Chapter 29
Chapter 29
fiye musu,bari kawai a dan buga wasan kafin yah kare ......................muje zuwa😀😀😀😀😀😀 *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤20❤ Tun daga bakin kofar prison din nake yah mutsa fuska ganin yanda wajen yake duk babu tsari ko kadan,wani daki aka kaini wai shine na mata,babu kowa a ciki sai wasu mata tula tula guda biyu a gefe suna zaune da kayan prison din a jikinsu. KO magana banyi musu ba na kade wani waje na zauna ina kallon wani gefen daban,muryar dayar naji tana min magana cikin wata hausarta da duk yare ya gauraya da itah. 'Ke baki ganin mutanene da bazaki kulasu ba" "Toh miye saina kulaku,tare mukazo daku,ko kuma zamanku nakeyi a wajen" Dayar ce ta matso tana wani hura kirji itah ga yar iska,nima gyara zamana nayi domin naji mai zata ce,cikin rashin sani naji ta kamani da kokuwa mun dungura kasa,matsawa tayi tana huci itah a dole ga karamar yar iska. Da farko takaici abin yabani ganin yanda tah batamin kayana da datti,dagowa nayi ina kallonta dadai da isowar wani ma'aikacin tsaro wajen,kallona yakeyi tareda dariyah yana cewa, "Bake yar iska ba hada marin ASP,yanzu zaki fadawa yan garinku a cikin wannan masifaffun matan,dama ba'a saka kowa a cikinsu,saboda karyah mutane sukeyi,yanzu zamuga bakin rashin kunyarki yarinya" Haushi maganar tasa ta bani,kafin nace masa, Kana nufin kenan koh karyani sukayi babu wanda zai dau mataki?" "Kwarai kuwa" Murmushin jin dadi nayi kafin nace, "hakan babu matsala ,bari a fara buga wasan" Tun kafin na gama magana na dauki buleliyar cikinsu na duma tah da kasa,dimmmm saida cell din yah Amanda wani vibrate,koh motsi batayi ba sai wani nishi da tayi na wahala,nufar dayar itah ma nayi fuskata dauke da wani evil murmushi,ihu ta fara tana neman taimako,wanda shima ganin abinda yah faru kaman yah daskare haka yayi shiru. Labari ne yaje kunnen DPO,inda aka kiramu nida su,tsura mana ido yayi da alamar neman karin bayani. Cikin sauri kuwa suka zayyane masa,hadda cewa wai ni ce na fara bugata da sumunti,nidai bance komai ba har naji DPO yana cewa a kaini cell din maza,kallonsa suke da mamaki,jin ina mace yace a kaini cell din maza,sannan laifinna ya nunku zuwa shekara guda ciff. Jana sukayi muka nufi wajen mazan har sannan ko kala banceba. Wajen mazan yafi girma sosai saboda suna da yawa a wajen,ni hakanma yafimin saboda ba fiye son zama da mata nake ba,sun faye rainin hankali. Cikin sati biyu muka saba dasu,saboda duk abinda suke tsoron yi ninake aikatawa,zuwa lokacin hausata ta fara dawowa normal saboda yanda nakeyinta akai akai. Masu shaye shayen cikinsu kuwa in sujjada nace sumin zasuyi,saboda dare nake bi na tsallaka fence cikin sauki (saboda training danayi a Brazil),na sayo musu a cikin gari,yan iska kuwa harka ta bude saboda sun samu jagorancina,kullum dare za'a raba ana hira kafin kowa yah tafi yah kwanta,daki daban na ware nace musu nawane,babu musu kuwa suka barmin shi,wasu yan kusan yankinmu na hadu dasu a wajen,suke bani labarin yanda garinmu yasanja,suma an kamasune bayan sunyi laifi a garin abuja. Mikewa nayi da sauri,kkwa saida yah kalleni dan ganin mai yah ke faruwa,hade fuska nayi babu alamar wasa nace, "Wayake son yabini garinmu?" Kusan mutane ashirinne suka daga hannu,ina ganin haka nace, "Shikenan an gama ,gobe zamu kama hanyar tafiyah da safe bayan an sallamemu,dan tunda naji labarin gida toh nafasa karisa wata goman,tafiyah zanyi kawai" Kallona suke da mamaki,musamman yanda na hade rai sun san da gaske nake,tsallakesu nayi na wuce,har nayi nisa na juyo na kallesu, "Kowa yah me yah kwanta kafin gone mu tafi,zanje wani waje sai na dawo" Ina fita ta fence ban same KO ina ba sai gidan DPO,dayake police quarter da wuta,haske ya garwaye ko ina,wata sanda na fara cikin kwarewa kamar mage na shiga cikin gidan. A falo na tsaya babu kowa a wajen amma ina jin hayaniyarsu shida matarsa a cikin daki,wasu kuloli na gani a akan dining table,ai kuwa idona yayimin tozali da wasu kaji a ciki sun sha farfesu,zama nayi na fara ci hankali kwance kaman ina cikin gidanmu. Ban kai ga cinyewa ba DPO yah fito daga cin shida matarsa suna min kallon mamaki,nuna ni yakeyi da yatsa yana kokarin fito da waya a aljihunsa,dagatar dashi nayi tah hanyar daukar wuka na yanka hannuna na hagun, Jikinsa ne yah fara karkarwa ganin yanda wajen yake komawa yanda yake,komawa nayi na zauna bayan na maida wukar inda take, "Karka daga hankali nka ka dagawa matarka ma,naga kaman kudin sabin aurene,koda ka kira wannan karnikannaka (yan sanda) babu abinda zasuyimin,dan haka ka saurareni da kyau,..........inaso gobe idan kaje aiki,abinda zaka farayi shine bugamin takardar sallama nida yarana guda goma,idan kuma ka barshi sai gobe,toh wallahi daga kai har matarka a duk fadin Nigeria banga mai hanani juya rayuwarku zuwa yanda bakwa tsammaniba,hmmmmmm kai karma kayi mana" "Zanyi wallahi zanyi,ni daman daga ganinki nasan ba mutum bace ke" "Nidai na fadamaka"har na fita daga gidan na dawo nace wa matar tasa, "Abincin ki yayi dadi sosai,kiyi hakuri na raguza miki miji,nagode sosai" Da safe kuwa tun kafin na karya saiga yan sanda guda biyu sunzo kirana,tashi nayi na bisu muka tafi office din. Tun daga shigowa ta da muka hada ido da DPO,yah dauke fuskarsa da sauri,nima bance komai ba har yah mikomin takarda ta,sunayen dana bashine su "burgu"naga an buga tasu sallamr ma. A ranar bamu kwana ba a garin abuja sai garinmu kuma gidan mu wato "GIDAN GANDU". Tun daga shigowata garin nake ganin sanji da dama,saboda tsawon shekarata goma bana garin sai gashi na dawo. Da wata yarinya muka fara haduwa a bakin kofah,bansanta ba amma daga gani yar gidan inna larai ce saboda yanda suke kama sosai,itam kallona take da mamaki kafin ta ruga kofarsu da sauri,mutanen gidanne suka fara fitowa ciki harda inna ramatu,wanda ta dan fara manyanta saboda shekaru. "Kuttt sameemah dama kina raye baki mutuba?". "Ga shi kuwa kin ganni,inso kike na mutu sai ki kasheni yanzu ma lokaci ai bai kuremikiba" Kowa shiru yayi yana bina da mamaki,gashi na wuce duka bare su dakeni su huce,dakin mahaifiyata na tafi wanda nasan shine yan matan gidan suke,matsar da kayan wata nayi a wajen danaga yafimin kafin na ajiye jakata a wajen. Tunda nafita bani na dawoba sai dare dauke da kayan amfani,wanda na siyo da kudina,su burgune suka shigomin dasu dayake shima dan garinne,biyar ne a cikinsu ba yan garinmu ba kawai. Sannu a sannu na fara kafa kungiyata harda su iliyah wanda suma suka zama yan iskan kansu,mika wuyah sukayi ga kungiyata saboda basu manta ceton rayuwarsu danayi ba shekara goma da suka wuce,hakanne yasa yan kungiyata suke bani daraja,saboda babu wanda na jawoshi da kudi saidai sadaukarwar daanyi masa ko kuma wani taimako. **** ****** *****"" DAWOWA CIKIN LABARI. Kowa tsayawa yayi yana kallon sameemah,ciki harda wanda yawu yah bushe a bakinsa saboda mamaki. Ta shi sameemah tayi daga kan kujerar da take tana kade rigarta, "Toh yanzu kunji labarina,kuma saura naji zancen a bakin wani,ban yadda wani ya fitar zancennanba,sannan munyi magana da alhaji labiru zan hau kan kujerar shigabar vigilantee ta garinnan,dukkanku za'a debeku aiki,kuma banason
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55