Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

oyiza ta ďago kanta zuciyarta a dake tace I found him my lord, amma mum naso ta kawo min matsala, chummy tayi dariya mai karfi tace ur mum ko kuma gvn mum, kin manta u sacrifice her sannan kika samu alhj basheer yasan inda kike, cikin faduwar gaba oyiza tayi kasa da kanta tace I love my mum my lord, chummy tace I knws dat amma in har kinason jin dadi dole ki katse numfashin mahaifiyarki, kuma bari in fada miki kina shiga gidanshi zaki samu ciki so u will be d apple of d house saboda u bring air to d family, , mum dinki ta fara tsufa so let her go ke kuma ki fara rayuwarki mai daďi, haka tayita convincn dinta har ta gamsu ta fitar da uwarta a ranta tayi alkawarin yau da dare zata bada uwarta saboda komai ya tafi mata daidai, sun kusa awa suna tattaunawa kafin Chummy ta bace, oyiza ta mayar da komai na tsafinta ta fito ta shiga kitchen dan tayi ma innocent mum dinta girki, tsayawa tayi a kitchen ta kasa komai tana tunano rayuwar da tayi da mahaifiyarta da irin wahalar da mahaifiyarta tasha akanta da karatunta, tayi tsaki a zuciyarta tace kuďi yafi min komai ciki harda ke mum, am so srry mum u have to go, ina son sunana ya shiga jerin mata masu arzikin duniya, girki ta farayi duk da jikinta a mace yake amma ta dake saboda zuciyarta ta daďe da kangarewa da shan jinin bil adama, Oyiza ta shiga cikin kungiyar asiri ne tun shekararta ta farko a jamiar lagos, wata kawarta esther Babajo ita tasata lokacin tana shan wahalar rashin kuďi da abinci saboda mahaifiyarta bata da kuđi, sannan kuma sun shiga ne dan su dinga samun first class result a set dinsu, haka kuwa yake faruwa dasu dan su biyun nan saida ya zamana babu wanda yake iya bugesu, kuma kuďi ma babu macen da zata nuna musu shanawa a cikin skull, duk irin gulmarsu da akeyi babu wanda ko wacce ta isa tazo gabansu tayi saboda tsabar tsoronsu da ake ji, jini kuwa su kansu basu san adadin na mutanen da suka sha ba, oyiza ta hadu da alhj basheer ne a airport lokacin sun dawo daga Italy ita da esther, tunda ta daura idonta akanshi da suka sakko daga jirgi taji sonshi mai tsanani ya kamata, tun a airport suke bin bayan motar da ta daukeshi har zuwa hotel din da zai kwana kafin safiya ya wuce kano, Saida suka bari ya shiga ciki sannan suka samu drivern da ya daukoshi suka tambayeshi sunanshi, da kyar da kuma kuďi da suka bashi ya sanar dasu sunanshi da kuma garin da yake, godiya sukayi mishi sannan suka wuce, tun daga ranar Chummy ta fara mata aiki akanshi, nan ta gano irin kudin da yake dashi da kuma wanda zaiyi nan gaba, ta kuma gano matsalar da yake ciki na rashin haihuwa , jin yunwarshi da tsayuwa a restaurant dinsu 4d first tym duk aikinsu ne.. dariya oyiza tayi bayan ta gama tunano wadannan abubuwan sannan ta sauke abincin da ta daura ta kwashe ta haďa juice ta jere su akan dining ta zauna zaman jiran mamanta dan suyi hirar karshe.... Allahu akbar,,, tabbas mun tsinci kanmu a zamanin da kuďi suka fi wadanda suka kawo mu duniya daraja, kuďi sunfi ďan da ka tsuguna ka haifa saboda a cikin 100% 85% zasu iya bada komai nasu dan su samu kuďi dattin duniya,,, tabbas a wannan zamanin da muke ciki masu karancin imani da tawakkali zasu iya aikata komai saboda kudi, Ya Allah ka tsarkake mana zuciyarmu da ta yan uwa musulmi baki ďaya, Allah ka azurta mu da baye bayenka kayi mana rowar talaucin da zai kaimu ya baro mu,, ameen thumma ameen.... Mrs tijjani shattima..... [15/12 09:32] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 7⃣ By Aysha Ya'u Kurah Daren ranar bayan sun gama hirah da mamanta ta nuna mata ta hakura da maganar alhj basheer, mum ta yi murna sosai dajin hakan daga bakin oyiza, sai gurin sha ďaya taga mum na hamma ta dafata tace mum bacci kike ji, mum tace eh bacci sosai nakeji bari inje in kwanta, oyiza ta mike tace bari in kara gyara miki ďaki saboda kiji dadin bacci da kyau, mum tayi murmushin jin dadin ganin yadda yarta ke tarairayarta, dakinta oyiza ta wuce ta yaye shimfiďar zanin gadon tasanya mata wani fari kall a kasa sannan ta ďaura nata akai, idonta yayi ja lokacin da ta dauko wata kwalbar farin magani zata yayyafa a gadon, sai da ta ďan zubar da hawaye sannan ta yayyafa maganin ta fita taje ta taso mum da ta fara bacci, har ďaki ta rakata ta rufo kofar ta koma ďakinta tayi tagumi tana jiran dare ya raba ta tafi gurin meeting, ,, 2:45am Tsugune suke gaban "CHUMMY LORD" cikin jajayen kaya su kusan goma sha biyar maza da mata masu neman arziki da mulki, jini ne a kwarya wani bakin mutum ya ďauko ya mika ma wacce take gaba ta sha ta mika ma sauran duk suka sha sannan suka ajiye kwaryar, wani irin kirari haďe da ihu "chummy" tayi akan wani farin kyalle sai ga wasu yara yanmata basu wuce shekara 14 ba sun bayyana a gabanta cikin night gown, yara ne farare kyawawa masu kama da juna da ganinsu yan biyu ne, a firgice yaran suka fara waige2 suna kankame junansu, chummy tayi dariya sosai tace Alhaji Sambo aikinka yayi kyau lallai ka tabbatar kana son cin wannan kujerar, da sauri yaran suka fara kallon mutanen gurin ko zasu ga wanda aka kira da sunan mahaifinsu, jikinsu ya kara rawa lokacin da idonsu ya sauka akan babansu mai kaunarsu dare da rana wanda a wannan daren kafin su kwanta bacci saida yayi yawo dasu cikin garin abuja da kewayenta ya kashe musu makudan kudi na ban mamaki, cikin rawar murya suka ce PA--PA, alhj sambo ya sunkuyar da kanshi kasa, daya daga cikinsu tayi karfin halin zuwa gabanshi ta dafashi dan gani takeyi kamar mafarki takeyi, jin da gaske shi ďinne yasa ta rusa ihu ta kalli yar uwarta tace "Fanne" ba mafarki nakeyi ba wallhy papa ne, meyasa zaka mana haka, yanzu ashe neman duniya zai iya saka ka bayar da ya'yanka na cikinka, papa sanda zaka bada damu bakayi tunanin bazaka kara ganin mu ba, cikin fushi dayar tace "Fanna" meye a ciki dan ya bada mu an kashe, kika san iya adadin mutanen da ya kashe saboda neman duniyarshi, kukan me kikeyi? Saboda bazaki kara shakar iskar duniya ba kome? Inda zamu tafi nan zai zo yau ko gobe ko jibi in kwananshi ya kare shima, gara ma su kashemu da zama karkashin zalunci da cin kudin haram da na kawunan mutane, wani mugun mari aka dauketa dashi ta waiga ta kalli bakin mutumin zuciyarta ta kara zafi tace ba mari nake bukata ba kashemu zakayi mu huta, "chummy" tayi dariyar kusan minti uku sannan tace ai dama kun mutu ruhinku ne anan, in naso zan iya barin ruhinku yayita yawo shi kadai a duniya gangar jikinku kuma tana rami, Fanna tace ki so din, fanne tayi saurin cewa dan

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});