Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,263 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya kad'a ya fice waje,gurin abokansa su sule maye. Ring wayar sameemah tayi,tana tsaka da cin abinci wanda tabawa wani yaro a gidan yah sayo mata,dan sam harka da miyar kukanne bazata iyah ba sam,miyah babu wake ba bu ishshshen kayan miyah sai uwar kuka kaman zatayi magana,kana sakawa a bakinka kafi zabuwa(ajino moto )zai yi cuuu a bakinka kaman zaiyi magana. Saida tayi tsuka kafin ta duba wayar dan ganin waye ya takura mata a lokacin,saida tah daga kafin taga ashe alhaji bala ne,yah mutsa fuska tayi kafin tace, "Uhm inaji miye?" "Haba sanyin zuciyata yah ina binki kina nuna min halin ko inkula,kinsan fah da arziki nake nemanki" "Eh nasani shine nace menene yah faru yanzun" "Inaso idan bazaki damuba gobe da kaman hantsi zan turo mota a daukeki zuwa gidan shakatawa ta saboda inada free lokaci goben kinga saimu wuni muna shakatawa,koh yah kika ce?" "Eh naji idan na shiryah goben zanyi maka magana" "Yawwa kefah komai naki na musamman ne........." "Idan ka dameni zan fasa zuwa,dan ba'a lallamata kamar wata yar yarinya saboda abinda naga dama nakeyi,bana bin ra'ayin kowa" "Shikenan gimbiya tah ai girmanki ne" "Toh naki koma girman waye kai yah shafa ni ba matsala bace,sainaga driver naka goben" "Shikenan,gaskiya naji dad'in amin..........." Kittt ta katse kiran kafin yakai ga karisah maganar sa. Yau ba wata tsiyah koh busa hayaki ,ciki yana dauka tabi lafiyar gado. Can wajen tsakiyar dare sameemah tayi zumbur ta tashi daga kwancen da take,ga jikinta sai rawa yake,saida ta rike kanta ta dad'e haka kafin ta sau kan tana maida numfashi,komawa tayi ta kwanta tana kallon silin da haka har gari yah waye bata koma bacciba. Kaman yanda sukayi da alhaji bala kuwa,can bayan rana tayi sameemah tah fesa wanka kafin tazo ta Zauna a gaban kayannata. Tah dade tana nazari kafin tafito da wani material anyi masa dinkin roba dinnan,irin wanda yake bin jiki,ga adon duwatsu da aka baza a jikin dinki,a takaice dai dinkin ba karamin amsar jikinta yayi ba gashi kalar pink. Takalmi tasaka shima pink din kafin ta daurah gyale shima pink akan kafadarta. Batayi wata kwalliyah mai yawa a fuskarta ba ,sai iyah dan lip gloss da tasaka kawai dakuma ruwan turare a jikinnata,ita kanta da ta kalli kanta a madubi saida tayi murmushi saboda kyawun da tayi. Cingam ta zefah baki tareda toshewa fuska da bakin glass,sannan tah zari jakarta itama pink tayi waje. Tundaga bakin dakinnasu ake karemata kallo ganin yanda tayi shiga kamar ta sauko a jirgi,tana fita kuwa idonta yayi tozali da wata zazzafar bakar motah a kofar gidannasu,tana isa gaban motar wani yah fito a motar yah bude mata kofah tah shiga kafin yah mayar yah rufe. Fiiiiii suka figi motar suka hau titi,sai alamar kurar inda suka tashine kawai yah saurah. Mutanen anguwa kowa yah bude baki yah rasa abincewa sai an lafah tukun kowa ya fadi albarkacin bakinsa. ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤11❤ " Kai kai isiyaku ka ga abinda nagani kuwa" Mai shayin kofar gidannasu ne ya fada yana jijjiga kai, "Hmm nikuwa nagani dan ma kai sanda ta fito daga cikin gidan baka gantaba kana sunkuye wajen tattara kofunan ka, "Gaskiya kam wai haka tah koma ne,itah ma ta koma bin mazajen kenan" "Kai amma ita bin mazannata mai aji takeyi ,ka kallifah irin motar da aka dauketa a ciki,aradu tunda nake ban taba ganin an dauki wata y'ar unguwar nan a irin wannan motar,kai motar fah ta zo matuka" Manjone yah karkace kai bayan yagama shan shayinsa ya ajiye kofin, "Kai Wai wa kuke magana ne,kaman fah wannan kanwartawa nagani wato jar wuyah,ko ba ita bace" Sule mayene shima yah gyara zama kafin yace, "It ah ce mana,kai bakaji nayi shiru ba ai haushine ya isheni,yanzu ina zaune a wajennan tasan ina matukar santa Amma ta tsallakeni tah shige wancar motar " Saida manjo yah gama kyakyatawa da dariyah shida mutanen da suke wajen ,har yana shirin fadowa daga tebur din, "Kaii Baaba dama san ta kakeyi,toh ai ni bansaniba" "Sule mayene yasake turbune fuska ganin yanda suka sakashi a gaba suna dariyah kaman sun samu mahaukaci, "Eh mana ai na dade ina sonta,kana ganin mace har mace,kuma ita ma nasan tana sona sosai" "Toh AI lefinkane abokina ,kasan ni babban yayantane kuma ance babban yaya uba,mai yasa baka zo kasameni ka fad'amin ba" "Kai kaji min mutum,dan iska kana garinne,basai jiyah muka ganka ka bayyana ba kaman tsohon aljani?" "Toh dai naji d'an heeege kai ,kana neman abu a wajena kana zagina,yanzu dai ka bani sadakinta nairah dubu talatin,kuma bazan rageba daga nan,Sannan dole ka ringa gaisheni duk inda muka had'u,idan kuma wani rashin arziki yah had'amu dakai toh rufe ido zanyi na kuma manta da ka bani dubu talatin nayi maka rashin mutumci" "Ba za'ayi hakaba indai akan seemah ne babu abinda bazan iyah ba" Motar bata yi parking a ko inaba sai gidan shakata war alhaji bala,budewa kofar tayi tana karewa gidan kallo tareda zare glass din idontah. Yaron alhajin daya kawota ne ya katseta da kallon gidan ta hanyar cewa, "Nan zaki biyo madam" "Binsa kawai tayi batace komaiba har suka iso parlorn alhaji bala din. Yana zaune yah baje akan kujera iskar AC tana kad'ashi,yana kallonta yah tashi da sauri yana washe hakora,kaman ance masa yaci zab'en shugaban kasa, "Lale lale da zuwan gimbiya sarautar mata,samu waje ki zauna,bari a kawo abin motsa baki,kai IDI maza a kawo abin mak'ulashe yanzunan" "An gama ranka yah dad'e" Da sauri idi ya fice daga parlorn,yayinda shi kuma uban gayyar wato Alhaji bala yah dawo kujerar da take kusa da wacce sameemah tah zauna" "Kallonsa tayi cikin yahtsina fuska irin ta tattatun shu'uman matannan kafin tayi masa magana tana yin bubble da dank'on cingam din da yake bakinta, "Alhaji ka damu akan nazo nazo,toh gashi nazo saika fadamin menene dalilinka na kirana,kana ta zancen shakatawa gidan rawa zamuje koh gidan shaye shaye" "Ah kina zuwa gidan rawane da dakuma shaye shaye?" Yah tambayeta da mamaki, "Hmm lallai kai karamin dan akuyane a cikin awakin,ai inaga nafi sabuwar bishiyah lokacin damina rausaya,sannan fidda hayaki kuwa,koh itacen murhu bazai nuna mini fitarda hayaki ba" Maganar da sameemah tayi masa ta bashi haushi amma haka yah murkushe ta yah hadiye kaman wanda tayi masa asiri. "Toh shikenan barina kira idi tun baiyi nisa ba yah had'o miki da taba" "Ahah mai kake nufi banasha cigarettes,wannan kayan saka mutum baki,saidai dulah,itama karka wahalar da kanka dan ba kowacce nakeso ba " "Toh shikenan ranki yah dade,yanzu dai mekike bukata" "Kai me make bukata dai?saboda kai ka damu nazo ba nice na ce zanzo ba,yanzudai ina bukatar shiga bandaki nuna min dakinnaka zan shiryah tukunna" AI kuwa cikin rawar jiki har murmushi yake ya nuna masa dakinnasa,dan shi a ganinsa koh irin dabarunnan irin na mata zatayi kafin azo kan harka. Wuceshi kwas kwas tayi ta nufi dakin,har tazo bude klfar zata shiga sai kuma tazuyo tana kallon alhaji bala, "Am yawwa nace ba,karka kuskura ka biyoni ka jirani na fito dan ba dad'ewa zanyi ba" Saida yayi dariya irin ta yan duniya kafin yace, "Ahhhhh karki damu wane irin shigowa kuma,ai ki gama

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});