Chapter 5
Chapter 5
dawa tareda cewa, "Kai dauko buhu musakashi muyi saurin gama aikinnan,dan komawa wajen shagalinnan,kunsan idan harta gama abinda take tariga mu,zuwa toh wallahi bazamuci wannan ganimar ba,nikuwa yanda yawuna yatsinke da wannan gashsshun kajin inban samu na yaga ba akwai matsala" "Hakane ogah burgu nima tawajennawa haka take yakamata mu hanzarta" Daukar labiru sukayi wanda yake ta yada kai dan wuya suka zefashi a wani katon buhu,bayan sun dorashi a mashindin arnen dawa suka dau hanya sai anguwar su labirun,wanda sannan yamma tayi,bayan layin ya dauke sawun mutane. Saida suka samu wani rami gefen kwatar gidan kafin suka jefah shi suka tafi. Parker mash in din tayi a kofar gidan ta shiga tana fed'uwa tareda yin wakar koroso,larai tasamu a tsakar gidan wato matar yayansu manjo wanda yatafi cirani ,wanke hatsin tuwo take a kwaryah,saboda neman magana sai kuwa tace, "Mutum bashi da aiki sai halayyar maza hakanma a mazan tantirai,allah dai yah shiryah" Tsayawa sameemah tayi daga shiga dakinnasu na yan mata,kafin ta jiyo ta kalli kulu din, "Kehh mekikace yanzunnan,kuma Sannan kifadamin dawa kike?" "Aikin banza Inna fadi da wanda nake ma uwar me za'ayi,karkarinta dai borin koro kunya ko za'a dakeni ne yanda akeyiwa yan dabar iyee" Jijjiga kai sameemah tayi kafin tayi wani bolll da kwaryar hatsin a kasa. Ihu larai tafara tana kururuwa tareda durawa sameemah ashar duk wanda yazo cikon bakinta. "Yar bantan uba ni zaki zubarwa hatsi ko uwarki ceh ta sayamin dazaki zubarmin?" Shiru ta hadiye wani yawu mukut,ganin yanda sameemah ta saita y'ar wuk'a a makogaranta, "Kika sake saka uwata a zancenki saina maida y'ay'an ki marayu kuma na maida manjo gwauron karfi da yaji,ki kuma sake ki gani zaki ga ko karya nake ko a'a,banza karya mai bin mazan wasu kawai" Kwalo ido tasake yi kafin ta ce cikin mamaki , "Dama kinsani?,dan allah karki fadawa manjo wallahi yankani zaiyi" "Banza karamar y'ar iska ashema tsoronsa kike ji,shine ni harkika samu damar shiga harka ta ko?" "Ahah kiyi hakuri bazan sake ba" "Kima kara mana kiga aiki da cikawa,mtswww" Wucewa tayi ta bar kulu tana d'ebe hatsin dake kasa har Sannan jikinta rawa yake saboda kashedin da sameemah tayi mata. Bakowa a dakin sai salma tana ta danne danne a irin wayar zamaninnan ,daga ganinta kaga irin matan nanne masu ji da kansu duk da cewa kyakykyawace dan inka dauke sameemah duk matan gidan ta fisu kyau,hakanne yasa take harka da manyan alhazan ds yan gidan basayi. Itah ceh y'ar larai ta fari wato yayar su hanifah,kwanan ta dawo daga bikin kawarta wanda akayi a abuja sune manyan kawaye. Sameemah koh kallonta batayiba balle ta yimata sallama,kayan jikinta ta cire kafin ta fito daga dakin daga ita sai towel a jikinta. Fitowartane yayi dadai da shigowar SULEH MAYEH (yayan labiru) gidan abokin manjo wanda tun bayan tafiyar manjo cirani bai daina shigowa ana gaisawa ba. Lashe baki ya hau yi yana kare jikin sameemah da kallo,dawani gashin bakinsa buzubuzu ga idonnan yasha kwalli dakyar kake ganin kwayarsa dan rinewar idon ,saboda shan sholi. 'Yawwa yau na taki sa'a gaskiya tunda idona yai arba da wannan d'anyar kazar yau,kai rabbana yayi hallitta a wajennan,kaiiii dolema naje nasamu tsohonnan wato baba umaru,na mika yan kudina a bani ke mushiga daga ciki tunda naga ke baka d'ebi romo ka wuce" Koh kallon inda suleh maye yake bata kallah saima neman ruwa da take wanda zata watsa a jikinta saboda zafin da'ake. Wani dan yarone yazo wucewa ta kirashi, "Kai zo nan,jeka kofar uwarka ka d'ebo min ruwa kace injini neh" Da saurin jikinsa kaman zai kifah da kasa ya karba yayi kofar tasu da gudu dan cika umarnin nata. Suleh ne yadameta da magana,dan shi a ganinsa tana jinsa,wani shegen kallo ta juya ta watsa masa kafin tace, "Kai kasan allah duk da nasan ba saninsa kai ba,toh ka tattara yan kafafunka kabani waje,koh kuma yanzu nayi maka wani naushi da saina bajeka anan wajen saidai a zo a daukeka,kaga tsohuwa sai tayi jinyar majinyata biyu" Karbar ruwan tayi da yaron ya kawo mata ta shige bandaki tana jan tsuka. Saida ta gama shirinta tsaf kafin ta nufi gidan kungiyartasu,lokacin ana shirin kiran magriba,wasu masallacin kam ma sun shiga amma itah koh a jikinta kaman ma an ce an yafemata sallahr. Lokacin da ta isa su burgu sun gyara wajen tsaf kaman ba shiba,a kijerar da aka tanada ta hakimce tana wani shan kamshi ,kayan ganimar aka bajemata a gabanta. Kajine sun sha suya mai kyau jajaye sai turiri suke,gakuma lemo masu sanyi dakuma duulah mesaka mutum ya jishi a sama,wata kururuwa su burgu suka buga dan dadin ganin irin abunda aka kawo. Hannu tasa ta yagi cinya guda d'aya tasaka a baki kafin kuma kowa yafara yagar nasa rabon,kid'a akasa mai irin buga sautinan kowa yana rausaya wa yana cika bakinsa da d'i, "Kai shugaba jar wuyah mufah tunda muna kungiyarki mun more fah,wace kungiyace zakaga ana siyan kayan dad'i ana cin wannan dad'in in ba kungiyar seemah jar wuyah ba. Wani rausayah seemah jar wuyah tayi irin na wanda aka zigashi dinnan, "Hmm aiku bari kawai saima idan an samu wata hanyar ta bud'e,harka tazo saidai kuji ana kungiyar seemah jar wuya sai ana cika form kafin a shiga" "Heeeeeeehuuuuu sai seemah jar wuyah" Dukkansu aka dauki ihu tareda shewa ganin irin kirarin da suka yi mata yah shigeta sosai. Salame ceh a zaune ana ta tad'i itama a nasu gidan da yamma itada surukanta da kuma kishin balbali, Hira akeyi wanda duk rabin hirar tasu gulmar gidan gandune, d'aya matarce wadda duk zancen da akeyi bata saka bakiba saida ga baya tace, "Babar labiru wannan gulmar dakukeyi bata da amfani ko kadan,abinda yake faruwa a gidan abune daya zama tamkar ruwan dare a namu sauran gidajen musamman ma kauyukan mu da kuma iyaye masu san ransu wanda daka yiwa y'ay'an su fa'da gwara komai ka musu,addu'a yakamata mu dingayi ba wai mudinga yayata lafin y'an uwanmu bah" "Kehh Wallahi kiyimin shiru banason wannan iyayin naki da kutufifi,zaki wani zo kina yimana wa'azi an fadamiki nasiha mukeso,toh muje masallaci mana...........," Wani yarone yah shigo da gudu yana kiran salame da karfi, "Babar labiru babar labiru,wai kizo inji wasu a waje,wai buhu suka gani a bayan gidan can yana motsi,suna budewa sukaga labiru ne wai an konashi da wuta a cikin buhun" "Kuntun ubah kai meka ce?,dagaske kake Kuwa,yau nashiga uku na lalace wane la'ananne a fadin garinnan ya yiwa labiruna haka wayyyooo na lalaceh" Amma babar labiru kamata yayi kiyi addu'a ba ki dinga ihu ba" "Dallah rufemin baki yar kan uwa shegiya wato bazaki barni da wannan wa'azinnaki ba koh,yanzu haka ma dake aka had'a baki inaga,dan dama duk bakin ciki kuke min dani da y'ay'ana" Ganin fad'an na neman komawa kansune yasa kowa tayi kofarta ,ita kuwa ta rufa hijabinta batasan ko dadai ma tasaka ba,tayi waje har sannan bakinta bai yi shiru ba. Saida su seemah suka kai wajen karfe dayan dare kafin kowa yayi tunanin hanyar tafiya gidan su,mashin din burgu ta dauka tayi gaba ,yana ta magana amma ko juyowa batayiba bare yasa ran zata dawo masa da mashin din. Hanyar anguwar su sameemah ba kowa haka ta bi da wannan uban daren ga kuma duhun
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55