Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 50

Chapter 50

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,261 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wuka ya yanka wuyahsa da itah,sannan jinin yana tafiyah direct zuwa cikin kwaryar wajen da sameemah take. Ko motsi kasawa tayi har jinin bokan yah kare yah fadi a wajen,itah kuma kwaryar ta fashe,wani dogon numfashi sameerah taja kafin tah tashi ta furma da gudu zuwa cikin gari a kafarta duk da tsohon daren. Tashi tayi daga baccin duk da har sannan gari bai wayeba dan koh assalatu ba ayiba,hankalinta kwance ta tashi ta debo ruwa ta sha kafin koma ta kwanta,saidai babu alamar bacci a idonta dan haka kallon rufin dakin kawai takeyi,idan ta tuna wanj abu sai tayi Murmushi wani kuma tah jijjiga kai. Tana bude idonta sukayi tozali da sameerah wanda ta dawo da asuba tah zo daukar wani abu dakin,dan tunda ta dawo ba yanda ba'ayi da itha na amma daga ta doso dakinnan su sai jikinta yafara karkarwa saboda tsabar tsoro,sannan an tambayeta mai yah faru tace kuma babu komai,sai aka barshi da inaga gamo tayi a hanyarta ta dawowa,itama da taji mai suka ce sai ta amsa musu da cewar hakanne. Toh yanzun ganin rana ta farayi amma sameemah bata fitoba ne yasakata shiga dakin da sanda domin daukar kayanata dan wancan din duk sun yage a hanyar dawowa daga jejin cikin hali na fitar hankali. Saidai kashh rashin sa'a,tana shigowa itakuma sameemah tana tashi,karkarwa kafafunta suka farayi har sun gaza daukarta gabadayah,bajewa tayi a tsakar dakim har sannan idonta bai bar kan sameemah bah. "Ke miye kike min kallo kaman kinga aljani" "Bbbbbba bbbbbbu shhshshugabata dama kaya nazo dauka kuma banaso na tashaki a bacci,kiyafeni dan girman allah kiyimin rai" "Hmm banace miki kar naji ba maganar nan a bakin kowa ba,toh ciki harda bakinki,gobema ki sake gigin yin shashancinki akai,dalla jita kaman kinsan allah ke,da kike hadani dashi nayimiki rai" "Ahah na tuba kiyimin rai,in da san samu ma ki daukeni aiki a karkashinki koh kuma ki hadani da mai miki wannan aikin nasan tabbas babane a harkar" Wata harara sameemah ta watsa mata kaman idonta zai fita tace, "Lallai dan adam kayan allah ,wato baki daddara ba koh?,toh wallahi idan kika sakemkn wannan zancen koh kika fadawa wani toh zanjiji sarai,kuma hukuncin bazai miki dadi ba kkh kadan" Tun kafin tabari ta karisa sameerah ta yunkura da sauri tah fice a dakin har sannan jikinta rawa yakeyi kaman tasha tsimin yan farautan. Saboda maganar da sukeyi da sameerah har sameemah tah manta davzuwa gidan su surayyah da zasuyi itah da kawun burgun saboda tambayo masa izini,daga wayar tayi domin kiran burgu dan taji koh kawunnnasa yah shiryah dan itah bata son zuwan daren ta fiso ta gama da wannan babin kawai. Tashi tayi tah fara shiryawa jin zuwannasu yana nan ba'a canja ba. Dayake Surayyah ta sanar da zuwan su sai aka fara shirin taryarsu tunda wuri,dan haka lokacin da suka shigo kowa yana gidan harda babanta shima yau bai je aiki ba. Toh wata sabon gani surayyah ta fada a ranta ganin yanda sameemah tasha wani uban hijabi mai alkyabba kaman ba itah ba saboda koh a tairihi babu wanda yah taba ganin tasaka,"gaskiyah koba komai na samu matsayi a ran shugabrtawa alalmu ya nuna ta karbi tayin zamana kanwa a wajenta" Har suka wuce falon baki inda akayimusu shiri bakin Surayyah bai rufuba dan farincikin ganin su sameemah,koh yaushe suka hada ido sai tayiwa sameemah Murmushi itakuwa koh sau daya bata sau fuska ba bare kuma tayi mata magana,hakan bai damu surayyah ba koh kadan saboda tasan haka take,kuma itah haka kawai sameemah take burgers Kodak bata yimata komaiba. Maganar abinda yah tarasu suka farayi bayan kowa yah kammala abinda zaiyi. Babantane yafara magana bayan yah bude taro da addu'a. "Toh da farko tun banji abinda yah taraku anan wajen ba hankalina a kwance yake,don yanayin da kukazo da kuma yamda kuka sananr damu zuwanku akan wata muhimmiyar magana nasan abin alkhairi ne,dan haka zamuso muji abinda yake tafe daku" Alhaji isah yayan mahaifin burgu shiya fara jawabi kafin yah fara magana da jawabi duk da bai fito fili ya fadi abinda yake ransaba. Haushine yakama sameemah ganin yanda suke tah jan magana guda daya ana ta bata lokaci ,dan dama tun sanda shigo bata ce komaiba,katsewa kawun burgun tayi tareda numfasawa tana kallon agogonta tukun kafin tafara cewa, "A takaice dai a daina wani bata lokaci,ni sunana sameemah nasan kunsan sunan koda fuskata zatayi muku wuyahr sani,sannan kuma nice shugabar kungiyar da yaranku suke ciki kafin yanzu kuma suna karakshi kuwata ta kungiyar vigilantee,kuma dukkanku saida kuka amince kafin na fara aiki dasu,wanda hakan ya nuna kun yarda dani a kusa da yaranku. Sun zo sun sameni akan nayi magana da ku amatsayin iyayensu saboda su basuda karfin gwiwar tunkararku saboda abubuwan da suka faru,abayah. Sun ce su na son junansu kuma kuma burunsu shine hakan yakaisu ga aure,shin kun amince???. Shiru wajen yayi kowa yana nazari,ganin hakanne yasa sameemah cigaba da cewa, "Ni nazo a matsayi guda hudune,na farko amatsayin shugabrsu na biyu a matsayin yar aikar sako,na uku a matsayin abokiyar Ahamd(burgu)na hudu kuma a matsayin yaya ga Surayyah kuma yar uwa,wanda jiyah ta rokeni akan na zamo tamkar yaya a gareta kuma na amince,dan haka ni na amince da kasancewarsu tare saboda hakan abune mai kyau wanda ake fatan yah dore" Kowa ma dayaji abinda sameemah ta fada kuma sun san dagaske takeyi sai kawai suka amince har aka fara shirye shiyen yanda abin zai kasance,daga haka taro yah kare kowa yah tafi nasa harkar. Dadai lokacin da sameemah tazo fita daga zauren gidan taji an rungumeta ta baya,ko bata fada ba tasan mai aikata hakan,muryar surayyah tah tsinkayo tana cewa, "Nagode sosai da kokarin da kikayimana anty sameemah,ina lekawa duk naji abinda kika fada,hakika ko kowa bazai alfahari dake ba ni ina alfahari dake antyna. Har cikin ranta sameemah tah ji dadin abinda surayyah ta fada,amma a fuskarta iyah karamin Murmushi tayi tareda cewa "nagode"atakaice kafin ta fice. *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤35❤ Wata biyu aka saka biki surayyah da burgu,babu a binda suke sai murna da hakan saboda ganin burinsu zai cika,dan yanzu ko a wajen aikima soyayyar su suke sha,dan ma sameemah tana taka musu burki ganin abinnasu yana nema yah wuce gona da iyahka. Kwanaki haka ma watanni sun shiga,yanzu sameemah tana neman shekara guda akan kujerarta,inda yazamo cewa burunta na yin suna a garin yah fara cika saboda duk inda ka shiga babu abinda ake labari sai gwarzuwar macen da tayiwa maza zarrah barekuma mata,ta kawo cigaba da kuma gyara da dama,amma idan muguntar tazo ma ana tabata kuwa. Maganar da baba umaru yayi musu na aure tana cigaba da matsowa,saidai koh kadan hakan bai damu sameemah ba dan tasan zancen bai shafeta ba ta kowacce siga. Su kuwa wanda zancen yah shafesu wato su inna ramatu ana ta shirin hidimar biki,dan saurayin zainab yah turo akan yah shiryah shima yanzu. Wata motace a tsaye a bayan gidan su sameemah tah faka a cikin duhu dan kar a gane me suke a wajen,salma ce cikin yatsina fuska tace ,"alhaji yakamata idan sona kake toh ka fito,dan nima tunda

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});