take neman cikin ďa namiji, cikin sauri suka ce in tashi zasu fitar dani, da sauri na mike ina tambayarsu su bazasu tafi ba, amsar da suka bani tasani zubar musu da hawaye sukace sunfi shekara ashirin a haka, yanzu gangar jikinsu ya riga ya zama kasa, wani hanya suka nuna min nayi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61