Chapter 39
Chapter 39
min baki ya fadi cikin daga murya, ya dago Afeeyah ya kalli wuyan rigarta yace yi shuru ki share hawayenki karki kara cewa zaki je gida sannan yau ďinnan zan siyo miki komai na abinci ki dinga girkawa kina ci a dakinki, salma cikin kuka tace daddy marin da yarinyar nan tamin taci bulus kenan, alhj basheer ya juyo yakai mata wani marin a baki yace in mafaďin magana wawa ne ai majiyinta ba wawa bane, yaya za'ayi Afeeyah ta iya daga hannu ta mare ki, salma cikin kuka sosai tace na rantse da Allah daddy ta mareni, ta kalli Afeeyah suka hada ido ta sakar mata gwaloo hade da murmushi salma ta kara tunzura tayo kanta zata duketa alhj basheer yace wallhy tallahi kika taba yarinyar nan sai na lahira ya fiki jin dadi, oyizah dai tana tsaye kamar gunki mamakin Afeeyah ya hanata cewa komai, haka suwaiba, Affan ne ya fito da gudu jin muryar mahaifinshi, rungumeshi yayi iya karfinshi yace daddy ka dawo, alhj basheer yace na dawo Affan kana nan lafiya ko, Affan ya noke wuyanshi ya haďe rai yace daddy nayi fushi da Afeeyah bazan kara mata magana, alhj basheer yayi murmushi yace me tayi maka, Affan yace batason wasa dani kullum sai su anty salma suyita sata aiki ta goge can, ta goge nan, tayi girki da yawa kuma ita bata ci, kuma sai ta rufe kofa ta hanani shiga inyita bugawa taki buďewa, alhj basheer ya harari salma da oyizah sannan ya kalli Afeeyah yace meyasa bakya bude mishi kofa, oyizah tayi saurin cewa dan Allah alhj kabar maganar nan muje ka huta anjima sai ayita, alhj basheer bai kalleta ba yace Afeeyah dake nake magana, Afeeyah ta dago kanta ta kalli oyizah da zufa ya jikata tace daddy saboda shan maganinshi ne na dare, kafin lokacin yayi nayi bacci bana sanin yana bugawa, oyizah ta saki ajiyar zuciya a hankali.. alhj basheer yace wannan ba hujja bace daga yau ma duk magungunshi ke zaki dinga bashi, Affan ya kalli oyizah yace mummy wai ita zata dinga bani magani? Oyizah ta haďiye miyau tayi murmushi tace eh hakan ma yafi, Affan ya kalli Afeeyah yace zaki dinga bani magani dakyau yadda mummy take bani, Afeeyah tayi murmushi ta saci kallon oyizah tace sosai ma, kasani ma ko in fita iya baka da kyau, yayi tsalle ya rungumeta yace to muje mu dauko magungunnan mukai dakin mu ko, alhj basheer yayi dariya yace banason shirme ka bari mummynka zata kawo maka har ďaki, ya kamo hannun Afeeyah yace zo muje muyi wasa irin na rannan, Afeeyah tayi saurin fisge hannunta ta wuce daki cikin jin kunya, ya bita a baya da gudu, alhj basheer ma daki ya wuce ba tare da ya kalli oyizah ba,, suwaiba tace kinga abinda nake faďa miki game da yarinyar nan ko, oyizah tace uhummm kawai ta wuce daki salma ta bita har lokacin kuka takeyi,,, suwaibah taja gyalenta itama tayi waje... Karfe huďu na yamma alhj basheer ya dawo gida motarshi cike da kayan abinci, masu aikin gidan maza su suka shiga da kayan lokacin Oyizah na zaune a parlor tana ta tufka da warwara, ko kallonsu batayi ba har suka gama shigewa da kayan suka fita, shigowar alhj basheer ne yasata mikewa da sauri tana mishi sannu da zuwa, bai amsa mata ba yace kin kai wa Afeeyah magungunan, oyizah tace yanzu zan kai mata alhj, dan Allah ka fahimceni wallhy--yayi saurin dakatar da ita da hannu yace babu abinda zaki fada min in yarda, tsakani da Allah safiya a bani amanar yarinya ku hadu ke da yayanki ku dinga kuntata mata, oyizah ta fashe da kuka tace wallhy alhj sharri tayi mana, kaima kasan abinda zanyi da wanda bazanyi ba, yace in ke baki mata ay yayanki na mata kuma bakya tsawatar musu, Oyiza ta kara tsananta kukanta tace dan Allah kayi hakuri wallhy zan dauki kwakwaran mataki akan su, dakyar alhj basheer ya hakura kuma yasa ta kira su salma yayi musu concrt warning akan Afeeyah... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣5⃣ By Aysha Ya'u Kurah Cikin fushi tace dalla ni sakeni in gaida ubangijin da ya halicceni kuma ya raine ni da ni'imominsa, Affan ya kwantar da kanshi a kafadarta yace ni kike ma ihu ko? Tayi tsaki tace ay kai duka ne ma ya kamace ka ba ihu ba, ya dawo gabanta yayi narai2 da ido yace zaki iya duka na, tace sosai ma in dai bazaka dinga yin sallah ba, ta tallabi fuskarshi da hannunta ta rage murya tace kasan falalar dake cikin yin sallah?, Affan ya girgiza kanshi, tace ko na fada maka bazaka gane ba, ka faďa min duk abinda kakeso wanda yake ranka yanzu, ya rufe idonshi cikin murna yace ammmm inason ganin abokina, ya bata rai kamar zaiyi kuka yace abokina ya gudu ya barni ya daina zuwa guri na nayi fushi dashi,, idon Afeeyah ya ciko da kwallah tace kar ka damu zaizo ya ganka, amma fa sai ka yarda kayi sallah, yace in nayi zaizo tace sosai ma, Affan yace to sai kuma ina son kullum ki dinga tayani wasa, mu buga game tare, mu buga kwallo tare, Afeeyah tayi saurin cewa har abinci ma tare zamu dinga ci mu dinga bacci tare amma fa sai ka yarda kayi sallah, ya daka tsalle yace yeeee zanyi, Afeeyah tace sai me kuma, ya bata rai yace sai kuma su anty salma, banason suna min ihu suna zagina wata rana harda duka na akai, in nayi sallah zasu daina, tace sosai ma, ai in ka yarda kayi sallah ko sun maka ihu zan rama maka, yayi dariya yace yauwa barbie na to muje muyi sallah, ta dauko dadduma ta shimfiďa mishi duk da tasan ba daidai zaiyi sallar ba amma gara yayi wit tym zai fara yinta daidai, Guri ďaya suka tsaya ya maida hankali yana yin duk abinda tayi yana waige, isha'i sukayi da shafa'i kadai banda wutiri, saida ta gama lazimi sannan tace mishi ya ďaga hannunshi sama kamar yadda tayi, yayi yadda tace, tace yauwa to duk abinda nace kace "Ameen" ya sauke hannunshi yace nace "Ameen" tace a'a kar ka sauke hannun ka ďaga hannun, yace "Ameen" tayi dariya ta kama hannunshi tace haka zaka barshi, ya kuma cewa ameen, cikin dariya ta fara karanto adduo'i yana cewa Ameen, inuwar mutane ta gani a kansu ta ďago da sauri ta kallesu, bata tsayar da addua'r ba saima sake mata salo da tayi ta hanyar faďin "Auzubillahi minash shaidann rajim" Affan yace ameen da karfi yana kallon oyizah dake huci fuskar nan babu annuri, salma ta daka mishi tsawa tace tashi ka fita a dakin nan, jikin Affan ya fara rawa yana kokarin mikewa Afeeyah ta matse hannunshi ta shafa addua'r da ta idar tace ina zaka je, Fareeda tace gidan uwarki zaije, tashi ka fita ko in tattaka ka, Afeeyah tace ikon Allah, to dai nasan Affan baida wani dakin da ya wuce na matarshi, saboda haka babu inda zashi, oyizah cikin fushi tace kika ce me? Afeeya ta kalli salma tace maimata mata inaga kamar tana da matsalar ji, salma cikin fushi ta kai mata naushi da sauri
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61