Chapter 58
Chapter 58
gurin tsoho yayi ya dinga neman wacce tayi silar zuwanshi gurin bai ganta ba, girgiza kanshi yayi yace in kere na yawo,,, sannan ya kalli su esther da suka tsure yace kuje Allah yasan yadda zaiyi daku itama waccan ogar taku banyi niyyar yi mata komai ba saida tazo cutar dani, yana kaiwa nan ya bace,, da sauri su esther sukayo kan chummy da ake iya hangen komai na tsakiyar kanta, dagota sukayi suka ga komai na kanta na zuba a kasa, a firgice suka saketa suka fara tattara kayansu, wata a cikinsu mai suna HADASIYYA ta kalli kujerar tsafin chummy, muguwar zuciyarta ta sak'a mata ya kamata ta gaji kujerar itama ta zama 1 daga cikin matsafan da ake ji dasu ta samu mabiya tayi mulkinta san ranta, murmushi tayi ta ajiye kayan hannunta tayi gurin kujerar, tun kafin ta karasa karnikan gurin da eagles suka dinga kuka irin nasu na dabbobi, tana taka step din gurin esther tasa ihu tace Hadiscos karki zauna, nan hankalin sauran yakai kanta suka haďa baki suka dinga rokonta akan kar ta zauna taxo su gudu, inaa wanda yayi nisa baya jin kira domin dai hadasiyya gani take bakin ciki suke mata dan karta fisu matsayi, tana daura mazauninta akayi sama da ita, wani irin girgiza ďakin ya farayi yana cilli da duk wanda yake cikinshi, saida ya gama cillar dasu sannan ginin ya ruso gaba dayanshi kan ragowar chummy, "hmmm duniyar chummy ta kare" saura oyizah ko ina ta shiga.... Sauki sosai ya samu a gurin Afeeyah har an sallameta ta dawo gida, tana matukar samun kula gurin zeenatu da Affan duk da ba wani sabo sosai tayi dashi ba, gyara sosai alhj basheer yasa ayi a gidan da saukar alqurani saboda shi har a lokacin a tsorace yake dan yasan indai safiya na raye to bazata taba barinsu ba, farida ma ta nutsu sosai dan islamiyya ta koma ta zama saliha gwanin ban sha'awa, tsakaninta da zeenatu ba raini sai matukar girmamawa, haka suna girmama junansu ita da Afeeyah.... 3mnts later Alhj Bara'u ne tsaye a ďakin jabeer yana duba wasu takardun Asiyah da jabeer din ya amso mata ana sauran sati biyu ya rasu, cikin drawer ya bude ya gama bincikosu ya gansu can kasan kayanshi, har zai rufe drawer sai yaga wasu takaddu a tsaftace cikin file dinsu, dariya yayi yace jabeer kenan sarkin ajiyar takardu, daukosu yayi ya rufe drawer ya budesu yana binsu da kallo, cikin mamaki yace wannan ai takardun kadororin alhj basheer ne, fitowa yayi daga dakin ya rufo kofar ya kaima Abida takardun Asiyah sannan ya wuce gidan Alhj basheer.... Mrs tijjani shattima....... [15/12 09:38] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 65 By Aysha Ya'u Kurah A parlor suka zauna sai da suka gama gaisawa sannan Alhj bara'u yace wasu takardu na gani a dakin marigayi kuma da sunanka a jiki, alhj basheer yace takardu kuma, alhj bara'u ya mika mishi yace kwarai kuwa, alhj basheer ya amsa ya duba su cikin mamaki yace ikon Allah, wadannan takardun sune silar shigan iyalina cikin tashin hankalin nan alhj bara'u, nan ya bashi labarin kyautar da yayi ma Affan, ya daura da cewa ashe jabeer ya bawa ajiyarsu, tabbas nasan safiya tayi neman takardunnan bata gansu ba, kai gaskiya nagode alhj ubangiji Allah ya jikan jabeer ya kai rahama kabarinshi, alhj bara'u yace Ameen, nan suka cigaba da hirarsu hankali kwance,,,,, Fitowa tayi daga inda take makale kullum a cikin gidan bayan ta gama jin hirar alhj basheer da alhj bara'u,, tunda ta gudu daga gurin tsafin su kullum a gidan take yini a makale bacci ne kadai ke mayar da ita wani kurgugun daji inda take hada kulle kullenta, dariya tayi sannan ta shiga parlourn ta dauki takardun tayi kissing dinsu tace me ya rage min tunda na samu wannan, bari kawai in tafi inje in fantama hankali kwance, a hankali ta fito daga parlorn ta make jikin window tana jiran alhj ya shigo ta fita, tana tsaye a gurin ta hango Afeeyah da cikinta dan wata hudu da kwanaki har ya fito sosai kamar dan wata bakwai, Affan na tsaye kusa da ita ya daura hannunshi kan cikin yana mata magana kasa2 suna dariya, wani bakin ciki ne ya turnuke oyizah saboda tuno cewar Afeeyah ce silar fitarta daga gidannan, itace silar rushewar komai na farin cikinta, kwafa tayi cikin bacin rai tace wallhy bazan bar yarinyar nan ta dawwama cikin farin ciki ba, dole in dawo da shirina gobe in tarwatsa rayuwarta kafin in bar kasar nan gaba daya.... Washe gari tun takwas na safe ta gama shirinta na zuwa gidan alhj basheer ta gama da Afeeyah ta huta, takardun da ta ajiye can kasan katifarta ta daga cikin izza zata dauka taga wayam, hankali tashe ta bankade katifar tanata dubawa ko idonta ne amma sam bata gansu ba, cikin tashin hankali ta karaďe arear da take zaune ko zata ganshi nan ma babu labari, a gigice ta sa takalminta ta nufi cikin gari rike da kwalbar acid da ta tsaya ta siya jiya da daddare kafin ta dawo makwancinta, bacewa tayi kamar yadda ta saba ta shiga gidan, dakin alhj basheer ta shiga yana kwance yana bacci hankali kwance gidan sai kamshin girki yakeyi, tana kallon side drawer dinshi ta hango takardun da ta tabbatar ta kwana dasu a dakinta, a rude ta daukesu tace ya akayi suka dawo nan, rungumesu tayi tace koma wani tsinannan ne ya dawo dasu to sun dawo hannuna kuma bazasu kuma fita ba, saurin bacewa tayi saboda jin motsin kofa tayi dakin su Afeeyah, Kwance ta sameta tana bacci cikin bargo shi kuma Affan yana zaune a gefenta yana duba wasu takaddu, murmushi tayi ta makale jikin bango ta buďe kwalbar hannunta ta ďaga zata zirara a kyakykyawar fuskar Afeeyah, juyi Afeeyah tayi hade da mika tana faďin "la'ila ha illallahu muhammad rasoolullah sallalahu alaihi wasallam" Alhamdu lillaahil-lathee 'ahyaanaa ba'da maa 'amaatanaa wa'ilayhin-nushoor.,, nan kwalbar hannun oyizah ta fara girgiďi nan take tayi taka juye a fuska da jikinta, a gigice ta saki takardun hannunta tasa razanannan ihun da saida ya girgiza gidan saboda kararshi, a firgice Affan yaja Afeeyah yana kallon oyizah da ta sauya kamanni, mikewa yayi da sauri yana fadin "Allaahumma 'innaa naj'aluka fee nuhoorihim wa na'oothu bika min shuroorihim." Da gudu su alhj basheer suka shigo dakin suna fadin lafiya, ganin oyizah sukayi a kwance tana birgima ta yage duka kayan jikinta tana ciccisge gashin gabanta dan tsananin azaba, da kafarta alhj basheer ya ganeta yace safiya!!! Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ya waiga ya kalli zeenatu yace kin gani ko na fada miki safiya bazata kyalemu ba, "Tabbas bata kyaleku ba dan tana bibbiyarku kullum a cikin gidannan, tare kuke yini da ita," sukaji wata murya ta ratso kunnensu mutumin ya bayyana a gabansu, gaba dayansu suka ja baya a tsorace, da sauri tsohon yace kar kuji tsorona, ni ba mugu bane, asalima na zama kariya a gareku tun lokacin da take bibiyarku, a jiya ne ta samu damarta da take ganin ta gama samun komai saboda kwashe wadancan takardun da tayi, a daren na maido da takardun shine yau ta dawo ta kwashesu kuma tazo da niyyar kashe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61