Chapter 2
Chapter 2
yanda sukayi da alhaji Sama'ila,duk zancen dayakeyi bata kulashi ba saima umarni da ta bashi cikin karamar magana, "Ka saka su dodon dawa su kama Labiru dan malam sule,su kaimin shi gidan karangiya,su dan tabashi kafin naje wanjansa gobe" "Shugaba reza mai yayi haka?" "Bai shafeka ba kayi yanda nace kawai" "Wai yau labiru yaga ta kansa tabbbb" Da haka har suka isa gidan kungiyar tasu burgu bai sake cewa komai ba saboda yaga yanda shugabar ta murtuke fauska. Gidane da akayi wajen da langa langa saikuma,dakuna na bulo guda biyu da kuma dakuma dan tsakar gida. Babu KO sallama haka suka saka kai ,inda kowa yatashi yana yi mata barka da isowa,dakin dayake farko ta shiga,tareda hakimcewa akan wata kujera wadda aka saka tebur a gabanta,sukuma suka zauna a sauran kujerun dakin, "Uhm uhm,kaman yanda kuka sani wannan kungiya ta kafu bada iya taimakona ba harda naku,sannan muna abune bisa tsari,in munyi abu saida dalili toh dan haka,ba mason katsalandan da yan sanda,alhaji Sama'ila yaba mu aikin ragamar siyasarsa,dan haka zamuje yau ,amma iya mutum shidane zasu biyomu sauran nasaka burgu yabaku aiki,shi zai fadamuku mai na sakashi yasa ku aiwatar kuma kunsan banason ganganci,dan haka k kula,kai kuma ASUSU,(tafada tana nuna wani dan saurayi a gefen burgun a zaune),nawa muke dashi acikin bankinmu na kungiya?" "Eh shugaba iyah dubu talatinne" "Toh kabawa dodon dawa dubu goma yah,yasayo mana suyar kaji da lemo,sannan kuma ka tambayi burgu inda ake saida dulah mai caji ka sayo mana,dan wacce ka kawo wancan sati ta asarar kudi ce kawai,inna dawo daga wajen alhaji Sama'ila akwai shagali" Ihu wajen kowa yadauka mai feduwa sunayi, "Sai ogah kina abinda kika so,sai shugabar gidan gandu,da girman kujerarki,sai reza ki yanki wanda yasayeki idan ya kuskuren rikeki ba dadaiba,kuma dole ya gyara yayi aiki da ke,ehhhhhhooooool" "Toh ya isa haka maza ayi haramar fita aiki kuma" Kowa tashi yayi inda masu kamo labiru suka tafi bayan burgu yayi musu bayani,sannan masubin shugaba seemah jar wuyah kuma suka bita a baya da mashinan su,sai gidan alhaji Sama'ila. Toh farkon farawa kenan a cikin littafin gidan gandu,daga taskar sady-sakhna,kuci gaba da bibiyar littafin da sannu zamu nishadantar daku yanda yakamata inshaallah,nagoda ga duk daukacin masoyan wannan littafin. ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤02❤ Labirune a zaune shida abokansa suna shan rake a baki rafi,kai kace ba abinda ya aikata hankalinsa kwance kaman tsumma a cikin randa,yana cikin zance sai waigawa kawai yayi yaga bakowa a gefensa kamar dama ba zaune suke shida mutane ba,tun kafin yayi magana yaji an toshe masa baki,yayinda wani duka ya jiyarci keyar sa ta baya,daga nan bai sake jin komai ba sai duhi daya lullube ganin sa. Sun gumarsa sukayi suka sabashi a bayan mashin din daya daga cikinsu sai gidan karangiya. Zefashi sukayi a kasa kaman kayan wanki yayinda daya daga cikinsu yace, "Kai baaaba yanzun zamu dabashi kaman yanda shugaba reza tace kokuma kawai mubarshi ta ji dashi" "Haha nayi dakon kawoshi a banza wallahi saina dan tabashi,dama inajin haushinsa sani ne bakayi ba,shine fah wanda yayi shunemu a wajen yan sanda lokacin da muka sato akuyar hajiya delu zamu babbake mu maida maiko,kasani ai dakyar muka sha,badan shugaba jar wuyah tananan ba da tuni sun tara mana jini da majina" "Gaskiyarka arnan mazaje,dole mudan mauleshi koh kadanne,dan babu abinda na tsana kaman masu bakaken kayannan(yan sanda) yan banza saikaace cinnaku" Dariyar yan daba suka sa baki dayansu kafin daya daga cikinsu yasamu daidai duwawun labiru ya narka masa sandar hannunsa,wani wawiyar zabura yayi ya mike yana rarraba ido akan kowane dayansu. Daya daga cikonsu ne wanda shine ya daki labirun da alama shine shugaba idon sa ya dau kwalli kaman tsohon dan farauta, "Heeege gama karemu da kallo yau uwarka zaka ci a wajennan dan ma bamusan mai kayi ba,amma tunda ka tabo shugaba yau kataryarka sai tayi jawur a wajen mu" Yana gama magana ya hau tabkar labiru kaman an aikoshi wajensa. Saida sukayi masa lilis kafin suka barshi yashe a wajen tareda rufo kofar suka bar wajen. Basu wane dade su sameemah suna tafiya a hanyaba suka iso gidan alhaji Sama'ila,gidane sannane kowa yasanshi saboda siyasarshi,a bakin kofar get din gidan suka yi parking din mashinansu kafin suka tunkari mai gadin wanda yake zaune akan benci yana jin radio,burgune yafara masa magana cikin gadara, "Kai dattijo maza shiga gidan ka sanar da mai gidan isowar mu" Bai ce komai ba sai tashi da yayi ya shiga gidan dan aiwatar da abinda suka sakashi saboda tsira da mutuncinsa,bai dade da shiga kuwa ba saigashi yafito, "Eh na Shaida masa isowarku yace kushiga daga ciki" "Shikenan dattijo godiya muke" A parlorn baki suka sameshi ya baje akan kujera tareda ware cinyoyi yana shan iska,saboda kibar da yayi irin ta yan siyasa,washe bakin nan yayi yana musu barka da zuwa. Sameemah ceh ta kalleshi tana yatsine fuska bayan ta zauna akan kujerar daya daga cin parlorn,dora kafa daya kan daya tayi kafin tace, "Kafin a fara komai alhaji hada wannan cinyoyinnaka waje daya tukunna,dan banji dadin zama ba da ganin yanda ka wani ware kafafu kaman mai jiran kaciya ta biyu" Cikin kunya da kuma dariya irin ta yan duniya ya hade kafafunsa waje daya amma da gani baiji dadin yanda sameemah ta disga shiba a gaban yaranta,saidai babu yanda zaiyi tunda shiyake nema a wajensu. Maganar abinda yatarasu suka farayi gameda campaign daya ke so suyi masa na mutane,Musamman matasa na birni da kauye,sameemah ceh tayi saurin katseshi tareda cewa, "Dakata harda kauye kakeson muyi maka ko iya cikin gari,sannan kanason mukula da ta bangaren yan sanda ko kuma ba ruwanmu dasu?" "Eh kowanne nakeso ayi nidai kawai na samu na hau zabennan shikenan burina yacika" "Toh sharadinka shine;zaka bada rabin kudi yanzu sauran rabi kuma saika hau zabe,amma idan ka hau zabe ka manta da mu,toh kasani sanda ka sauka a mulki saidai kanemi wani garin ba dai nan ba,dan bana barin bashi ko ranka zaka sayar saika biyani kudina bai dameni ba,sannan idan wani yarona ya shiga hannun hukuma kai ke da alhakin fito dashi ,idan ka yarda da sharruda na,kayiwa burgu magana zai kawo maka takardar saka hannu" Gilas ta fitar daga jin jakarta ta toshe fuskarta kana ta mike tsaye har ta juya zata fita can kuma ta dawo, "Am karka manta,inada lawyer wanda ba'a siyansa da kudi,karkayi kokarin wani kuskure,dan ni ba irin sauran yan dabar bane,ku tashi mutafi yara" Kowa mikewa yayi kaman dama umarninta suke jira,sun zo dadai kofar fitane suka hadu da wani gogygyen dan siyasa da alama yafi alhaji Sama'ila ma matsayi a siyasar. Tsayawa yayi kaman wani gunki ya tsare sameemah da ido wanda ta bashi hanya tun dazu ya wuce,ganin shiru kaman bashida alamar wucewa ne yasata dagowa dan ganin mai yake kallo haka,wani dan isakan kashe mata ido yayi tareda lashe baki irin na yan duniyar nan,dayake itama shugaba ce a wajen cikin sakanni ta gano mai yake nufi,take kuwa ta mayar masa da martani ta hanyar daga masa girarta ta hagun, "Kibani numberki idan bazaki damu ba mana" Ba wani bata lokaci tafara karanto masa yaronsa yana copy akan wayar datake hannunsa,saida suka gama yace,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55