Chapter 17
Chapter 17
ta baya, tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba hawayen da ya gama taruwa a idonta ya fara zubowa, a hankali ya juyota ya ciro wayarshi yana haska fuskarta, murmushi yayi da yaga hawaye akan kumatunta yasa hannu ya fara share mata a hankali yace shikenan ke kuka bashi da wuya a gurinki, da abun kuka da wanda ba na kuka ba duk sai kin musu kuka, yanzu faďa min abinda aka miki, ta kara fashewa da kukan da daga ji na shagwaba ne tace ba kai bane--- sai kuma tayi shuru, yayi dariya yace ba ni bane mee? Ta kauda kanta tace ban sani ba, ya juyo da kanta yana kallon cikin idonta yace fadamin laifin da nayi in hukunta kaina yanzun nan, ta turo baki tace tun ďazu nake jiranka anan kuma kasan zan jiraka shine ka tafi gurin wannan kawar taka mai kama da nunar rana, jabeer ya kwashe da dariya yace wacece me kama da nunar rana? Afeeya ta kara turo baki tace ohoo ka fini saninta, jabeer ya kasa tsayar da dariyarshi ya kamo hannuwanta ya hadesu guri ďaya ya sa bakinshi ya sumbace su a hankali haďe da lumshe idonshi, magana ya fara yi ba tare da ya bude idanuwanshi ba yace gurin Affan naje Afee, kinsan babu abinda da zai hanani zuwa gurinki da wuri sai ganin Affan, ta zare hannunta daya ta kai saman idonshi ta fara jan zara zaran gashin idonshi tace ni dai ban yadda ba ka fada min gaskiya ko in tura hannuna cikin idonka, ya buďe manyan idanuwanshi da sauri yace ki makantar dani kenan, tace eh mana sai inga da idon da zaka dinga zuwa yawo, yace haba Afee nah yanzu in kika makantar dani wacece zata aureni, ko bakya so ki samu anty wacce zata dinga kula dake, Afeeya tayi narai narai mayatattun idanuwanta tace yaya jabeer in kayi aure shikenan zan daina ganinka, zaka daina zuwa gurina,? zaka daina kulawa dani ko?, ya janyota jikinshi yace babu abinda zai hana jabeer kula da Afeeyah in dai yana raye, bana fatan abinda zaisa rana ta faďi har inyi bacci batare da nasaki a idona ba, ta kara narkewa a jikinshi kamar karamar yarinya tace to ay in kayi aure zan daina ganinka haka hajja ta ke cemin kullum, da karfi yace inji hajjan, afeeyah ta gyaďa kanta tace eh mana kullum sai ta faďa min da daddare wai in rage sabon da nayi da kai saboda zan sha wahala in kayi aure, ay nasan bazaka bari in sha wahala ba ko? ya gyaďa mata kanshi zuciyarshi na kara zurfi a cikin soyayyar afee, da afeeya tafi haka da babu abinda zai hanashi faďa mata abinda yakeji game da ita, girgizashi tayi yayi firgigit, tace to karkayi aure ko kuma ka aureni sai mu zauna gida ďaya ka dinga goyani muyi bacci tare ko, ya kalleta sosai yace kina sona? ta rufe fuskarta tace sosai ma, yayi dariya ya buďe fuskarta yace da gaske kikeyi, tace dagaske yayana, to in ban soka ba wa zan so, kaima ay kana sona ko?, yace fiye da yadda nake son kaina wifey na, ta daka tsalle tace bari inje In faďa ma hajja ta daina min gori, yace muje dai mu faďa mata tare ko, tace eh hakane ta kamo hannunshi cike da murna suka shiga ciki... Sai goma saura ya fito daga gidansu afeeyah, zama yayi kan dakalin gidansu yana kiran wayar Affan dan ya fito su ďan rage dare, sau huďu yana kirah ba'a ďauka ba, mikewa yayi a ranshi yace may be yayi bacci ko kuma yana can suna hira da umma, dakinshi ya wuce ya kwanta yana tunanin Afeeyah, Allah ya sani yana matukar kaunar afeeya, hakuri kawai zaiyi ya jirata ta gama sec skool ya aureta ya maida ita mallakinshi ya bata duk wasu nau'in kulawa da gata marasa yankewa, da wannan tunanin bacci mai cike da mafarkai yayi awon gaba dashi.... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣1⃣ By Aysha Ya'u Kurah Karfe 6 na asuba Alhaji basheer ya iso gida a gajiye, bacci sosai yakeji dan haka ya wuce ďakinshi don ya kwanta ya samu isashshen bacci, ya yi matukar mamakin rashin ganin zeenatu ta fito tarbarshi kamar yadda ta saba, amma sai ya share da tunanin ko itama bacci ne yayi gaba da ita ko kuma dai wani abun daban amma haka nan zeenatu bazata taba kin fitowa tarbarshi ba ko da kuwa bazaii kulata ba, da wannan tunanin bacci ya ďaukeshi... Ihu ya dinga ji kamar a cikin mafarki, a hankali ya buďe idonshi yaji bugun kofar da ake ma ďakinshi yaki tsagaitawa, da sauri ya diro daga kan gado jikinshi na rawa ya bude kofar, Salma da farida ya gani tsaye suna ihu suna kuka suka ce daddy Affan-- Da sauri ya katsesu yace me yasamu Affan din, kasa bashi amsa sukayi sunata nuna hannunsu saitin kofa, da gudu ya fita waje ya'yan hanjinshi sai kaďawa sukeyi, turus ya tsaya ganin masu aikin gidan da oyizah tsaye kan affan suna kuka jini ko ta'ina a kasa da kanshi, wani irin ihu alhj basheer yayi haďe da karasawa yana girgizashi yana kuka, da kyar yake iya hado sunan Affan ya kira saboda tashin hankali, daukarshi yayi bai kula da jini da fashewar da tsakiyar kanshi yayi ba ya turashi cikin mota, binshi oyizah tayi tana kuka tace alhj ina zaka kaishi, ya riga fa ya mutu, alhj basheer ya watso mata ashariyar da baisan yadda akayi ya fadeta ba ya shiga mota yayi asibiti da affan, likitoci kansu sun tsorata da ganin Affan, wani a cikinsu yace ranka ya dade wannan ay ya mutu, alhj basheer yayi kanshi yace ubanka ne ya kasheshi? Doctorn yayi baya yace sorry alhj, nan likitoci sukayi caa akan Affan duk da bawai sun sa ran yana raye ba saidai dan bala'in da alhj basheer ke musu, Cikin ikon Allah karfe 2 na rana Affan ya fara motsa hannunshi, cikin mamaki doctor musa ya kura ma hannun ido ko gizau yake mishi, ganin ba gizau bane yasa shi fita kiran sauran likitocin cikin murna, alhj basheer dai binsu yakeyi kamar zararre yana fadin bai mutu ba ko, dr musa ya gyada mishi kai kawai suka wuce dakin da Affan yake, sai hudu suka fito kowa yayi hanyar office dinshi, doctr musa ya kalli alhj basheer yace ka kwantar da hankalinka alhj muje office inyi maka bayani,, alhj basheer ya bishi office din ba tare da ya ce uffan ba,, Doctor musah ya kalli alhj basheer cikin damuwa yace alhj ka saurareni da kyau kuma duk abinda zan faďa maka kasani bani nayi ba kuma ba wani bane yayi Allah subhanahu wa ta'ala shine ya jarabceka kuma ya jarabci danka, saboda haka dan Allah alhj kayi tawakkali saboda cuta ba mutuwa bace, alhj basheer ya share hawayen da ya zubo a idonshi yace faďamin komai doctor, fadamin abin da ya sami Affan,, doctor musah ya mika mishi takardun hotunan kwakwalwar da sukayi ma Affan, ya karba hannunshi na rawa yace bazan gane komai a ciki ba doctor kayi min bayanin komai da baki, doctor musah yayi ajiyar zuciya yace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61