Chapter 21
Chapter 21
ya biyo bayan yah sameer saboda su inna ramatu idan basu kulada rsyuwata ba banu komai saboda ni ba dolensu bace,amma yah sameer shi aka bawa alhakin kulawa dani,kobai min komai ba a kallah ya tambayi wane hali nake,amma babu ruwansa saima wata masifa daya dauki yi kaman wani shine uban mutane, "Duk abinda kika ga dama ma kiyi tayi,kowa a gidan zancen rashin muncinki yakeyi dama ummah ce take daure miki gindi gashi yanzu babu itah" Katseshi nayi da masifar dayakeyi kafin nace, "Uhm akwai abinda zanyi idan ka fadi metasa ka kirani" "Dama ba kiranki nayi na dunga kallonki ba inason na fadamiki gobe zan bar garinnan da asuba zan tafi aikin soja,ogah soja na anguwarnan ya min hanya,saiki fadamin mai kike bukata" Kallonsa nayi kawai na ya rainamin hankali dan yaga ni yarinya ce ,banda haka yaushe rabon dan ganshi sai yanzu zai cemin wai me nake bukata? "Babu abinda nake bukata ni,saboda duk abinda nake bukata,ina yiwa kaina dan haka kaje allah yah bada sa'a,idan shikenan nizan tafi cikin gida" "Eh shikenan dama dan karkiji na tafine baki saniba kice ban fadamiki ba," KO magana ban sake yi masaba na bar wajen saboda wani abin bakin ciki daya tasomin dan takaicin halin yayannawa na rashin kulawa. Dakinmu na shiga da sauri ,ina shiga kuwa na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya,saboda duk abinda yakemin ma na halin koh inkula,koba komai in ina ganinsa ko ina tuna cewa yana cikin gidan hakan kan karamin sanyi a zuciyahta,musamman kama da yakeyi da ummah kaman an tsaga kara,irin kyau na anihin fulanin asali,naso ace nima na iyota saboda na dunga kallon fuskata a madubi duk lokacin dana yi kewarta,saidai yanzu shima zai tafi yah barni a cikin wannan halin na kunci ni kadai,wanda kullum cikin kalubalen rayuwa nake. Saida nayi kukana na koshi kafin na fito daga dakin,ina mitstsika ido. Yah sameer kuwa kaman yanda ya mafadamin da asubar yabar garin yah nufi jahar porthacourt,domin cikar burinsa dayayi niyyar cikawa,nima kudira nayi a raina saina cika nawa burin na tafiyah babban gari aiki nemam kudi,wanda zamubi irin manyan motocinnan da suke wucewa idan sanyi yazo. Haka rayuwar take ta garamin da dadi da babu dadi,har muka fara shiga sanyi sannan an gama duk aikin gona,shiri mukryi sosai da wasu tsofaffi wanda suma dasu zamu tafi,inyaso idan lokacin aikin can yakare saimu dawo,dama suna zuwa duk shekara nice dai sai wannan shekarar zan fara zuwa,zancen makaranta kuwa dama ba zuwa nakeyi ba tun daga mutuwar ummah na daina zuwa dama itah ce take korani zuwa makarantar ba a son raina nake zuwaba,dan haka koh hanyar makarantar bana zuwa,idan kanason rawar jikina toh aikin kudine zanyi a biyani toh zakaga aiki har sai ka kama baki. Tun kafin saura sati dayah da tafiyar nake ta shiri kaman ance zamje makkah,nayi wanki da sabulun dana siyo duk da ma kayan sun tsufah kyakykyawan mutstsika su kayi saidai kaga garinsu a cikin hannunka. Shagon dan anguwarmu naje na sayi garin kwaki rabin kwano dakuma k'arago a wajen a wajen masu tallah,a takaicedai na hada kayana kiciff saboda tafiyah. Acikin akwatin ummah na karfe na jera kayana a ciki ina kuka ina komai haka na dauko kayan na fito daga dakin,wanda bantaba tunanin zan barshi a kwana kusaba,kkda na kwana dayane bare na watanni. Dakin inna ramatu na shiga suna zaune ita da baba umarun,tsugunnawa nayi daga gefe tareda gaisheshi,maganar sa ta farkoce tah batamin rai sosai, "Ahh sameemah dama kina nan yaushe rabon dana ganki a cikin gidan,yanzun wani abune yah faru ?" Daga masa kai kawai nayi tareda cewa, "Eh dama inaso zanbi su iyar shehune aikin gona zuwa cikin babban gari" Shiru yayi yana tunanin maganar tawa,har zai ce wani abu inna ramatu tai caraff tace, "Ahh Toh ai dakyau kije allah yah tura keyah" "Ahah ramatu hakan bayyiba tafiyah mace neman kudi hakanma har wani garin?" "Ahh ba ita tace zatajeba ina ba kai ka tursasa mata ba,ai babu alhakinka koda wani abune yah faru,taje kawai allah yah tsare hanaya" Daga kai kawai yayi alamar yah ji,nikuwa koh na jira yace wanj abu na kama hanyata na fita a cikin gidan,koh sauran kofofin ban shigaba nayi musu sallama,shima abinda yasa na fada masa dan yah amsa sunan uba ne,badan hakaba saidai yaji labarin tafiyata,dan hakan kamar halin gidannamune in kaga da hanya kawai saidai aji baka nan kayi wata hanyar. ** *tan uwa mukula musamman ma mata,saboda daga majority matan mu na yanzu daga an saki kishiyarki koh kuma ta rasu sai yah zamana duk wani aiki su za'a dinga sakawa ko kuma shikenan sun daina zuwa makaranta saboda dama uwarsu ce take kokarin rakasu makarantar*. *abinda matanmu basu saniba shine idan yaron yayi karatum watakil ke zai fara amfana saboda ke yatashi yagani ba uwar tasaba,mu kula dan Allah,d'a na kowane idan da hangen nesa*. *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤15❤ Lokacin danaje gidan su iyar shehun ban samesuba sai sallahu suka bari akan na bisu da sauri sun tafi neman motar dazasu hau,akwatina na dora a kaina na yanki hanya ina ta gudu burina karsu bacemin bangansuba,ina haki ina komai kaman raina zai fita amma ban dakata da gudunba saida na fara alamaun ganin bakin hanyar dasuka ce na samesu tukun. A jiye kayana nayi a gefe,lokacin dana isa. Bamu muka samu wata motar ta daukemu ba har wajen karfe 8:00am na dare,saboda lokacinne suke wucewa mu kuma said mu sauka a bakin garin su kuma su wuce garin dazasu je. Hawa mukayi dukkanmu kowa da kayamsa,nikam samun waje nayi na kwanta tareda yin filo da kayana saboda gudun sata,su kuwa kowa yana bayanin idan an sauka,mai zai farayi,masu lissafin wajen da zasu sauka daban haka masu lissafin irin aikin kudin dazsuyi daban kafin lokacin yah kare mudawo. Na dade ina bacci saboda lokacin dana tashi duhu yah lullube sararin samaniyah ga kuma duhu hazo da kuma azababben sanyi dayake hurawa kaman an saka mutum a cikin fridge. Kallon sauran mutanen bayan bodin motar nayi ,suma duk sun takure a wajen daya kaman sardines,hmm neman kudi da wuyah na fada a raina. Karar salatin da mai motar yah fara yine yah dawo dani daga duniyar tunanin dana tafi,inda kowa a cikin motar shima yah tashi zaune dan jin mai suka gani,hantar cikin mune da duri ruwa tun kafin mu san abinda yake faruwa,tsofin cikin said salati sukeyi wanda suk da banyi karatuba kuma banason yi nasan ba dadai suke fadaba. Wani daga cikin yaran dirabannne ya leko ta gefen glass din gaban motar yake cewa, "Toh jama'a saidai fah kowa yayi ta kansa saboda,yan fashine a gabanmu kadan" Iyar shehu ce tayi saurin cewa, "Yan fashion kuma,a wannan hanyar amma bamu taba jin labarin yam fashi a hanyar nan ba duk wushewar mu" "Hakane I yah muma bamu taba gamuwa dasuba gaskiya akwai abinda yake faruwa,gashi babu damar mukoma da baya ,domin suna dauke da bindigogi a hannunsu kuma basuyi kama da kananan yan fashi ba" Duk abinda suke fada ina jinsu,saidai bana gane mai suke hasasowa saboda ni ban taba ganin yan fashinba sai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55