Chapter 9
Chapter 9
sukayi suna kallonta, "Hello,burgu mai kake cewa waim" "Had'uwa da BUBA JINI kuma ?" "Shikenan zamuji da Wacce yazo saidai ka kaishi zuwa gobe dan yanzu akwai abinda nake shirin yi ne" Saida ta ajiye wayar ta kallesu kafin suka kula da yanda ta basu umarni cikin kankanin lokaci kuma suka bi batare da sun sani ba(sameemah kenan). ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____***GIDAN GANDU***____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤07❤ Tashi sameemah tayi kaman mai kiwuyar tashi a wajen kafin ta nufi kofar da alhaji babban yake. Yana kwance anyi masa shimfidi a tsakar dakin saidai idonsa yana kallon mai wucewa,kallon sameemah yake da son gano wacece, "Wannan din wacece?" "Sameemah ceh " "Ohj sameematuh ceh,toh yah labarin mahaifiyar taki kuwa an ji labarin itah y'ar inace ?" "Mahaifiyata kuma ,ita kam ai tah rasu" "Yaushe amma banida labari. Koh?" "Ina nasan maka ni zaka tambaya,ya jikinnaka?" "Lah jiki da sauki yar nan kinsan tsufah ne " "Eh AI naga alama kam" Tafada tana kare masa kallo daga inda take zaune, "Toh nizan tafi allah yasa kurigamu gidan gaskiya,ina haka ake cewa?" "Ni zaki tambaya,toh kigaida ummartaki idan an ganta" "Kai ni karka dameni da wani zancen na gaisheta,inaga ma kaine kake kallonta saboda ka kusa jona sahunsu,haka kawai zaka wani dameni da cewa in gaida wanda yah mutu,kai idan kaje kace ina gaisheta " "Lallai yar nan allah yayi ja'irah" "Ashe da sauran hankalinka kasan mai kake,to sai anjima allah yah sawwake" Daga haka ta kade skirt dinta tabar wajen tana buga feduwa,tai hanyar waje,bayan tah gyara gyalen wuyannata(dan itah yanda maza suke ficewa daga gida sanda suka so fita haka take ficewarta sai sanda ta dawo). Washagari da safe da wuri tabar gida saboda shirye shiryen haduwa da buba jini,dan kaff garin ba kungiyar dabar da ta kai tasa wajen kwarewa da kuma bud'adden ido. Lokacin da suka isah ainihin inda sansanin yan dabarsa take saida burgu yayi Mamakin irin tsarin da akayiwa wajen kaman na yan boko haram. A harabar cikin wajen suka samu anyi shimfid'a da kayan marmari duk na tarar seemah jar wuyah da yaranta. Tun daga nesa kuwa buuba jini yah hangosu itahce a gaba suna biye da itah ,har Mamakin irin biyayyar da yaranta suke mata yake,saboda ko shi daya tara manyan yan daba,basa masa biyyayah yanda yaran seemah suke mata biyyayah. Tana zuwa saida ta zauna a tsakiyar daddumar suna kallon juna ita da buba jini kafin sauran yaran ta,wato su burgu suka zauna a bayanta. Murmushi yayi tareda dage girar hagun irinna yan iskannan kafin yace, "Barkanki da zuwa" Itama irin yanda yayi mata tayi kafin tace, "Na amsa gayyatarka ,saika fadamin meyake dauke a bakinka da har ka nemi yin magana dani,kuma har cikin gidanka?" "Ba komai bane ,inaso ne kawai ki had'e da kungiyata muzama d'ayah" "Meyasa ka bukaci hakan" "Saboda keh macece,nasan ba iyah dan kungiyah yan siyasa suke nemanki ba,harda wani kudurinsu na daban,kinga idan muka hade ,karfin izzarki da kuma tsaro zai karu,nikuma kinga saiki kawo mana hankalin yan siyasah su bamu aiki,nasan bazaki ki amincewa ba" "Idan kuma naki amincewar fah mezakayi?" Kallon idonta yayi yanda take maida martani kaman ba a gabansa take ba ,babu alamar tsoro a idonta, "Tunda kika shigo gidannan dole ki amince da bukata ta " "Idan naki fah mai zai faru" "Toh bazaki bar gidannan da kafarki b............" Tin kafin yah karisa maganar,seemah ta yanka jijiyar hannunsa daya rike wukar dayake mata barazana da itah cikin kiftawar ido. Kururuwa yah fara yana danne wajen da jini yake tah fitah, "Kai din dama ba babban shege bane ,ya za'ayi wanda yake kiran kansa da suna jini kuma yayi ihu dan jini yah fito daga jikinsa?" Yan dabar sa ne suka iyo kanta da sauri,sai kuma yah dakatar dasu ,cikin dauriyah da cije baki yace "Karku yi mata komai,kuyi hanzarin shiryah motah yanzu mu tafi asibiti,banason kowa yayi mata hukunci,ni nan da kaina zan hukuntata,sai tayi dana sanin abinda tah aikata" "Kai dakata da surutun haka,duk naji su,bana bukatar neman ayimin maimaici,saidai kai din kayi hanzari,domin in bakayi sauriba jininka zai kare a nan wajen,kaga sai muga wa zai baka ransa kazo daukar fansar dashi" Mikewa yayi idonsa yayi jawur dan azaba,fadawa mota yayi tareda watsawa sameemah wani mugun kallo,na alamar zamu had'u. Ita kuwa gogar ko a jikinta saima murmushi da tayi masa tareda daga masa hannu tana yimasa bye bye. Duk abinnan da ake,su burgu mutuwar zaune sukayi lokacin da suka ga abinda sameemah ta aikata,dan sun saddakar yau kam kwanansu yah kare a wajen buba jini,dan duk fadin garin babu wanda bai sanshi wajen yanka ba da kuma aika aika,kowa tsoronsa yake babba da yaro. Saida ta shuri burgu kafin yayi ajiyar zuciya yace , "Ma'am shugaba,sun yanka mu ne" Zefah masa makullin mashin tayi kawai batare da tace komai bah. Bayan sun hau mashi dinne suna tafiyah burgu yace, "Amma shugaba bakya ganin yanzu muna cikin matsala" "Dallah ni yi shiru ka rufemin baki ,bakuda aiki sai tsoron tsiyah,ni narasa meyasa ma nake tare daku har yanzu" "Yi hakuri bazan kuma bah" "Kudin hannuna yayi low,kaini gidan badariyyah,zan karbi bashina da tazo har gida ta karbawa mijinta a wajena,yau zanga mai hanani fitowa da kudina a cikin gidannan,in tareda uwar wani ake samosu" "Gaskiya kam shugaba kiyimasu rashin mutunci ba shin fah ya kusa wata guda a wajensu,babu ma yah wannan mijinnata kullum yana wajen caca" "Toh ina ruwanka,kai waye zaka zagi mijin yar uwata,ko cewa nayi ka tayani,kudinka ne koh nawa?" "Kiyi hakuri shugaba an iso gidan " Sauka tayi daga kan mashin din kafin tacewa burgu, "Jirani na Shiga na fito,dan ko bayanan saita fadamin inda yake" Langa langan kofar gidan tah buga da karfi,saida awakin gidan suka dungura suna d'aure,badariyyah ce ta fito da sauri,suna had'a ido da sameemah ta buda wani uban salati da a'uziyyah tana dafeh kirji. "Eh zaki kori shedan mana tunda kinga nice,na rantse ko dujal zaki kora saikin fitomin da kudina,koh kuma ki fadamim inda lalataccen mijinnaki yake naje na karba" "Haba sameemah babu koh Sallama,kuma ai saiki shigo mu gaisa koh?" "Ba gaisuwa ceh ta kawoni ba,kudina nazo karba,saiki bari sanda nazo zumuncin saiki ce ga wajen zama,ki fitomin da kudina yanzu ,dan babu d'aga kafa yau,koh inna karime zaki sayar bai dameniba,ni kudina nasani,tunda ba da wani shege aka hadu aka tarasu ba" "Kiyi hakuri sameemah,wlh ko kudin cefane nima bai baniba,kuma ai ni yar uwarkice" "Hmmm ke kikasan wannan yaren,fad'amim inda yake yanzunnan,ko kuma na tattare y'an awakincan nayi kasuwar dabbobi dasu yanzunnan" Tafad'a tana nuna awakin Badariyyahn, "Ahah kiyi hakuri,indai baban iliyah neh,wallahi yana rumfar kofar gidan Ashiru mai shayi" "Dama nasan ai duk munafurcine,ba sonsa kike na,indai akan kudinkine" Juyawa tayi ta fice daga gidan bayan tayi boll da langar data gani a tsakar gidan miyar kuka ta bushe a ciki, "K'azamai kawai,ai dole kuyi ta gudawa" Bayan ta fitane Badariyyah ta sauke ajiyar zuciyah tareda cewa, "Na rabu da masifar yau kam,saikuma wata ta gaba" Ashiru mai shayine ya k'ara gyara zamansa zance yayi dad'i yace, "Hmm AI baka saniba BALA,shi sha'anin kudi a bishi a hankali kawai" Audu ne (baban iliyah mijin Badariyyah),wanda shine mai raba cacar yana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55