Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 49

Chapter 49

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,255 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bayanta kawai kinga tayi mikk nisa,tunda Kika ga tayi haka tana nufin ki bi bayanta ne,saboda kimsan ba magana zatayimiki ba kaman sauran mutane" Dahaka surayyah da dan gudu gudu saboda tayi mata dan nisa,tana yiwa kuma burgu bye bye wanda yah tada mashin din yana shirin barin wajen. Tun daga shigarsu take ta kalle kallen cikin gidan,wanda yakeda kofofi da yawa a ciki,tana jin labarinsa amma wannan shine zuwanta na farko. Wata kofah taga sun nufah sai gasu a dakin su sameemah,a bakin gado tah zauna yayinda sameemah ita,kuma tah fita waje sai gata da pure water a plate. Ajiyewa tayi a gaban surayyah wanda ta hade jikinta waje dayah tana ta kalle kallen wajen , "Ke Kallon mai kike ne tunda zu,kincemin akwai abinda zaki fadamin kuma naga kinzo kinyi shiru baki ce komaiba" "Ah Toh dama shugaba,ko na ce anty sameemah dama nida Ahmad(burgune )muke soyayya toh shine bamusan yanda abin zai faruba,sai muka yanke shawarar fadamiki tukunna duk yanda kika yanke akai" "Nikuma nice mai yamke wa abinda yake cikin rayuwarku,ni babu ruwana da hakan saboda babu wanda nakeyiwa dole a cikin tsarina bare kuma saka shi dole sai yabi tsarina,saidia idan har ya yarda da cewa zai zauna dani toh wannan kuma daban" "Eh dama ba haka bane anty sameemah,nice ma nace dole sai mun fadamiki,saboda iyayena sun amince da zamana a wajenki,duk da sunsan ba abune mai kyau ba nake niyyar yi amma kuma sun yarda dake ba niba,sannan tunda dukkanmu nidashi a karkashinki muke inaga ke yakamata ki shige mana gaba wajen hada kan iyayenmu da yimusu bayani,dan allah karkice a'a,ke kadai nake ganin zan samu goyon baya,wani abin a rayuwata rashin yar uwa mace da kuma rashin samun abokiyah ta gari mai hankali shiya fara saka raywata cikin hakan,saidai a yanzu ni ba ganinki na ke a iyah shugabata ba harda ma yar uwata,dan allah inaso ki daukeni a matsayin hakan" Numfasawa sameemah tayi kafin tace, "Shikenan inshaallah zanyi kokarin hakan tunda kin saka yardar ki a gareni" "yawwa nagode anty sameemah Allah ya biyaki" Daga haka suka bar zancen akan zata yi musu nata kokarin amma suma su sanar da iyayenna su akwai meeting dazasuyi da itah. Dadine yakama surayyah har bata saN lokacin da ta rungume sameemah dan farinciki. Tad'i suka dan fara yi bayan wannan zancen wanda kusam rabin maganar surayyah ce takeyi,dan itah bata iyha a zauna ana tadi ba irin na mata. Sai wajen la'asar kafin burgu yazo yah dauketa suka tafi,wanda duk zamanta a dakim su salma basu kulata ba itama kuwa da ba baya bace a rashin mutunci sai abin yatafi a balance dan itahma kaman bata samu mutane a dakinba haka tayi. Tun yinin ranar sameemah takejin faduwar gaba ga kuma wani nauyi da kirjinta yake yi mata wamda bata san daliliba,ta dawo daga raka surayyah zata shiga daki taji kamar alamar ana kiranta da karfi,bata wani bada reaction akan hakan ba duk da cewa zuwa sannan tah tabbbatar wani ne yake turomata wani abun,kasancewar ba wannan ne farko ba da ake mata,kuma tanada masaniyah akai. *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤34❤ "Haba manjo ka gyara hannun mana na gyara maka rigar,wallahi hadda ragwancinka ma yamzu kam tunda ciwon ya warke ai sai ka barni na ji da y'ay'anka ma" "Wai ni kulu meyasa kika sanjane kullum cikin fada,nikam bana cemiki bazna kara shaye shaye ba,zan nemi sana'a na dungayi" "Yah rage naka kuma,in kanaso ma ka cigaba" Shiru yayi yana jinta shidai bukatarsa ta zubo masa wainar da takeyi ta rana yah ci tukunna komai ma sai ayi. Hakan kuwa akayi tana zubowa yah yagyara hannun yanan dandanar miyar ganyen masar yana antayawa a bakinsa,koh maganarsa ba kaji, "Hmm Gaskiyah nayi sa'a dana sameki dan naji ance sule har yanzu baya tashi. ~~~wani bakin tsuntsune yake ta bita mai kama da hankaka a wani waje mai surkukiyar gaske,dubawa tayi taga babu komai a jikinta sai wani farin yadi an yane jikinta daahi. Ganin babu mafita ne yasata furmawa da gudu shikuwa ya bita a baya yana wata irin kara mai ratsa cikin kunnuwa. Sun dad'e suna gudu har suka iso wani waje da hanyar bazata bulle ba sai wata babbar katanga wanda iyah ganin mutum baya iyah ganin keshenta. ***** A can kuwa cikin sukukiyar daji da kuma tsohon dare,mutane biyu ne a zaune wanda saboda maita da kuma san abin duniyah basa da niyyar kwanciyha bacci irin na kowane san adam. Sameerah ce ta kalli bokan da yake mata aiki tace, "Toh yanzu kana ganin aikin zai yiwu kuwa?" "Eh zai yiwu mana,yanzu haka tana can tana mafarki saboda munyi nasarar kama kuruwarta tun dazu,yamzu wancan tsuntsun da kike gani wanda muka tsireci da allurah uku bayan mun saka masa gashinta a cikin bakins kafin mu kasheshi,toh ruhinsa zai bayyana a cikin mafarkinta duk inda kuma yah ji mata ciwo toh bazai warkeba saidai ciwon ya cigaba da yaduwa irin na uwartah" Leka kwaryar da take gaban bokan sameerah tayi dan ganin menene a ciki,idonta ne yayi tozali da video abinda yake afkuwa a cikin mafarkin sameemah,dadai inda bokan yasaka wani abu mai kaman katanga a gabanta saboda hana ta damar wucewa. ~~~,duk da gudun da tayi amma babu alamar gajiyah ko haki a cikin jikinta,saidai rashin ganin hanyar dazata cigaba da gudun yasa ta juyah tana kallon bakin tsunstun dayake nufowa wajen ta cikin saurin gudu da yafi na karfin tsuntsaye a gaske,saisa yazo daff da itah kafin tah mika hannunta tareda cewa, "Tsaya Haka angama wasan. Yakai wannan *BAKIN RUHI*,(littafin marubuciyah oum hairan). Kayi kuskuren biyonin har wannan wajen,daga inda kake in jiyowa wani bangare na jikina a tareda kai,dan haka in umarninka daka tsaya a inda kake,idan kuma kayi gangancin matsowa toh mutuwar ma sai ta fimaka sauki" Cak ya tsaya a wajen yana daddaga fuka fukansa kaamn yaga uban gidansa, masawa tayi inda yake tareda cewa, "Yaron kirki ace dai kana jin magana" Daga idonta tayi wanda yayi za kaman jini tana kallon sama,dadai wajen da su sameerah suke kallonta,gashin kanta ma yana dagawa a iska tamkar fatalwar data fito daga sabon kabari. "Kinyi kuskure daga ke harshi din,a tunaninku bansan duk abinda kukeyimin bane?,nasani dukka kuma ba barku zanyiba ku tafi a banza,tunda yanzu har kun fara yin bakin asiri da kuma ruhin ba bayyi muku komai ba,duk da nakan dauki ruhi amma bana taba ruhin da baida laifi koda kuwa naso hakan,amma ku kunsaka kanku ciki saboda ku azzalumaine masu cutar wa. Hhhhhhahhha kana nan yan iska kuna tunanin zaku iyah yimim wani abu a duniyar mafarkine wanda take itama duniyata ce?,kai daga nan inaso ka kayanka hannunka har sai jininka ya gama zubewa,ke kuma bazan yimiki komaiba kinci albarkacin yan uwantaka amma zaki karbi naki hukuncin koh ba yau ba kuwa,idan na barki da halin da kike shirin shiga ma ya isheki,sannan idan kin dawo ki gargadi uwarki abinda na fada miki cewa karta kuskura ta sake shiga gonata,idan kuma wani ya ji a binda yafaru anan wajen toh sunanki matacciyah". *** Abin bai kara bawa sameerah mamakiba saida taga yanda bokan yah dauki

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});