Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 51

Chapter 51

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

babba ce, muyi kwanciyarmu a kasa ko, ya gyada mata kai yana murmushi ya kwanta a kasa yana kallo sama, bayi ta shiga tayi alwala ta kare ma bayin kallo tana gyada kai cikin mamaki dan cike yake da magunguna da sabulan bleaching, fitowa tayi ta dauki hijab dinta ta kwanto dankwalin kanta ta shimfiďa dan bata ga dadduma a dakin ba, sallah ta hau yi in ta idar ta kara tayar da wata kabbarar, tun Affan na kirga sallahr da takeyi har bacci daukeshi bata idar ba, ☆ 2:30am ☆ Lokacin ta idar da sallolin da takeyi ta fara adduo'i tana neman taimakon Allah akan abin da zata aiwatar yanzu, saida tayi addu'a sosai sannan ta mike ta cire hijab dinta ta rufe Affan dashi ta tofe shi da addu'a, Saida ta tabbatar ta rufe windows din dakin sosai ta yadda ko kuda bazai iya bi ba bare ido yaga me akeyi a ciki, da bismillah ta yaye zanin gadon sannan ta daga katifar, dakyar ta iya cire katakon dake kasan gadon saboda nauyinsu, a razane ta ja baya saboda hango wani makeken rami a karkashin gadon, hasbunallahu wa ni'imal wakil kawai take fada saboda ta matukar tsorata da ramin, zuciyarta sai bugawa takeyi saboda tuna ita fa xata sa hannunta cikin ramin, girgiza kanta tayi ta fara ja baya tana fadin wallhy bazan iya ba, ji tayi kamar ta daki mutum a bayanta ta juyo a razane taga babu kowa sai muryar kaka liman dake mata yawo cikin kunnuwanta, "na rokeki karki tsorata ke kadai ce garkuwar bayin Allahn nan, in kika tsorata babu wanda zai iya, "in kika gansu Ruwanki ne ki barsu ko ki ciresu ki taimaki mahaifi da kakar abinda ke cikinki"" A hankali ta karaso gurin ramin idonta cike da kwalla tasa hannu ta fara ciro kulle kullen dake ciki, gumakan dake cikin ramin uku ne, daya an soke kanshi da mashi, biyu kuma an haďe su guri daya an kulle, saida ta tabbatar ta fitar da komai daga cikin ramin sannan ta maida kayan gadon tana yi tana share zufa, gaba daya a lokacin ta nemi tsoro ta rasa, kwashesu tayi cikin hijab din da ta rufama Affan ta buďe kofar dakin tayi saurin wucewa dakinta, kitchen ta wuce cikin dakewar zuciya ta fara warware duk wani kullin garin magani tana zubarwa a cikin zinc tana kwarara mishi ruwa, haka layunma duk tayi musu, gunkin lakan da aka hade su guri daya ta fara warwarewa ta sa tabarya ta dakeshi ya zama gari sannan ta kwararar dashi cikin zinc, dauko dayan gunkin tayi wanda akayi shi da roba, da bismillah ta zare mashin ciki, tana dauko wuka zata fara yankashi taji wata guguwa mai karfi ta bude windown kitchen din, hannaye taga an ziro ta cikin windown tayi saurin yar da wukar hannunta ta cilla wannan mashin bayan cabinet, a hankali taga gangar jikin mutum na shigowa, da gudu tayi hanyar waje tana addu'a, tana zuwa kofar taji an datseta da karfi, ja da baya ta fara yi tana salati tana kiran sunan hajja, oyizah ta gani muraran ta bullo ta cikin kofar, zaro ido tayi murya na rawa tace m-u-mm-y, oyizah ta buga mata wata sanda a bakinta, rike bakin tayi tana ta nemo addu'a a bakinta ta rasa, cikin kunan rai oyizah ta fara matsowa fuskar nan babu rahama tace yau sai na kasheki, daga yau kin daina numfashi a doron kasa bare har kiyi yunkurin shiga rayuwata, da hannuna zan kasheki tunda duk wani abu da nayi akanki bana samun nasara, ban taba haduwa da abin da ya dameni ba sai a kanki dake da matsyacin saurayinki jabeer, kamar yadda na kawar da jabeer da mahaifiyar Affan kema haka zan kawar dake kije can ki samesu dan babu wanda ya isa ya shiga gonata ya fita ba tare da yayi noma ba, tayi wani huci hade da daga wannan sandar zata buga ma Afeeyah, da sauri ta goce ta rike sandar sosai, nan suka fara dambe sosai har oyizah tayi nasarar kwace sandar, da karfi ta shiga laftar Afeeyah da ita, ihu Afeeyah takeyi tana ja da baya saboda azaba, wani jug ta rarumo a gefenta ta kwaďa ma oyizah akanta, nan jini ya fara zuba sosai, da sauri Afeeyah ta bangajeta ta kama kofar kitchen din tana jijjigawa tana ihu sosai kamar zata tsaga gidan, ganin kofar taki buduwa yasata daukar wuka ta nuna ma oyizah dake tahowa kusa da ita tace wallhy kina matsowa zan kashe ki, oyizah ta goge jinin gefen idonta tayi wata irin dariya tace wai gawa ce ke maganar kashe me rai, cikin kuka Afeeyah ta juya tana faďin ya Allah ka taimakeni, tana jan kofar taji ta buďu tayi saurin fita ta datso oyizah a ciki, da mamakinta tana bude kofar parlonta ta tarar da oyizah da wata mata mai gebararran halitta, runtse idonta tayi ta fara fadin hasbunallahu wa ni'imal wakil, la ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalumin, wukar nan dake hannunta ta ďaga da niyyar buga ma oyizah, nan tayi saurin dukawa ta kamo kafar Afeeyah ta daga ta sama tayi wurgi da ita ta bugu da bango da tiles din dakin, kara mai karfi ta saki wacce ba alhj basheer kaďai ba har masu gadin gidan saida suka girgiza da jinta, tun daga wannan karar Afeeyah bata kara sanin inda kanta yake ba, jin Alhj basheer ya bude kofar dakinshi yasa chummy ta bace,, da sauri oyizah ta yar da sandar hannunta ta tsuguna tana ihu a gaban Afeeyah, da gudu Alhj basheer da farida suka karaso gurin, cikin rudewa alhj basheer ya shiga jijjiga ta yana kiran sunanta, kallon oyizah yayi tana kuka sosai yace safiya me ya sameta, cikin makirci oyizah tace nima fitowa nayi na tarar da ita anan tana dambe da iska, ina matsowa kusa da ita sai naji saukar wannan wukar a goshina, anya alhj yarinyar nan ba matsafiya bace kuwa,? alhj basheer ya daka mata tsawa yace kamata mu kaita asibiti muji abin da ke damunta, oyizah ta share hawayen karya ta kamata a zuciyarta tana murna dan suna zuwa asibiti zata karasa ta acan, Alhj basheer na tada mota yaji kamar muryar Affan a gefen glass din motar, kallonshi yayi yace Affan ka tashi ne, Affan ya gyaďa kanshi idonshi jajur yace daddy ina zaku kaita, alhj basheer yace asibiti zamu kaita yanzu zamu dawo je ka kwanta kaji, bude motar yayi ya zauna a inda aka kwantar da ita yace muje daddy, alhj basheer yace kayi hakuri Affan ka je ka kwanta kafin mu dawo, Affan kamar zaiyi kuka yace daddy bazan iya bacci ba, oyizah cikin fushi tace ka sauka akace ko bakaji abin da aka ce maka bane, kallonta yayi cikin ido hawaye na sauka cikin nashi yace saidai idan tare da Afeeyah zaku saukemu, oyizah zata kuma magana alhj basheer ya tada motar yace muje kyaleshi, oyizah tayi kwafa dan wannan mayen ya rusa mata plan dinta, har suka kai asibitin idon Affan bai bar zubar da hawaye ba, janyoshi daddy yayi yana rarrashinshi akan ya daina kuka babu abinda zai sameta, sun dan dade a tsaye kafin doctor yazo, direct ya wuce dakin da aka

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});