Chapter 57
Chapter 57
murmushi a kullum ba,, nasan bazamu sake haďuwa mu rungume juna mu faďa ma juna damuwarmu ba, bansan me yasa mutuwa ta zabi jabeer ta barni, bansani ba Afeeyah, ya karasa fadi yana kuka kamar karamin yaro,, kuka suka dinga yi babu mai rarrashin wani a cikinsu, saida sukayi mai isarsu sannan Affan ya ďago ya kalleta murya a dashe yace nagode, nagode da abin da kikayi min, kau da kanta tayi tace ka gode ma Allah da kaka liman, ya juyo da fuskarta yana kallon rinannun idanuwanta yace kullum cikin gode musu nake, godiyarki ta daban ce Afeeyah, babu wanda zai dauki kasadar da kika ďauka a duniyar mu ta yanzu, kinyi mana abin da ko dan uwa na jini bazai iya yi mana shi ba, bamu da wata kalmar da zamuyi amfani da ita gurin gode miki, Afeeyah tace karka gode min na cika kudirin jabeer ne, wannan shine burinshi na karshe, saboda wannan kudirin aka kashe min shi,,, Affan yace nasan komai Afeeyah kuma in shaa Allahu wacce ta kasheshi ba anan duniya ba ma har a lahirah bazata taba samun kwanciyar hankali ba, Afeeyah tace tun a duniya nakeson Allah ya wulakanta min ita, wallhi da nasan ita ce silar mutuwarshi na rantse da bazan kyaleta ba da nayi mata abun da zata gwammaci mutuwa da rayuwa, Affan ya share mata hawaye yace ki kwantar da hankalinki nasan yanzu duk inda take a cikin bala'i take, Afeeyah ta girgiza kanta tace da hannuna nakeson in kasheta kuma yau dinnan, Affan yace hmm nima naso hakan tun ranar da na dawo cikin hayyacina, nan ya bata labarin komai harda dawowar umma da bacewar oyizah,,,,, cikin mamaki Afeeyah tace zatayi abinda yafi haka muguwa azzaluma, Allah ya isa tsakanina da ita, in shaa Allahu sai tayi mutuwar kask---Affan ya katseta da sauri yace wannan adduar bata kamace ki ba, Allah yasan yadda zai tafiyar da irinsu ki zuba ido ki jira lokaci, Afeeyah tayi shuru tana kallonshi kamar ba shi bane tababben bawan da baya taba maganar da zaka iya fahimta a da, Allah mai iko...... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:38] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣4⃣ By Aysha Ya'u Kurah Daren ranar suna zaune gurin meeting bayan sun dawo daga gurin dodon tsafinsu, gaba dayansu suna sanye da jajayen kayansu da suke amfani dashi, bayan sun gama tsaface tsafacensu sai chummy ta mike taje ta shigo da ďan tsoho, a tsakiya suka sashi kamar yadda suka saba, kewayeshi ta farayi tana yan sirkullenta a kanshi sannan ta zauna, ďaya bayan ďaya tsohon yake bin mutanen gurin da kallo, yana zuwa kan oyizah ya tsayar da idonshi kyarr a kanta baya ko kiftawa, kureshi itama tayi da ido cikin rashin tsoro ta daka mishi tsawa tace daina kallona, idon wannan tsohon ko rawa baya yi ya fara motsa bakinshi da babu hakori ko ďaya a ciki, oyizah ta kalli chummy tace my lord plss mu gama da tsohon nan mu cigaba da abinda ke gaban mu, chummy bata kalli oyizah ba ta cigaba da haďe haďenta na tsafi cikin wani katon koko, mikewa tayi ta iso gaban tsohon ta ja hannunshi da karfi har yana bigewa ta jona mishi wani abu mai tsini kamar kibiya a jijiyar hannunshi tana kallon cikin kokon, a firgice ta juyo tana kallonshi ta kuma maida idonta cikin kokon dan gasgata abin da ta gani a ciki, da sauri ta saki karfen taja baya saboda yadda ya dauki zafi kamar tana rike da garwashi, wata irin dariya tsohon nan ya saki yace jinin nawa ya isheki haka, in kina bukatar kari kizo ki diba san ranki dan ko zaki dibi cikin tanki bazai kare ba, su oyizah duk suka marmatso suka leka cikin kokon, a gigice suka ja baya saboda ganin wani bakin ruwa mai kaurin gaske a ciki, oyizah murya na rawa tace my lord kiyi wani abu plss wannan kamar ba mutum bane, cikin su esther da alhj sambo ya ďuri ruwa suka ce kwarai wannan ba mutum bane, cikin dakewa chummy tace ko ma waye shi tunda yazo nan bazai taba fita ba, ta dauko wata sanda mai mugun kyalli ta nufi wannan tsohon dashi, tana karasowa gaban shi ta ďaga wannan sandar ta saita cikin idonshi ta turata ciki, ga mamakinta sai ganin sandar tayi ta rabe gida biyu, daya a cikin idonshi ďaya a hannunta, sa hannunshi yayi ya zaro sandar yana dariya ya mika mata yace haďata guri ďaya, a harzuke ta yar da sandar hannunta ta koma ta shirya kanta sosai tace yau ko waye tsohon nan sai na gama dashi, ta bayanshi ta bullo ta sa farcen hannunta ta shako wuyanshi ta baya, da azama ya juyo ya sanya nashi faratan a makogoranta, wani irin kakari ta farayi tasa kafarta ta haureshi yayi baya, nan suka fara b'ace b'ace suna faďa sosai, ba karamin wahala chummy take sha ba amma saboda tsabar ta dahu da tsafi kuma bata so mabiyanta suga gazawarta haka ta jajirce suka cigaba, wani lungu ta shiga a cikin ďakin ta fito rike da wani magani ta bace tana kokarin watsa ma wannan tsohon, sam bata san yana kallonta ba ta ďaga wannan maganin zata zirara mishi yayi saurin juyar da hannunta ya zuba wannan ruwan a tsakiyar kanta, wani irin ihu ta saki ta faďi kasa tana ta shure shure nan take kanta ya fara zagwanyewa, tun tana ihu mai karfi har ta koma yi a hankali gaba ďaya mummunar halittarta ta canza kama,, a gigice su oyizah suka fara ja baya hankalinsu a tashe babu wanda a cikinsu yayi kokarin zuwa gurin wacce suke kira mai taimakonsu, itama yau gashi ta kasa taimakon kanta, mikewa wannan tsohon yayi yana kallon su oyizah, mai da hankalinshi yayi gurin alhj sambo yace alhj sambo Bana, minister mai fuska biyu, a fili fuskar kamala a zuci ta zalunci, ina son kayi ma kanka hisabi ka zabi hukunci cikin jerin abinda zan lissafo, na farko ko in kasheka anan in kaika gida da kayan jikinka, ko kuma in barka ka koma gida ka fito media ka faďi ko me kakeyi sannan ka fadi adadin mutanen da ka bayar akasha jininsu, alhj sambo cikin rudewa yace kayi min rai dan Allah, dan tsoho yace Allah shi ke da rai bani ba, alhj sambo yace ka rufamin asiri wallhy na tuba, har abada bazan kara aikata irin wannan aikin ba, dan tsoho yayi dariya yace zunubin da kayi baya kuma fa, kayi kisan kai, shirka, da sauransu duk dan ka samu mulki, haka nake so kaje gidan talabijin ka sanar musu da halinka, alhj sambo ya girgiza kanshi yace mutunci na zai zube, dan tsoho yace ai gara ya zube a duniya, alhj sambo yace dan Allah ka kasheni anan kawai gara suga gawata, dan tsoho ya girgiza kanshi yace a'a bazan yi kisa ba gara a hukunta ka kafin kaje ka tarar da na ubangiji, kuka sosai alhj sambo yakeyi yana mishi magiya akan ya kasheshi ya huta amma tsoho yayi kememe yaki, alhj sambo da yaga babu sarki sai Allah sai ya amince da abinda tsoho yace mishi ya kimtsa ya bace yayi gida hankalinshi a tashe, kallon sauran yan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61