Chapter 4
Chapter 4
yayi kan kirjinshi dake bugawa da sauri yace am so sorry Afee nah kece bakya ji in na miki magana, tace wallhy na daina kaje ma ka tambayi hajja Allah ko sun tsokaneni bana tanka musu, jabeer yace to yi shuru na yadda ki daina kuka kinji, ta gyada kanta tace promise me bazaka kara yin bacci baka ganni ba, yace I promise baby in dai da rai da lafiya bazan kara ba kinji, tayi murmushi tace Allah ya kara maka tsawon rai da kuma lafiya in dinga ganinka har karshen rayuwata, ya ja kumatunta yana murmushi yace Ameen my queen, tayi dariyar jindadi suka cigaba da kife kwanukan suna hira har suka gama, a parlor suka zauna yake tambayarta karatun jarabawa, tace tanayi sosai saidai maths ke dan bata wahala, yace baki da matsala zamu dinga yi kullum kafin ku fara exams tashi ki rakani gidansu Affan, ta turo baki tace nidai bazan shiga ba, ya harareta yace yau sai kinzo munje kin gaisheshi rabonki da shiga gidan tun kafin ya fara ciwo saboda haka yau sai kin shiga, ta marairaice tace ni fa ba ruwana in wadannan masu kama da iyamuran sukayi min wllhy ramawa zanyi saidai kace bani da hakuri, ya murďe bakinta har saida tayi kara yace suwaye masu kama da inyamurai, tace oho ni nasan sunansu ne, yayi dariya yace bazaki taba canzawa ba afee sai dai addu'a, tace wallhy zan canza amma fa baza a dakeni a hanani kuka ba, yace to naji tashi muje bazamu daďe ba, tace too ta mike suka fita suka shiga gidan Alhj Basheer,, Cigaban na 4.. Yana zaune as usual a gurin kifaye yayi kasake yana kallonsu kamar me nazarin wani abu, jabeer ya dafashi ya juyo a firgice ganin jabeer yasa shi washe hakori sosai yana kaďa kanshi cikin murna, jabeer yace Affan abokin jabeer kuma abokin kifi, Affan yayi dariya cikin maganar dolaye yace jiya baka zo ba inata kallon can kofar mota har dare baka zo ba, jabeer yace kayi hakuri na danyi wata tafiya ne, Afiya dake tsaye fuskarta dauke da tausayin halin da affan ke ciki tace ina wuni, ya ďago kanshi dake rawa yana washe hakori yana kallonta baya ko kiftawa, duk maganar da jabeer ke mishi bai kalleshi ba idonshi na kan Afeeya kanshi yaki tsayawa guri daya, jabeer ya kalli afeeya da ta rabe tana jin tsoron kallon da Affan ke mata yayi murmushi yace affan baka gane Afeeyah ba, affan ya girgiza kanshi ya runtse idonshi kamar yana son tuno wani abu can ya bude idonshi yace na ganeta amma na manta a wani cartoon na taba ganinta, jabeer ya kwashe da dariya haka shima affan suka dinga dariya tare saida jabeer yayi shuru sannan affan ma yayi, jabeer ya kalli afeeya da ta cika tayi fam ya maza ya mike yace Affan ka jamin bala'i, affan ya mike shima ya matso kusa da afiya sosai kamar zai shige jikinta yasa hannu ya shafi fuskarta wani irin laushi yaji haďe da sanyi mai fisgar zuciya ya maza ya cire hannunshi yana tsalle yace bari inje in fada ma mummy yau na taba fuskar cartoon, jabeer ya janyoshi yace karka kara ce mata cartoon, Affan ya bata fuska yace to mecece in ba cartoon ba kalli fa idonta kato irin nasu, kuma ka taba fuskarta kaji, jabeer yace idonka ne ya ga cartoon wannan Afeeya ta ce, ka tuna ta, Afeeya mai kyuiya mai kukan banza ya faďi yana mata kallon tsokana,,, affan ya kara rufe idonshi ya bude yace mai kuka irin na mage, Afiya tayi tsaki cikin fushi ta fara tafiya, affan yace jabeer kace ma cartoon ta dawo dama bani da barbie din wasa, jabeer yabi bayan afeeya yana cema affan jeka kace ma mummy ta siyo maka wannan barbie din tawa ce, Affan ya bata rai yace sai na fadama daddy in ya dawo ince kaki bani barbie, jabeer bai kulashi ba shidai hakuri kawai yake bawa afeeya, suna kaiwa gate zasu fita shima affan yasa kafa zai bisu yaji wani irin tsawa mai firgitarwa sannan gabanshi yaga kamar namun daji suna so su biyoshi, a sittin ya ruga ciki yana ihu yana kiran sunan mummy, jabeer sam bai lura da yanayinshi ba ya ďauka shirmenshi ne dan baya taba wuce kofar mai gadi yauma yayi mamakin da ya biyosu har gate saboda barbie,, Har cikin gida ya rakata yana rarrashinta da kyar ta sauka da alwashin ta gama shiga gidan Alhj basheer har ta koma ga Allah dama sam jininta bai haďu da flowers din kofar gidan ba ma bare a kai ga mutanen cikinshi gara ma daddy da shi affan din suna gaisawa in jabeer ya kaita gidan, ta saki ajiyar zuciya tace yaya jabeer haka Yaya affan ya dawo rabona da ganinshi tun ina js3, Amma wai wane irin ciwo ne wannan, hajja dake gefensu tace au ke yau kin shiga kin ganshi,, ay a unguwar nan babu wanda ake bari yaje dubashi ko meye dalili oho, jabeer yace hmm babu wani dalili hajja kawai dai matar gidan ce bata yarda a ganshi ni ma dan ta rasa yadda zatayi dani ne shiyasa ta barni,, ga daddy ba mazauni ba dan sai yafi wata bayanan, hajja tace to Allah dai---- sai bakinta ya sar'ke kamar a datseshi da gum... wannan itace babbar jarabawar da Allah ya daurawa AFFAN ta hanyar kishiyar uwa babu wani mahaluki a doron kasa da zai iya yi mishi addu'ar samun sauki, jabeer shi ne kadai yake iya ganinshi har yayi yunkurin sanyashi a hanya amma saboda karfin iko da lokacin da Allah ya ara ma mummy, daga affan ya fara jin maganar jabeer kamar kiftawar walkiya sai ya mance abinda yace ya bijire mishi, duk yadda taso rabasu ta kasa saboda amintar su mai karfi ce wacce zaiyi wuya kasamu labarinta a kasar hausa, Bari in baku takaitaccen tarihin gidaje ukun... Mrs tijjani shattima... [15/12 09:32] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣ By Aysha Ya'u Kurah A unguwar "zoo road" dake cikin garin "kano" ta dabo tumbin giwa nan zan ďan tsakuro muku tarihin gidajen makota ukun, Alhaji Basheer Balarabe dan asalin k'asar Cameroon ne, sana'ar Gwal ita ta shigo dashi kasar nigeria tun yana saro kaďan2 yana siyarwa har Allah ya sanya wa abin albarka ya koma sarinsu da yawa yana shigowa dasu yana siyarwa, a duk cikar kasuwar gwal dake cikin garin kano babu wani wanda yakai Alhj Basheer kawo ingantattun gwalagwalan da babu mixed a cikinsu, wannan dalilin ne yasa duk wanda ya tashi siyan gwal to fa a gurinshi zai siya dan shagunanshi sun fi karfin goma a cikin kasuwar, Alhj Basheer ya auri matarshi ta farko kuma yar uwarshi Zeenatu, auran zumunci akayi musu wanda ganin girma da kuma karamcin rik'on da iyayen zeenatu sukayi mishi yasa ya yarda da auren amma badan yanaso ba, shekararsu uku da aure suna zaman lafiya saboda irin biyayyar da take mishi, a cikin wannan shekarun ne ya dakko ta suka dawo Nigeria da zama kwata2 sai dai suje cameroon hutu, a shekararsu ta biyar da aure ne hankalinsu yayi matukar tashi saboda rashin haihuwa, babu ma kamar alhj basheer da yake ganin madarar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61