Chapter 35
Chapter 35
farin cikin idon ya koma jawur kaman garwashin wuta,saida ta cije bakinta har fatar bakinta tana fashewa saboda bakin cikin dayake cikin ranta kafin tace, "Sameeeeeer! Sameeeeer!! Sameeeeer!!! Idan har kanaso ka cigaba da tunanina a matsayin kanwarka da kake da ita guda daya cikin kaunar rai toh kadaina shiga rayuwata ,bare har hannunka yasake taba fuskata,kayi na farko dazu yanzu kayi na biyu toh karka sake na uku,saboda hukuncin dazai biyo baya bazai yiwa kaff yan gidan gandu dadiba,har ummah da take makwancinta bazata yafemin ba. Dan haka tun ina iyah rike kaina duk da hakan yana cutar dani toh karka kara,kaci albarkacin umma dan haka karka sake shiga sabgata na fada maka,ka dauki matarka ku tafi kuna cikin koshin lafiya. Wannan gargadine idan kaji da kyau idan kuma ba haka ba .....................hmmmmmm" Dunkule hannunta tayi jikinta har rawa yakeyi ta shige cikin gidan ta barshi a wajen yana wasiwasin abinda tayi. Gogar kuwa tana zuwa ruwa ta diba tafara tuttulawa a cikin bakin ta tana jijjiga kai,saida ta gama ta fada kam gado tana ritse ido da karfi,dahaka can wani lokaci bacci ya dauketa mai nauyi sosai. ............kallonta take a wata duniya daban mai duhu,sadai daga ganin idonta dama tah saba zuwa wajen ba yau ne na farko ba,kayan jikinta ta kallah jawur da su ,saida ta daga ido taga suma wanda suke wajen haka kayansu yake,saidai itah nata anyi masa hoton wani katon tattoo a tsakiyar rigar irin na jikin kayan shugaban dayake kan kujerar, "Koyaushe cikin saba doka kike,babu wani ruhi daga cikin mu dayake saba doka saike,kuma kedai ce a tarinhimu kike saba dokar shugaba amma yake kyaleki dan haka ki shiga hankalinki" "Idan naki fah ,wai me hadina daku ne wai,akan uban me zan dunga bin umarnin naku,shidin yayanane kufurinku shine kusakani kashe duk wanda ya bata min rai ciki harda ahalina,to kun makara dan yanzu na koyi control din hankalina ba kaman shekarun baya na lokacin ina Brazil,sannan ai bance ina cikinku ba ai" Tana gama fadin hakan ta kama rigar da take jikinta da karfi ta cireta,aikuwa cikin kankanin lokaci hankalinta yah koma iyah cikin bacci kawai,da haka baccin gaske ya dauketa bayan ta bar wajennasu. Kwana sameer yayi yana tunanin yamda sameemah tayi masa magana,abin haushi ya bashi ganin yamda take taka kowa san ranta. Tun kafin kowa ya tashi saleemah ta tashi ta gyara danta saboda tafiyah,dan itah gidan ya isheta musamman sameemah da tsoronta takeyi yanzu tun sanda akayi dramar mota a gabanta,kuma ta dau kudurin babu ita ba garin zariyah har abada,musamman wannan yankin nasu da babu komai sai yan daba,ta tashi a cikin sojoji amma bata tashi a cikin mutanen da babu wanda yake ganin mutuncin na gaba dashi ba. Shima sameer bayan yah karyah fitowa yayi suka gama sallama da mutanen gidan ya kama hanya. Gogar kuwa sai wajen bayan azahar kafin ta tashi tana mutstsika ido,hada ido sukayi da karen ta bingo yana saki baki,hannu ta mika masa yazo yana shanshanata, "Oh Baku ci abinci bane,bari na tashi dama akwai wajenda zanje na manta kwatakawata" Sakkowa tayi ta fito daga dakin tana hamma da kuma mika,da baba umaru suka hadu a tsakar gidan yah dawo daga gona,kallonta yayi tareda jijjiga kai,koh gaisheshi batayi ba kuwa tayi hanyar bandaki,dan dama idan ba yan muyuncinne suke kusa ba koh gaisuwa bata hadasu da yan gidan, "Ke sameemah ni kun yi sallama da yayannaki ne?" "Ahah " "Ya tafifa dazu da hantsi kuma bakuyi sallmaa ba" "Sallama kuma,saikace wasu yara,yafi masa ma dan wallahi daya ga yanda ake iyah shege,kuma hankalinku yah kwanta" "Tabbbdi lallai yarinyar nan,yanzu dan uwannaki kiyi shekara da shekaru baki ganshi ba saida ya tafi bakuyi sallama na kike cewa yafi hakan" "Baba bazaka ganeba ne a bar zancen kawai" Shiryawa tayi cikin atamfa anyi mata dinki simple na doguwar riga,sai daurin ture ka ga tsiya da kuma gyalen rigar a kafadarta,tayi kyau sosai dan ba karamar kyakykyawa bace (kyan dan macijiba)kuma tafi saka abaya,ko kuma riga da wando,haka in bata ga dama ba sai tayi sati bata daura dan kwaliba sai gyara gashi kawai takeyi ta daureshi. Hanyar waje tayi su bingo suna biye da itah a baya,kicibis sukayi da manjo yana shigowa,yah saka wata babbar riga wanda takusa ta yadi goma,a ina ya samota oho,dan dama manjo ba dai shigar hauka ba,taba ce a hannunsa tana hayaki ga kuma wani kwalli dayasha kaman dan farauta, "Yawwa ke dama ina nemanki zamuyi wata magana" "Wacce maganar ka bari saina dawo akwai wani abu dazanyi manage yanzu" "Ke ni zakice zakiyi wani mange(manage),maganar muhimmancin nima nake tafe da itah" Har zatayi magana saikuma ta gyara tsayuwa tareda cewa, "Ina jinka manene" "Ehe yawwa zancen soyayyarki keda sule maye,inaga maganar zatayi karfi tunda ni yayanki nashiga ciki,yanzu hak nace yabani sadakinki dubu talatin,kuma yabani duk da ma na dan ci dubu biyar a ciki,kinsan sha'anin rike kudi abinka da mutum mai dan uzuri,hhhhhhh amma tunda naga yana sonki sosai nasan zai karo cikaton kudin. Kai dole ma ya ce yanason ki duk da irin tantirancin da kikeyi ,akwai kyau ne musamman idan kikidau wanka" "Toh yanzu dai kagama magana mai muhimmancin ko kuma da saura har yanzu kai" "Ke kina rainani fah,dama sanda na dawo kulu tacemin kin mata rashin kunya kyaleki kawai nayi saboda sule abokina yana sonki" "Allah koh,haka akayi kenan,duk zancennan ka barsu idan na dawo sai muyi shi" Jijjiga kai kawai tayi tana Murmushin mugunta ta shiga mota suka tafi itada karnukannata. Wajen da ta ajiye surayyah ta tafi domin jin yanda ta kaya,yauma a zaune take saidai dayake su mugun dawa sun tafi aiki daga itah sai C.I.D shikuma bashida magana sai leken asiri koh bera ya sara masa. Sameemah tana shigowa surayyah ta tashi tana gaisheta duk da a gida koh uwarta sai taga dama take gaisheta. C.I.D ne ya matso tareda yimata bayanin abinda yah faru dazu,mika mata wata takarda yayi yana cewa, "Ranki ya dade ga wannan paper burgune ya kawota dazu wai yayan surayyah ne yabayar,yayi signing din yaan neman a sake masa kanwarsa,tun dazu muje jira ki iso gashi kin ce kar wanda yakiraki shiyasa na zauna ko zaki zo" "Okay shikenan babu matsala,zaku iyah maida ta gida,amma ban yadda tasan wane waje take ba,na gama da wannan shafin" Saida ta gama kallon signing din ta tabbatar shine kafin ta rufe paper cike da murnar nasarar da ta samu. "Amma shugaba nafadamiki cewa nima fah a nan wajen zan zauna" "Eh kuma nima na fadamiki idan baki kawo signing din yan uwankiba bazan daukeki ba ai,koh kin mantane?" Sunkuyar da kai surayyah tayi cike da jin haushi saidai ta kudiri aniyar karbo izini dan itah taga wajen zama inda yayi dadai da ra'ayinta. Wani bakin kyalle aka saka mata a idonta har sannan sai cuna baki takeyi wai sameemah bata yadda da itah ba,ita kuwa ko kallonta batayiba har su ka isa kofar gidan yayannata a mota,C.I.D yah fito ya budemata kyallen fuskarta da kuma motar kafin ta fito,cikin gidan yayannata ta shige koh kallon sameemah batayiba. Suna ganin shigewarta gidan suka bar wajen. Mahmoud ne a zaune shida matarsa haka ma iyayennasa suna zaune a daya kujerar kowa yayi jugum sun rasa ma me
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55