Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,271 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

labarinsu dana keji a nayi kawai.yaran cikin motar kuwa su iliyah da bazasu wuce shekarunmu ba sai kuka suke suna kiran sunan iyayensu sai kace wani shegenne yace su taho. Motarmu ce tafara sloww a hankali har muka tsaya cak da tafiyah. Wata muryah ce marar dadin ji ta doki cikin dodon kunnena daga jin muryar babban mutumne kuma ba yaran hausawa ba,masifa yake yiwa direban akan ya fito daga cikin motar. Fitowa yayi yana gaishesu,saida suka kwala masa wani abu kafin daya daga cikinsu yace, "Kudi ka bamu kudi koh kuma mu dauka rai" "Ogah babu kudi yamzu muka debo kayan" Wani ne daga cikinsu yace kai wannan ka barsu kawai basuyi kama da wanda zamu samu kudi a wajensu ba" Har sun barshi yakoma cikin motar mu fara tafiyah,wani yaro daga cikin mu yayi atishawa saboda murar dayake yi,hantar cikinmu ce tah kada dan dagani kashinmu yah bushe yau. Tun kafin na gama Tunani naga sun yaye tampol din da muke ciki sai gamu gasu lokacin da suka dallemu da wata fitila mai haske. Wani daga cikinsu ne ya duro cikin motar yana daukar mu yana mikawa wanda yake waje shikuma yana diremu a kasa,kallon mu sukeyi da mamaki ganin yara a motar kayah. "Kai driver kenan sato yara kayi baka fadamana ba" "Ahah ogah ba sato su nayi ba,zan ajiyesu a babban garine na wuce" "Taya zamu yarda dakai lallai dole kayi bayani" Dukansa suka farayi yana ihu tareda rantse musu,nice nayi saurin cewa, "Ba sato mu yayi ba mu ka ce yarage mana hanya zuwa cikin babban gari" Tun kafin na rude baki wani daga cikinsu yah yadak'i dan kwalina tareda gashina da karfi,wata kara na sake mai kara saboda azabar danaji,zefarni yayi a gefe tareda cewa,ku kama yarannan dukka ku saka min su a motah. Su iliyah suna jin haka suka fara ihu,babu abinda na tuno a raina sai yanda dukka yaran iyayensu suke matukar nuna musu soyayya,yah zasuji idan suka ga cewar yaran su sun bata kenan har abada,musamman mahaifiyar iliyah shikadai ta haifa a rayiwarta ,dole na ceci abokaina in ba hakaba zasu illatar dasu,sannan koda na saukar da rayuwata babu komai tumda idan na mutu a sannan babu wamda yake sona bare yah tuna Dani,da haka na samu karfin gwiwar tashi daga wajen nace, "Bazaku tafi dasuba,saidai ku tafi da ni kadai, in ma tafiyah zakuyi da wani daga cikinmu,sukam dole su koma wajen iyayensu cikin koshin lafiya" Dariyah ogannasu yah fashe da itah ganin yanda na wani murtuke fuska kaman wadda zata iyah masa wani abu,tahowa yayi wajena yah kamani tareda hade hannuna waje daya yana kallon fuskata,cizo na garya masa a hannunsa na kusa da fuskata,aikuwa cikin sauri yayi min duka mai karfi wanda saida hankalina yah gushe. Cikin juyawa da kaina yake na ga lokacin da motar yan sanda tah fara tahowa daga nesa,yayinda ogannasu yace su daukoni su sakani a cikin motarsa,ina ganin lokacin da motar dana ke ciki tana ta tafiya cikin jeji hoton motarmu kuma yana karayin nisa a cikin idanuna har wani duhu yah lullube ganina. Bude idona nayi na ganni a wani daki mai dauke da yara da yawa,dukkansu tsiramin ido sukayi kaman sunga dodo,nima a vangarennawa kallonsu nakeyi da tunanin a wane waje nake haka,babu wanda zai amsamin tambaya ta da alamu saboda yaran dukkansu a tsorace suke taya zasu amsamin wata tambaya. Daga idona nayi ina kallon wani mutumi wanda shigowarsa dakin kenan,kama yayimin dana daba ganinsa awani waje,saida nayi Tunani kafin na tuna da yana daya daga cikin yan fashin da muka hadu dasu a hanyarmu ta zuwa babban birni,cikin kankanin lokaci hankalina yah fara tunanomin abinda yah faru dallah,saboda hankalina ya gushe lokacin baya saboda dukan da shugabannasu yayimin a kai. Daga ido yayi yana kareni da kallo sannan yana daga gira,nima kallonsa nayi saidai ban dade ba na dauke ganina daga Kansas ina sunkuyar dakai kasa,wani ne daga bayansa naji yana tambayar sa cikin gurbatacciyar hausa. "Wace yarinyace wannan kuka kawo jiyah" "Mutumiyar ogah ce yana bukatar hukuntata ne,idan yah warke,dan yanzu haka yana can daki hannunsa ya shanye saboda cizonsa datayi,nazo yin magana da itah kuma naga kaman da alamun hankalinta yah gushe saboda mummunan duka da ogah yayi mata akai" "Wai dagaske kanayi shine abinda yah faru" "Eh babu karyah akan hakan,yanzu bari na kaitah dakin ogah doctor yana nemamnta" Duk maganar dasuke inajinsu,saidai koh daga kai banyiba,amma batun hannunsa daya shanye nasan dama hakan zata faru dan yadda jinina yake da guba haka ma bakina,nikaina ina Mamakin hakan. Fizgata yayi ta kayi saidai da alama shidin a tsorace yake dani,domin duk yah daure hannunsa da wani karfe,duk da halin ciwo da nake na rikeni dayayi saida nayi dariyah da abinda yayi din. Dakin babu nisa daga inda yah fito dani saidai kuma yanayin surkukiyar wajen daga gani anyi ne domin samun damar tserewa idan rana ta baci. Ni kaina saida abin yah tsoratani ganin yanda hannun nasa yayi wani baki musamman wajen da cizon yah fara,kamar wanda maciji yasareshi,sunkyar da kai nayi har ya sakko daga kan gadon ya iso wajen danake,kama kumatuna yayi kafin yah dago da fuskata dan dole. Nima kallon mummunar fuskar tasa nake mai,cike da takaici a cikinta, "Ke me kika saka min acikin jikina mai azabar ciwo wanda inaji yana kone jinin jikina sannan kuma yana rubar da fatar jikina?" "Ni babu abinda nayi maka,kawai wata cutar ce dakai" "Ke kewaye da har zakice haka,zaki fuskanci hukuncina dole,ku daureta a cikin cell,sannan ku fara shirye shiyen tafiyarmu,kasar da zamuje ta boyayyiyar hanya" Komawa sukayi dani daga amma yanzu wani daki ne daban mai matukar duhun gaske. Tun daga bakin kofar mutum yake jiyo kukan beraye da kuma warin datti dana mushe,tunkudani ciki sukayi tareda maida,kofar suka rufe. Tafiya nake a hankali a wajen saboda bana ganin gabana har na isa jikin bangon dakin,samun waje nayi na zauna dan ganin mai zai faru kuma yanzu. Mutanen da suka saba zuwamin ne yauma suka zo,saidai yanzu sun sanja kaya daga jajaye zuwa bakake wuluk,kara mikomin kwaryar sukayi yauma dauke da wani jan ruwa a ciki,har nayi kokarin kawar da kai mutumin yace, "Karki dam u wannan ba ruwan dawowarki cikinmu bane,wannan na biki ne da mukeyi,kuma yah zama dole shikin sha wannan domin a wannan lokacinne zaki fara taka mataki na gaba" Sake mikomin yayi bayan ya gama bayani,abinda yah ban mamaki shine na kasa yimasa,musu akan hakan saima karba nayi na kai baki,dandanon gishiri naji dakuma karni daya ziyarci hancina,cikin sauri na sau kwaryar ta fafi kasa ina mai cewa, "Jini jini kuka bani na sha ,meyasa" "Saboda shine nasararmu zaki sani daga baya watarana,yanzu zamce yakare tunda kin dandana a bikinki,duk wanda kika dandana jininsa a nan gaba zai kasance namune,ki saka wannan acikin kwakwalwarki" Tun daga wannan maganar na farka daga baccin danake yi,yau banyi Mamakin ganinsu ba saidai abinda yabani mamaki shine abinda suka bani nasha,kuma tun daga lokacin nakejin kaman ana zigani na ciji mutane. Bamuyi kwana uku a wajen ba na ga wani yazo wajen kejinnawa amma ba wanda yasava kawomin abinci bane,budewa yayi tareda yimin alama na biyoshi,saboda hasken daya ziyarci idona karo na farko bayan kwana uku,bansan lokacin dana rufe idona ba,saida nasaba da hasken

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});