Chapter 12
Chapter 12
gari yana wayewa ya kama hanyar tasha bayan yayiwa kowa sallama,dan baya fatan sake gamuwa da irin wannan hukuncin da tunda uwarsa ta haifeshi ba'a taba masa yau gashi seemah jar wuyah tayi masa. Saida aka shafe kusan kwana biyu wata fitinar bata sake kunno kai ba tun wacce akayi da daddare tsakanin dan liti da sameemah. PORTHACOURT:SOLDIER'S BARRACK. SALEEMAH ceh a zaune akan kujera tana chatting ta nad'e k'afa d'ayah kan daya kaman wata yar basarake. Kyakykyawace ajin farko ga tana ji da ilimi da kuma matsayi,kowa a cikin barikin shayin wani abu ya had'ata dashi yake,dan ko fita zatayi sojojin da suke rakata sun ninka wanda suke raka mijinnata idan zata fitah. Itah kadaice a wajen mahaifinta wanda shine General a duk gabad'ayah barikin,yataka matsayi da dama Sannan allah ya jarrabe shi da son yar tasa wanda yake jinta a cikin ransa,baya kaunar duk wani abu dazai tab'a farincikinta bare kuma lafiyar tah. Tun lokacin da tah dawo daga karatunta a Germany,suka hadu da sameer yah kawo wasu document wajen mahaifinta,tun daga wannan ganin taji duk duniyah babu Wanda takeso saishi. Har daki tasami mahaifinnata ta fad'amishi ,cikin kankanin lokaci General Musa Funtuwa,yah amince dan shima yah yaba da hankalin sameer din,saidai yanada zuciyah da kuma tsayayyan ra'ayi,amma indai kyan haline yasamu lambar yabo kaf barrack din akan haka. Cikin kankanin lokaci yah kirah sameer yasanar dashi bukatarsa,da farko yace yah bashi d'an lokaci,amma daga baya yah amince saboda mutuncin general din a idonsa,sannan kuma duk da saleemah bata had'a dukkan abinda yakeso ba,tana da wasu abubuwan,dan itah din macece da bakowa zai kalleta ba baiji ta burgeshiba. Bayan yah amincene soyayya ta fara kulluwa tsakanin saleemah da sameer duk da ba wasu cikakkun masoyah bane ,saidai kowa yana daraja lokacin kowa. Saidai soyayyar da saleemah takeyiwa sameer din a gaban kowa take nunawa har da kuwa iyayenta. Saboda soyayyar daya ga tana yiwa sameer ne ya sashi d'aga matsayinsa zuwa major general sannan yah aura masa itah. Lokacin da aka daurah aure,gida guda yah basu tareda colony na sojoji guda akasa a area gidannasu saboda tsaronta da kuma yi mata hidima. Masu aikin cikin gida ma part guda aka waremusu,saidai duk wadda tazo aiki saleemah tah nuna batayimata ba ,a ranar ake sanja ta a dauko wata. Masu kulada kayanta daban,masu kulada abinci daban,masu kula da sashenta daban haka masu kulada sashen mijinta su ma daban. D'anta kuwa suna ta haifeshi ne,dan said tayi kwana uku bata ganshiba yana wajen nanny,ita kuma tana harkar gabanta. Duk inda ka wuce ba sunan dayake tashi sai madam,shi kansa sameer bai isa yasaka ta abinda batayi niyyah ba,sai idan taga ransa yana baci kafin tah aikata abinda yah ce. Mai shara ce ta zo goge palourn amma tana tsoron yiwa madam din magana saboda kar a koreta kaman yanda ake yiwa sauran. Kulada itah saleemah tayi a tsaye kafin tace mata, "Ke kuma miye kika wani make a can lumgu,kafin kifara sharar jeki waje duk sojan da kika gani kice ina san ganinsa yanzunan" Cikin sauri kaman ana turata da iska tafita domin cika umarnin nata,koh minti uku batayiba said gata da wani soja sun shigo. Saida ta gama abinda take a wayar kafin tace," "kuje kaida driver gidan kawata Surayyah zata baka sak'o ka kawomin,yanzunnan" Saida yah sankame ta sara mata kafin yace, "Yes madam" Ta shi tayi ta koma daki dan bawa mai sharar daman gyara wajen. Tana cikin sharar ne sameer yah shigo daga wajen aiki,babu kowa sai kawai mai sharar tana ta aikinta, "Saleemah tana nan" "Eh ranka yah dade yanzu tah shiga ciki" Bai amsa mata ba said wucewa da yayi d'akin saleeman,nan ma saida yah jera sallama uku bata jishiba. Samunta yayi tah kure wakar Alan walker,ga kuma chat tanayi. Jin an fisge wayar tane,yasa ta saurin d'agowa tana kallon sameer din,cuna baki tayi kafin tace, "Honey ka dawo neh?" "Ba zancen honey bah,ki amsa gaisuwar danayi tukunna,koh kina so ki cemin bakiji sallamar ba?" "Ahah ni banjiba" "Toh yanzudai ba wannan ba ina abbana yake? Nasan sun dawo daga school tun d'azu" "Nima ban ganshiba,amma ai sun dawo yana wajen su nanny d'insa" "Wai saleemah anyah kuwa ke uwace ta gari,yanzu haka iyayenki suka miki,d'an ki haifeshi a cikinki amma kuna gida d'aya yah dawo a makaranta koh bai dawo ba ke baki saniba,sai chat da friend shi kika iyah kawai" "Kai honey fad'anka yayi yawa kwana uku baka gida,kana dawowa babu hug din kayi missing dina ,sai fad'a" Ficewa yayi yah tafi d'akinsa bayan yah mata kashedin ta d'auko masa yaronsa kafin yah fito. A haka badan taso ba tah nufi sashen da nanny din farouq din suke. A zaune tasameshi yana cin abinci har sunyi masa wanka,yana kallonta kuwa yah taho da gudu yana kiran mommy. Tsugunnawa tayi ta rungumeshi itah kanta tana son d'annata saidai rashin halin kulawa irin nata kawai, "Mommy tun d'azu na dawo daga school,kuma anty tace wai gobe zamu koma sabon clash" "Eh hakane ya kk,ka gama cin abincinne?" "Eh mommy ni bana son abin abincin tsami yake yi(mayonnaise) " "Shikenan muje abbanka yadawo yana nemanka" "Hee I mish abba" "Okay toh muje" Sanda ta koma sashennasu har yah fito daga bandaki da towel a kansa yah watsa ruwa,yana kallon yaronnasa yah mika masa hannu yana dariyah, "Oyoyo abbana ya kake yah makaranta?" "Fine abba,na dad'e ban ganka ba abba,sai yanzu" "Eh my boy Abba yah tafi aikine,amma yanzu yah dawo,zamuyi wasa koh" "Eh Abba " "Yawwa Toh yanzu kaci abinci sosai" Saida yah yatsina fuska irin ta yara kafin yace, "Ni Abba bana son mayonnaise indomie zanci" "Shikenan kije mommy ta baka koh" Har suka gama firar saleemah na tsaye ta nad'e hannayenta tana kallonsa,saida ta ji an sakota a zancen tukun tah mikawa farouq hannu akan yazo su tafi,had'e fuska tayi kaman mai shirin fashewa itah a dole yana magana da farouq banda itah. Bayan ta gama hidima da farouq dinne tah sake turashi sashen su nanny din,sai tsuka take itah a dole ta gaji da yi masa aiki. Fitowa yayi daga dakin yasha kananan kaya amma na kakin sojoji,sosai ainihin yarintar sa yah ,tundaga fitowarsa saleemah tah kafeshi da ido ganin yanda kullum kaman kara kyau yake,shima yah kulada irin kallon da take masa saidai yasan inda kallon nata zai nufah wanda in akaje shi zata bari a ruwa. Kujera yah ja ya zauna a wajen cin abincin,kafin ta tashi tah zuba masa abincin,bai yi wani murna dashi ba saboda yasan ba itah ce ta dafa masa ba da hamnunta,duk da yah dade bai dawo ba bazata iyah yi masa girkiba ko d'okin zuwansa saidai tayi ta masa korafin baya yimata soyayya yanda ya kamata. Bai fi loma biyar yayi ba ,yah rufe abincin tareda cewa yah koshi, "Haba honey Har ka koshi mai ma kaci toh" "Shine cin,bari na fitah akwai dan aikin dazanyi saina dawo" Rike rigarsa tayi tana masa shagwaba irin ta sakalan yarannan,dan dama ta kware tah wannan fannin, "Uhm uhm shikenan daga dawowa sai kace zaka fitah,gaskiya yau gabadaya lokacina ne ,kuma kasan nafi bukatarka fiye da kowa yanzu" "Saleemah ba dadewa zanyi ba ,in anjima zan dawo daga nan koma miye kisaka ni a gaba kiyi dani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55