Chapter 27
Chapter 27
da tunanin ta dan yanzu banason saka wani abu a raina har ya dameni. Maida himma nayi akan aikinmu ba dare ba rana,dan yanzu nice nake kulada da kowanne shiga da fita,saboda ogah Binlad shida Samad sun tafi kasar Brazil,binciken wani sirri,yanayin yanda abun yake tafiyha har yafi in ogah yananan,saboda sun fi tsorona fiye dashi yamzu,dan kowa yasan halina idan yah aikata abinda banceba. Ina cikin bincikene na gano wani aiki a gidan sarkin malamai,saboda yanada kudi sosai,sannan duk wani kudi a gidansa yake tarawa. Shirye shirye muke ba kama hannun yaro,kullum muna cikin binciken yanda zamu aiwatar da shirin. Tun da yamma,na zabi wanda zasu bini da kuma wanda zasu kulada gida kafin mudawo,babu wanda yayi magana bare musun abinda nace,bindigoginmu muka cika da bullet,duhu yana farawa muka shiga motocinmu sai cikin gari,a bayan gidan muka tsaya muna ganin shige da ficen gidan,wasu motocine suka,fara shigowa zasu kai wajen bakwai,har wajen karfe sha daya amma babu motar da ta fito hakan yasa na bada umarnin mushiga kawai. Wani daga cikin yaranne yace, "Amma ogah seemah akwai fah mutane a ciki" "Nasani ai ko makahuwa ce ni,ubanme mutanen zasuyi mana,idan tsoro kake ka zauna acikin mota,banza lusari kawai,idan kuma suka fito da kudin suka tafi fah,mu mai zamu samu" "Afuwa Ranki ya Dade" "Dallah yimin shiru,ku mazaje maza a kafta" Cikin sanda muka fara dosar gudan,har muka shiga babu wanda yah kulada mu,cikin gidan babu kowa sai haske daya gauraye gidan,ina biye suna bina a baya har muka haura stairs din benin,acan wani daki karshen corridor muka jiyo maganar mutane,da alama suna cikin dakin kenan. Alama nayiwa na baya su tsaya kafin nayiwa nagefena su biyoni,a bakin kofar muka tsaya sai kuma muka banka kofar da sauri. Falone mai girman gaske an jereshi da kujeru,manyan malamaine a zaune amma shigarmu kowanne ya tashi ya tsaya yana kikkifta ido,jerin malam na bi da kallo inda idona yasauka akan mu'allim,"dank'ari" nace a raina. Daga bindigar nayi sama kafin nace wa yaran, "Maza Ku bincikemin sako da lungu na dakinnan,karku bar ko ina" "Angama ranki yah dade" Zagawa nayi ina kallon malaman wajen,tsawa na daka musu cikin sauri suka zube a kasa suna karkarwa,tafiyah nake saida nazo saitin mu'allim kafin na tsaya,sunansa na kira inda yah dago da mamaki da alama yasan muryar,dadai lokacin yarana suka dawo da cewar basuga komai ba,. Cire hular fuskata nayi ina kallon mu'allim din da shima kallona yake da Mamakin. "Kayi mamaki koh,nicedai sameemah,wannan itace hanyar danake kai ba wacce kake kokarin dorani ba,inayine saboda tsoronka badan ina so ba,tunda kai ka sanni inaso ka fadawa shugabanku yabani kudi na tafi bana bukatar taba kowa a nan wajen,idan kuma ba hakaba,karkayi tunanin,zaka iyah kallon wannan sameemar" Tun kafin mu'allim yayi magana na nuna masa yayi shiru saboda ina kallon sanda shugaban yah mikawa yarona kudin ta gefen idona. Tsayawa nayi a gabansa,bayan ya mika kudin nace, "Mu zamu tafi saika musu bayanin irin kodar yaran daka siyar kafin ka samu wannan kudin,saboda su sanjaka da wuri kafin lokaci yah kuremusu,muma kuma su daina zargin mun sace kudin marayu kamar yanda ka fadamusu" Ina gama fadamasa na tunkuda keyarsa da karshen bindigata zuwa gaban sauran malaman nayi gaba. Sai wajen karfe biyun dare 2:00am,muka koma sansanin mu. Ogah binlad nasamu a kan kujerarsa a zaune har sannan bai kwanta ba yana jiran isowa ta,kallona yayi da alamar tuhuma na fitar aikin danayi bayanan. Nima banyi masa magana ba sai mika masa jakar kudin danayi,karba yayi yana zugewa dan ganin menene a ciki, Dagowa yayi da alamar neman karin bayani,nima shiru nayi banyi magana ba ,dannaga alamar da miskilanci yadawo, "Baki fadamin wane aiki kukayi aka samu wannan kudin ba" "Toh ogah kaima baka tambayeni ba ai" "Hmm kina nan da rashin mutuncinki toh yanzu na tambaya" Labarin inda muka samu kudin na bashi tun daga farko har karshe,jijjiga kai yayi tareda mikamin alamar jinjina da hannunsa, "Yayi kyau gobe akwai maganar dazamuyi daku,akwai wanda za'a zaba zasu je Brazil wani aiki,amma sai gobe tukunna,kowa tafiyah yayi ya kwanta,kafin muji mai ogah yake tafe dashi bayan tafiyar tasu. *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤19❤ Tunda safe ogah Binlad yah taramu domin yanda lavarin yake cinsa kaman arai. Faraway yayi da cewa, "Yawwa kaman yanda kukaji nace akwai wani abu,nasan kunga munyi tafiyha nida Samad zuwa kasar Brazil mun hadu da wasu yan uwanmu na can,suke fadamin akwai training daza a yiwa sojojin kasashe na horon hacking,kwarewar harbi da kuma sneaking,(sanda),. Za'ayi program na tsawon shekara uku,duk wanda yayi nasarar gama wannan horo yah fito da mataki mai kyau toh ba karamin aiki zayyiba,a yanzu haka maganar dananke mun gama yin information na badda kama ga yaranmu guda uku;Na farko Samad ta biyu sameemah sannan kuma da hakeem,saboda shi yayi karatu dama a kan na'ura,sukuma sauran kowa yasan jarumtarsu da kuma boye sirri. Jin kaman ya gama bayaninsa ne kuma gashi banji gamshashshan bayani ba yasa ni cewa, "Amma ogah munji abinda kace,saidai munaso kayi mana bayanin a wane irin yanayi zamuje wajenne?" "Kinyi tambaya mai kyau,ke zakije a matsayin RAUDAH ABDULSALAM,mahaifiyar kice yar najeria babanki kuma dan palastine,zamu baki password akan raudah dakuma fuskar dazaki na sakawa saboda kar a ganeki. Kai kuma Samad zakaje a matsayin SULAIMAN BIN HUD,sai hakeem kuma a matsayin ABDULHAKEEM BIN MALEEK,na gama bayani kowa za'a bashi information akan sabon sunansa,dakuma training da ogahna zai muku kafin yasaka ku cikin sojoji ta barauniyar hanya,saboda kar a samu matsala ko kadan. Da farko abinne mukaji shi banbarakwai ,wai zuwa kasar Brazil kuma zama na shekara uku,har mun juya zamu tafi ogah Binlad yakirani,juyowa nayi da alamar ina jinsa, "Da farko inaso karkiyi wata yarinta a can,tunda har yanzu bakiyi shekara sha bakwai ba,girmanne kawai da kuma zallan kwarewa a harkar teranci,toh kikula sosai karsu gano ke karamace" Abin mamaki yabani jin yadda ogah Binlad yazageni hankalinsa kuma kwance,nima karkakce kaina nayi kafin nace, "Toh in hakane shi tsohon yaje mana tunda yana tsoron kar yara suyi shirme idan yah turasu,sannan kuma.........." Katseni yayi ta hanyar cewa, "Bana bukatar jin komai,tunda kinji mai na ce kuje allah yah kaimu wani watan" Tun daga lokacin muka dukufah yin training din yanda zamu boye kamanninmu a cikin ainihin sojoji,ta hanyar sanin abubuwan daya shafesu,lokacin da results wanda zasu tafi yazo kowa mamaki yayi ,domin a cikin wanda zasu tafi candin,a cikin mu dari kowa yah taho daga sansaninsu an zabeshi da kuma wasu sojojin daga wani waje a cikin kasar,dukkan mu iyah mutum goma suka dauka wanda zasu tafi kasar Brazil,abin mamaki babu sunan Samad a ciki. Bakin cikine kwance a kan fuskarsa ganin zamu tafi nida hakeem banda shi,da farko nayi niyyar hakura nima,amma yanda naga yana bakincikin hakanne yasa nace zanje,dan naga ya zaiyi,kuma *zama waje daya ma ai hatsarine inji kifi*,gwanda muje muga mai duniyah take ciki a dayah bangaren. Shiri aka gama mana tsabb muka kama hanya cikin taron sojojin palastine,bisa kasada irin tamu na rayuwa. Lokacin da muka dira a kasar wani iri naji saboda tsawon shekarata shida nafi sabawa da kasar palastine,a air Port suka saukemu mota tazo daukarmu zuwa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55