Chapter 42
Chapter 42
cizon yatsa shida mutanensa da kuma kudirin daukar fansa. Yayinda aka bar kuma yan kungiyar sabuwar tawaga da murna da kuma kudirin yin aikin su cikin nasu tsarin. Dadai lokacin sallah azahar ne manjo ya fito daga masallacin unguwarsu,har sannan wannna rigar gadon ce a jikinsa bai cireba. Yah karyo kwanar gidan kenna yayi turus ganin sule maye a kofar gidansu yana jiransa,kokarin komawa yakeyi amma babu dama saboda sun riga sunyi ido hudu shi da shi. Ga shi ba dama yakawo masa wani uxirin dan da alama bai yi shaye shayenba idonsa tar yake,maitar karban kudinsa tah motasa. Cikin sanda manjo yah isa har gaban sule mayen yana wani sunne kai,tun kafin yayi magana sule maye yace, "Karkace komai manjo billahillazi kudina zaka bani,dan nima daka gsnni nan ba kudina bane sato su nayi,kuma masu kudi sun ganoni dasu ma muke tare,dan haka ka bani na basu ,ko kuma na nuna ka nace kudi yana wajenka ehe" Toh manjo ka shiga uku,za'a manjeka kenan😀😀😀😀. *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤29❤ Wuri wuri da ido manjo yayi jin abinda sule maye yake fada. Gabadaya jikin sa rawa yakeyi,ganin yamda wasu mutane suka zagayesu da alamar sun fi su manjo iyah shege. Bakin manjo sai motsi yakeyi amma ya gagara fidda ko kalma daya,wani daga cikinsu ne yah kinsa masa duka a ciki,aikuwa ya hada kururuwa yana neman taimako. Ganin da sukayi manjo babu kudin a wajen sa cikin kankanin lokaci suka fara dukansu kaman sun samu kayan wanki. Tun manjo da sule suna ihu har sukayi shiru suna karbar ruwan dukan dayake Ziyartarsu. Karar motace da hayaniya ta tsayar da su daga jibgar su manjon suna kallon waye yake tahowa. Motar sameemah ceh a gaba sai wata mai bodi an cikota da mutane kuma anyi mata paint irin na uniform din jikinta. Fitowa tayi daga motar ta mutane suna binta a baya harda yan kungiyarta,a wajen su manjo ta tsaya wanda sukayi futu futu da rairayin wajen,saboda burburwar da sui tayi. Kallon masu dukannasu tayi tareda tambayar su abinda yah faru, D'aya ne daga cikinsu ya zayyane mata abinda yah faru,kuma ta yadda da hakan dan sunyi maganar kudin kuwa ita da manjo,sannan tasan ko za'a kashe sule maye bashida inda zai samo dubu biyar ma bare har dubu talatin,dan matarsa ma da shi kansa innarsu ce take ciyar dasu. Hakuri ta basu inda suka ce,dama tafiyah zasuyi tunda sun daki na kudinsu,saida suka bace daga layin kafin Sule ya karkace baki yace, Dama nasan har yanzu kina sona kawai zancen mutanene,gashi kin cece............." "Kai Dallah yimin shiru marar hankali kawai,duk da dukan daka sha hankalin ka bai dawo ba koh?,kasake magana a wajennan in ban kirasu sun karisa ka ba yanzunnan" "Kai kuma (tafada tana nuna manjo wanda fuskarsa tayi buleliya koh magana bayayi),kasake karbar kudi ka kashe kai a dole ga mai son banza,kaga yamzu sai kulu tayi jinyarka koh?" Tana gama fadar hakan ta yiwa wasu gardawa guda biyu magana akan su kinkimi sule zuwa gidansu,yayinda wasu guda biyun kuma suka shiga da manjo shima gida,sai nishi yakeyi saboda tsamin jiki. Tsitt kakejin gidan babu hayaniyah saboda kofar kawu shehu innna karima ce kawai a ciki,abokiyar fadannata wato inna larai bata nan bare a jisu ,ita kuma inna ramatu har yanzu itama bata dawoba. Kofar kulu tah nuna musu akan su kaishi,dan bazata iya da kuma hayaniyar kulu ba a lokacin,idan ta huta koma menene sai ayi,dan dama an saba ba yaune farauba. Kwanciya tayi ta kashe wayoyinta saboda kar a dameta. Baccine yayi gaba da itah har sai wajen isha kafin ta tashi,domin shirin tafiya dinner da za'ayi na samun kujera da sukayi. Wanka kawai tayi dan babu batun sallah,kafin aka zo fara shiri,rigar da akayi domin zuwar ranar ta dauko mai masifar kyau,daidai ciff jikinta rigar ta kama,ita kanta saida ta juya tayi Murmushi a gaban madubin kafin ta zauna domin yin hira. Dadai misalin karfe tara ta gama shiri saiga kiran umaruje,dan dama cewa yace tayi masa izinin ya kaita wajen dinner,da har taki amincewa amma ganin yanda ya damu yasa tace babu komai. Toh kawai tace kafin ta fita tana tafiya a hankali saboda takalmin da ta saka mai tsayi. A bakin kofar shigowa ta hadu dasu sameerah zasu shigo,tun safe da suka fita sai yanzu suka dawo,kallon kallo sukeyi da sameemah ganin kayan alfarmar daya ke jikinta. KO ci kanku bata ceba ta nufi motar umaruje wanda yah ke tsaye a kofar gidan. Yana ganin tahowarta ya fito tareda bude mata kofa ta shige,shima ya koma ya ja motar suka bar wajen. Duk abinda yake faruwa akan idon su inna ramatu wanda suka fasa shiga cikin gidan suna kallon Ikon Allah. Sameerah ce ta hade fuska gameda dunkuke hannu tace, "Ummah kin Gabi koh,wallahi yau zan fara amfani da maganinnnan basai gobe ba,tunda boka yace matukar tashi tsaye mukayi ba toh abin sai ya fi karfinmu" Hall din da za'ayi dinner ya dau haske da kida ga dare kaman ba shiba. Sameemah suna shigowa aka dau ihu da tafi,ita kuwa dan Murmushi kawai tayi na gefen baki alamun ta ji dadin abinda sukayi mata. Wajen da aka tanada dan zaman ta ta nufa kafin salon kidan ya sauya. "Kai aboki dan Allah ganemin lady din can,gaskiya duk wanda ya sameta yah more,ga kyau ga kuma zarrah,kai da ganinta kaga zazzafar manyan mata wanda ake shiga taro dasu" "U hmm saidai ka gani daga nesa,ita cefah aka zo taron dan itah,sabuwar shugabar yan vigilantee ceh toh,kai ma daga gani kasan za'a sha dabi,mace da shugabancin yan kato da gora,ai abin Akwai show billahillazi" "Hmm Bari kawai,ni ina ga da gangan zanyi laifi dan akaini office din ta na dung a Ganinta kawai" "Saika DA ur a niyya,idan naga ta wanye lafiya dakai toh nima sai nayi,dan ba a shaidar mutum a fuska,tsaff sai ta baka mamaki ina fada maka" Hakadai abin yakasance kowa yana fadar albarkacin bakinsa,shikuwa umruje duk yanda yayi da sameemah tazo suyi rawa kin amincewa tayi,iyah yanka cake akayi aka danyi serving abinci kafin kowa yah kama hanyar sa. Watsewa akayi saura iyayen gayyar wato sameemah da tawagarta,direct gidan kungiya suka wuce za'a fara sabon shagali,dan dama ta ayyana a ranta ita da gida kuma sai gobe. Da daddare da kyar su sameerah sukayi bacci saboda tunanin mai zai faru,dan maganar boka na cewar indai har ba rabata akayi da maza ba toh bazasu taba auren miji mai maiko ba,hakan sukayi ta jiranta bata dawoba har sukayi bacci. Zainab ce ta shigo sauri tareda fadawa inna ramatu sameemah tana shigowa cikin gidan. Cikin gudu gudu sauri sauri suka gama abinda zasuyi kafin ta karaso. Shigowa tayi amma kayan dayake jikinta ba na jiya bane da alama tah sauya kaya,babu sallama bare bisimillah haka ta zefa kan ta dakinnasu,wani abune taji ya coki tsakar kanta har saida kanta yah sara lokaci guda,sannan idan bata manta ba tah taba jin irinsa lokacin da ummah tana da rai. Basarwa tayi tareda shigewa cikin dakin kawai,duk da kannata bai bar sarawa ba amma bata kawo komai a ranta ba sam. Uniform din aikinnata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55