Chapter 39
Chapter 39
"Lafiyar ta Kalau,dama inaso naji in kina gida yau zan zo miki mu gaisa baby" "Kaman wane lokaci" "Kowane lokaci kika saka duk dayane" "Ka Bari sai anjima zanyi wani aikine" Ajiye wayar tayi tah shiga wanka domin zuwa wajen yarannata. Bayan surayyah tayi wannan gudunne gashi bata samu abin hawa da wuri ba hantar cikinta sai kadawa takeyi kaman zata fito waje,abin haushi kuma har saida ta yi kusan wata awar kafin sameemah ta zefo hancin motarta wajen cikin takama. Dukkansu tashi sukayi duk da ba itah ta saka masu dokar hakanba su suka sakawa kansu. Ajiyar zuciyah ta sake bayan taga dukkansu hankalinsu ya dan koma jikinsu. "Yawwa nasan kowannenku Yaga yanda ake saka ku aiki sosai,wasun ku sunsan dalili wasu kuma basu sani ba,toh kaman dai yanda kuka sani,daga rana i ta yau,wato wani satin ina so sunan kunhiyar nan ya tashi daga marar lasisi zuwa mai lasisi,wato zan mayar ta zuwa karkashin gamnati ta hanyar shiga kungiyar vigilantee. Duk abinda zamuyi zai zama babu mai kaimu kara bare kuma ya dau mataki,walau tah hanya mai sauki koh ta hanya marar sauki ina so mu saki ruwan rashin mutunci a garinnan ban daukeba har cikin gidan gandu domin kawo sauyi a cikin garianan sannan kuma muma mu kafa namu tarihin da wanda za'a dunga tuna mu dashi" Surayyah ce ta daga hannu tace, "Amma shugaba muma aikin vigilantee zamu dungayi mata damu,baza'a dunga aikin daba ba kenan" "Ke surayyah ke fah dama nakula duk da horon da aka baki har yanzu kina cin kasa,toh ki kiyayeni in dan auta kike ji nima nan itace,dan haka banson harkar lalaci duk wanda kika ganshi anan wajen walau mace koh na miji sonake ya zage dantsensa wajen nuna kwazo,banason abinda zai kawomin nakasu gameda burin danake son ai watarwa sam. *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤27❤ "Ina su Lubna da Kubrah" Dukkansu daga hannun su sukayi dan dama duk cikin su babu wanda tayi magana amma daga ganinsu kaga mata masu kirar karfi da kuma zarrah(ina baku mantaba sune wanda suka kira sameemah lokacin da yaron buba jinI yakeson zanta cikin jeji). "Yawwa ina so aikinku yahada da surayyah,duk wani wanda yayi Rashin mutunci yashiga dakin uwarsa toh ku nakeson ku shiga ku daukoshi sannan ku mikashi ga mazan su kawomin shi,saboda bai kamata muna gyara kuma mu bar maza su dunga shiga gidan mutane ba any how,jibi zanje mu sake zama da shugaban tsaro a cikin babban birini,idan abu yah tafi normal za'ayi bikin saka ni akan kujera,ku kuma za'a baku uniform bayan lokacin. Kowa zai iyah tafiyah,akwai training daga karfe bakwai na safe,sauran kuma burgu ya cemin wani bai zo da wuri ba hmmm" Ta shi tayi ta fita saboda ta gama isar da sakon da tazo isarwa dama. Inna ramatu ce zaune a daki itah da yayanta sameerah da zainab,wanda babu wanda ya kaita rawar kai itah a dole zatayi aure,sai wani rangwada takeyi tana cuna baki, "Yawwa ummah kikace zaki kaini wajen malaminki ta yanda zan mallakeshi kk uwarsa bata isa ta fada masa yajiba koh?" "Hmm ke harki na ganin zan manta da wannan zancen nne,ai kwantar da hankalinki ni kaina malam shine dogarona shine dalikin dayasa na kai yanzu a wajen ubanku,da badan haka ba da yanzu nasan inda dare yamin" Sameerah ce ta yah tsina fuska kafin tace, "Nikam da ina baki shawara karki bi ummah wajen wannan mutumin,idan ta kama taimakone ta karbo miki basai kinje ba kawai" Saurin katseta inna ramatu tayi tareda cewa, "Ke sameemah banason shashancin banza,dan ubanki ba shine dalilin dsyasa kikayi auren farin ba,sannan kuma shine yabaki sa'a kika Rike bazawarinki a hannunki kinsan da haka" "Eh ni dama bance ba shine yake bani sa'a ba ,kawai tun sanda yah turmusheni bana sha'awar komawa wajensa da dadin rai" "Kiji sameerannan wallahi ke yar bukulu ce,kina zagewa yana baki sa'a amma ni kice bazanyi ba koh,bana san shawarar taki toh,idan ba da neman taimako ba ai mazan sai a slow" Haka suka cigaba da zancensu har daga karshe aka yanke lokacin da za'aje wajen bokan(malami in jisu da fada). Yauma sameemah da wuri ta tashi saboda tafiyar dazasuyi tana cikin ranta sosai. Duk da sammakon su saida suka samu mutane a wajen sun rigasu wanda hakan ya bata mata rai sosai,akan layi suke amma hankalinta baya kan wajen kwata kwata,bata ankaraba sai jin hannun wani tayi akan bayanta wani Yana shafawa,zuyawa tayi da niyyar magana sai ta hada ido da wani saurayi ya sha askin wizaye da kuma sabullalen wando,lashe baki yakeyi yana binta da wani dan iskan kallo, "Yadai yan mata kinaso a cigaba ne ko yah?" Karisa juyawa tayi sosai tana kallonsa,dauke da dan iskan Murmushi, "Eh mana ina so a cigaba amma yanzu kamata yayi ya zama layina ne,nice zanyi koh" Wani washe baki yayi jin abinda tace tana wani kashe muryah. Cikin lokaci kadan sameemah ta rike ta rike kaciyar sa ta cikin wando da karfi kaman zata cireta,ihu yasaka iyah karfinsa amma hakan bai sa ko motsi tayi ba,saima wani daskarewa da tayi duk kuwa da dukan da kuma kokarin zanyeta da akeyi. Wani ne yah shiga da gudu ya fadawa shugaba abinda ake ciki,saboda yaron da ta rike dan sane,dama haka yake yi idan mata suka zo wajen neman wani abu,idan kika ki yin abinda yake so sai yasa a koreki,wai ana cewa yana da ciwon zuciyah da kuma dan dabin hankali,idan ba'a barshi yayi abinda yakesoba zuciyarsa zata buga. Security ne suka rike hannunta ta kowanne bangare kafin cikin saka karfi suka cire hannunta daga inda ta rike,sannan har ya galabaita koh ihu baya iyawa da kyau sai haki. Duk da hakan idonta yana kansa saima kokarin nufarsa da tskeyi tana huci,shikuwa ganin hakan da gudu yayi bayan wani security na miji kaman yaga aljani. Ganin tsaida itah zai musu wuyah ne yasa secretary yi mata magana akan ta shiga da bujatarta duk da lokacinta bai yiba,saboda a samu ta rabu dashi da ransa. Su burgune suka bi bayanta shida lawyer ta wanda idonsa yayi tsuru tsuru. A office din secretary suka tsaya itah kuma ta shiga office din da takardu a hannunta. A zaune yake yana zuyawa akan kujerarsa duk da yadan manyanta saidai zama a cikin AC,bazai bawa mutum damar ganin hakan ba. Itah ma zama tayi a kujerar guess wanda take fuskantarta tun kafin ya bata izini,karemata kallo yake na kurullah kafin ya karbi takardun hannun nata. Saida yagama dubawa tass kafin yah sauke dan glass dinsa yana kallonta, "Mekike nufin,cewar bansan labarinki ba,da irin abinda Kika yiwa alhaji bala,saboda ki karbi kujerar aiki daga hannun yaronsa,ko kuma dan kin ga kina juya wasu yan yara a yankinku shi zai sa na yimiki sign sannan na doraki akan kujerar tsaro. Sannan kuma kin daki yarona a waje,duk da nasan akwai abinda yayi miki amma baki da shaidar hakan,saboda yana da takardar asibiti na cewa bashida cikekken hankali,kinga yanzu dole ki amsa kiran kotu" Karishe maganar yayi yana shafa gemunsa tareda tsira mata ido dan yaji mai zata ce. Murmushi tayi mai kayatarwa kafin tace, "Dama inada wannan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55