Chapter 18
Chapter 18
alhj, Affan ya samu "brain disorder" abin da yabamu mamakin anan shine duk girman ciwo da karfin buguwar nan bashi ya taba kwakwalwar shi ba har yasamu "mental illness" sai wani abun daban,,,, ya mika mishi wata takarda yace wadannan sune ciwukan da kwakwalwar shi ta samu "Psychological trauma": wannan cutar may be triggered by P.T suffered as a child, kamar "severe emotional", physical, or sexual abuse;" abinda ke kawoshi kuma shine, "a significant early loss", kamar the loss of a parent; and neglect... sai kuma "Environmental stressors": "itama ana samunta ne a shock din mutuwa ko macen da aka saka, ko kuma dysfunctional family life, sacking 4rm jobs or schools, and substance abuse -- it can trigger a disorder in a person who may be at risk for developing a mental illness." Kaga kenan akwai abinda ya gani ko kuma ya sameshi cikin waďannan abubuwan amma sam ciwon kanshi bai da alaka da cutar, Alhj basheer cikin tashin hankali yace yanzu doctor kana ganin Affan zai samu lafiya nan kusa,? doctr musah cikin tausayawa yace sauki na gurin Allah alhj, in yazo yanzu baiyi gaggawa ba sannan in baizo yanzu ba baiyi jinkiri ba saboda Allah ne kadai yake iya bada sauki a lokacin da yaso, sannan ina tsoron sanar dakai mostly mental illnesses irin wannan are caused by a combination of factors and cannot be prevented so easily, saidai a dage da addu'a saboda babu abin da ya gagari Allah kuma babu wanda yasan gaibu sai Shi.., da sauri oyizah da tun shigewar su office din doctor ta iso ta juya cikin jin dadin ciwon da taji ya sami Affan da kuma firgicin jin affan nada rai kuma zai iya samun sauki a koda yaushe, kuma tasan yanzu alhj na dawowa zai fara tambayarta ina zeenatu? Kuma me ya samu Affan me ya gani har ya haddasa mishi wannan cutar, fita tayi daga asibitin da sauri cikin tsananin tsoron abinda zai je yazo, bata zame ko ina ba sai gurin tsafinsu..... Mrs tijjani shattima..... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣2⃣ By Aysha Ya'u kurah Alhj basheer ya fito daga office din doctor Musah idonshi jajur saboda kukan da yaci, dakin da aka kwantar da Affan ya shiga ya zauna gefenshi yana zubar da hawaye yana ta tunanin yadda akayi har Affan ya faďo daga wannan saman nisan gaske, to wai ma me Affan ya gani da har ya firgita shi haka, da sauri ya mike da ya tuno da tun asuba baisa zeenatu a idonshi ba, kuma ace har Affan baida lafiya batazo inda yake ba, girgiza kanshi yayi a fili ko dai wani abu ne ya samu zeenatu, gabanshi ya faďi sosai da ya tuno da kalaman doctor, jikinshi ya fara rawa ya murda kofar dakin da affan yake ya fita da sauri yana fadin innalillahi a zuciyarshi, da taimakon Allah ya isa gida, a waje yayi parking motar saboda tashin hankali, yana shiga ya wuce dakinta, babu inda bai duba ba a ďakin bai ganta ba, cikin kiďima ya fito yana haďa sunayen mutanen gidan yana kirah da karfi, da gudu suka firfito, oyizah da bata fi minti 5 da dawowa daga gurin tsafinsu ba ta matso kusa dashi tace lafiya alhj, ya nuna dakin zeenatu yace ina zeenatu take, fareeda da salma suka ce daddy tun jiya bamu ganta ba, oyizah tace ni rabona da zeenatu ma ay tun ranar da zaka tafi mukayi maka rakiya, cikin karaji yace to ina ta shiga, oyizah ta dafashi tace calm down my dear muje ka huta ka kira can gida kaji ko tana can, cikin damuwa ya kalli fuskar oyizah, nan ya tsinci kanshi da kasa yi mata musu ya bi bayanta suka wuce gurin dinning, saida ta bashi abincin da ta haďasu da sinadaran asiri sannan ta zauna gefenshi tana matsa mishi kafa, kallonta yayi har lokacin fuskarshi dauke da damuwa yace safiya ya akayi Affan ya faďo daga wannan saman mai nisa, sannan me ya faru a gidannan da har ya haddasa tabuwar kwakwalwarshi, oyizah ta fara share hawayen karya tace alhj nima ban sani ba, kowa na bangarenshi ya za'ayi insan abinda ya faru, Allah sarki Affan yanzu brain dinshi ya samu matsala, murya a dashe alhj basheer yace eh safiya, kuma bawai fadowar da yayi bane ya taba brain dinshi, hankali tashe kamar gaske tace to me ya sameshi, nan ya kwashe abinda doctor ya faďa mishi ya fada mata, wani irin kuka ta fashe dashi harda zama a dirshan a kasa tana faďin mun shiga uku, yanzu shikenan Affan ya haukace, alhj basheer ya shiga rarrashinta yana faďin addu'a zamuyi mishi safiya, dakyar oyizah tayi shuru tace ni alhj babban tashin hankalina shine rashin ganin zeenatu, Allah yasa ba wasu mugayen bane suka saceta suka wurgo Affan daga sama, hankalin alhj basheer ya tashi da jin furucin oyiza, ya kalleta yace da zeenatu tayi musu me zasu saceta, oyizah tace Alhj ka manta muna cikin zamanin da ba sai kayi ma wani komai ba zai maka mugun illah, nidai gobe kabi jirgin safe kabar kulawar Affan a gurina kaje can cameroon ka dubata dan wannan abun yafi karfin waya, alhj basheer ya share zufar goshinshi yace kin kawo shawara mai kyau safiya, amma--- ta katseshi da sauri tace na fada maka zan kula da Affan fiye da yadda zaka kula dashi, kai dai ka tafi nemanta dan hakkinta na wuyanka, cikin jindadin tsararrun kalaman oyizah alhj basheer yace nagode sosai safiya, Allah ya kaimu goben, tace ameen yanzu kaje ka kwanta ni zan tafi gurin Affan din in ta kama ma sai in kwana, alhj basheer yaji dadi sosai a ranshi ya dinga shi mata albarka.. Ďaki oyiza ta wuce zuciyarta wasai yanzu gida zai dawo karkashin ikonta, wani kulli mai kyalli ta kwance ta fito da babyn "Mutum mutumi" an soke kanshi da mashi, Kallon babyn tayi hade da kwashewa da dariya tace Affan kai da warkewa har abada, haka zaka dawwama cikin hauka har ka mutu kamar yadda babyn nan take haka zaka kasance sai yadda nayi dakai, ta mike ta daga karkashin gadonta inda ta dade da haka wani ramin sihiri ta kara tona gefen ramin ta kira sunan Affan sau uku sannan ta tura babyn ciki tana dariyar mugunta, ta kalli wata laya ta kara saka wata dariyar tace wannan naki ne zeenatu, ba yanzu zanyi aikin ba sai an gaji da nemanki, ta mayar da layar cikin daurinta sannan ta loda magunguna hade da turarukan tsafi a jakarta ta shirya wucewa asibitin.. Tun asuba jabeer ke neman wayar Affan ba'a dauka ba, daga karshe ma jin wayar yayi akashe, gurin karfe 8 yaso shiga ya dubashi sai wani muhimmin aiki ya taso mishi a office ya wuce, bai dawo gida ba sai bayan magriba, saida ya fara shiga gurin Afeeyah suka dan taba hirah sama2 sukaci abinci tare kamar yadda suka saba sannan ya mike jikinshi a sanyaye saboda rashin jin muryar amininshi yau tru out, abinda bai taba faruwa ba tun tasowarsu dan ko tafiya daya yayi to suna manne a waya, sallama yayi ma hajja da afeeyah ya fita ya isa kofar gidan su Affan, tun a gate mai gadi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61