Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,274 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kafin na bude ina kallon sararin samaniyah,da sauri na bishi ganin yanda yamin nisa kafin na isoshi. Samun su nayi kowa yayi shiri,dukka yaran an saka su acikin mota ,nima ina zuwa suka iza keyata cikin motar muka fara tafiyah. Tafiyar mai nisa mukayi,tun muna ganin rana har ta fadi mukayi bacci gari yah sake wayewa amma duk muna cikin tafiya,dukkan mu idan ka ganmu mun yi laushi lukwui saboda tsabar gajiya. Bude ido mukayi kawai sai ganinmu mukayi a bakin wani tafkeken ruwa,sai shiga jirgin ruwa ake ana wucewa. Mu ma cusamu akayi a wani jirgin ruwan saidai a kasan cikin jirgin ruwan inda babu wanda zai kuladamu. Nan ma munyi tafiyah mai nisa kafin muka ji ana mana alamar mu fito ,kallon inda muka nake da mamaki. Toh kuma nan ina ne ??? *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤16❤ Da mota aka daukemu zuwa masaukinmu wanda shima cikin lungunne kaman wanda muka fito a ciki,duk da bansan a wani abu ba lokacin amma nasan wajen ba kasarmu bace,saboda duk mutanen da muke wucewa fararene tass kaman zabiyah,kallon hanya mukai tayi har muka isa inda zamu zauna din. Washarin saukarmu a sabon wajenne muka tashi da cewar ogan su yah mutu,saboda cizon danayi masa sati d'aya daya wuce,zuwa sukayi suka sake daukata zuwa dakin dayake inda likitoci suke ta zirga zirga, Yaron oganne wanda shine mataimakinsa,tsaye yake akan gawar yana kallon yanda yayi bakikkirin kaman an shafeshi da gawayi,rufeshi yayi da wani farin kyalle idonsa yana zubar da hawaye,juyo da kallonsa yayi i zuwa gateni wanda nima kallon gawar nake. Tun daga fuskarsa zaka san ransa yah baci matuka saboda hatta naman jiknsa rawa yakeyi. Wata wukace a hannunsa mai masifar kaifi yake nufoni da itah,wani bugu zuciyata takeyi ina matsawa da baya domin nasa hukuncin ba mai dadi bane,magana yafara cikin dacin harshe, "Dolene kema ki mutu kuma kisan wulakanci tunda har kikayi sanadiyyar mutuwar dan uwana" Damkar wuyana yayi yah dagani sama yana kallon cikin idona,har sannan wutar bakin cikin dake huruwa a cikin ransa bata daina ruruwa ba,daga wukar yayi yah shaftata min wuka a makogarona,wani irin zafine ya ziyarci wajen inda nayi sautin saka hannu ina tari,tsorone ya kamani jin yadda iska ke fitowa daga makogarona a maimakon tah hancina ko baki,ina jin yadda iskar ke daina fita har yah zamo ta koma fitowa daga inda dama ya dace da ita wato hanci. Dauke hannuna nayi daga kan wuyana ina,kallon yanda jinin dake hannuna yake konewa,a lokacin dana kai kallona kan mutanen dake dakin dukkan su kowa ni yake kallo bakinsa bude,ni kuwa ko ta kansu banbi ba saima,fita da nayi daga dakin ,saboda idan Mamakin abinda yah farune ni na dade da gama wannan Mamakin,kawai na mika wuyah da duk ma wace halittace ni shikenan komai yah banjama banjam. Tun daga lokacin babu wanda yasake tunkarata da wani zancen komai kaffah kaffah sukeyi kowa yana tsoron zuwa kusa dani,tun abin yana min dadi har yafara damuna saboda yanda sukeyimin kallon dodo abin babu dad'i,sai a sannan na tuno illar da ummah take nunamin na gujewa nuna ainihin ni wacece a gaban mutane,musamman ma wanda suke kusa dani,dan saina budi ido na rasa kowa a DUNIYA TA. Washagari da safe lokacin dana tashi babu kowa a dakinnamu,abinne ya dauremin kai saidai ban ce komaiba,tashi nayi na fito waje nan ma ban hadu da komaiba, Wasu mutane nagani da alama kaman yan sanda ne danna gansu da kayan tsaro,suna kallona suka iyo wajena tareda sakamin wata sarka a hannu,nidai kawai kallonsu nake har muka dau wata hanya bayan mun shiga wata mota mai budadden baya. A bakin wani get muka tsaya saida wani mutum yah duba kafin muka shige. Gidan yana da bangarori da dama,gashi babban ginine wanda tunda nake ban taba ganin irin wannan gininba. Iza keyata sukayi har wani bangare wanda yake can karshen gidan,muna shiga naganshi kaman gida saidai,da gani wajen da tsaro sosai,a wani daki suka sakani bayan an cire sarkar da take hannuna. Wasu yarane a dakin guda hudu dukkan su suna sanye da kaya kaman uniform din makarantar garinmu irin wanda,aka bani bayan shigowarmu wajen,biyu daga cikinsu bazasu kaini ba,amma dayar da take gefe ita kam zatayi sa'a ta daga ganinta,dukkansu fararene tass da alama basuyi kama da kalar fatataba,duk da cewa nima farace amma baza'a hada nawa farin danasu ba. Samun waje nayi na zauna a gefe duk da yanda nakejin fitsari babu damar na tambaya tunda bansan da wane yare zanyi magana ba,saura kiris fitsarin yah zubo kafata har rawa takeyi naga daya daga cikinsu ta tashi ta shiga wani dan daki shima a cikin inda muke dinne. Bayan ta fitone nima na shiga saidai ja nayi na tsaya ganin wani katon baho a bandakin da kuma wani dogon karfe a tsaye sai wani abu kuma mai dan kai shima a kasan dogon karfen,tsugunnawa kawai nayi na tsula fitsarina koma dakin waye shiya sani. Bayan na gama ne zan tashi sai santsi ya debeni,kama bakin dake jikin dogon karfennayi gam,amma sainaji yah juya ruwa kuma ya fara zuba,tsayawa nayi ina kallon ruwan da mamaki ganin daga inda ruwan yake fita,kunnawa na farayi ina kashewa nayi yafi goma kafin na tsaya dayi,fita nayi da sauri na dauko wannan kayan da suka bani masu kyau kalar ruwan omo,zuwa nayi na wanke jikina kafin nasaka su na fito ina bubbudawa nima na saka irin kayansu. Yanzu nayi sati daya a wajen,kullum za'a kawo mana abinci mai dadi,su kam na dakin kaman basa son zaman wajen da kullum cikin tagumi suke abincin ma basaci da yawa,nikuwa saina cinye nawa na side kwanon wani lokacin ma saina hada da nasu na cinye tass,ga wanka yanzu nasan yanda ake amfani da komai na bandakin sainayi sau uku ma a rana,sannan idan rana ta dan fito sosai za'a kaimu wajen karatun su larabci da kuma su litattafai na addini. Cikin lokaci kankani nayi bulbul dani fatata har sheki tajeyi saboda tsabar dadin danake ci,abu daya na tsana wanda yake cimin tuwo a kwaryah,shine duk lokacin sallah sai anzo an tafi damu zuwa cikin masallaci ran juma'a kuma zasu bamu abaya da gyalenta musaka mu tafi masallaci,ga karatun asuba dole sai kowa yayi,wannan shikadai yake hadamu dasu,idan kuma mutum bayyiba ayi masa duka lilis,kuma sai ka wanke dukkan kayan yan dakinku da kuma wankin bandaki. Yanzu nafara sanin wani abu idan yan dakinmu sun fada ,dan yanzu nasan sunansu suma sunana,khairah da hairah,su yan biyune,matar babansu suka yiwa wankan soyayyan mai shiyasa aka kawosu,ita kuma shaheedah guduwa tayi daga gida tabi yan iska,shiyasa yan uwan babanta suka kawota nan,tambayar su nayi nikuma meyasa aka kawoni wajen,cewa sukayi wai sunji ana cewa an kamani ne da hodar iblis(cocaine)a cikin wani gida da ba'a amfani dashi,da alama wai abokan aikina ne suka gudu saini kadai,cikin kankanin lokaci nayi tunanin cewa,da gangan suka gudu suka barni a kamani saboda tsorona da sukeyi. Tun daga lokacin muke dan magana da,su shaheedah duk da cewa banajin yaren larabci sosai amma ina gwadawa,har take fadamin sunan kasar su palastine. Abin bai wani ban mamaki ba tunda ba wani sanin mai take

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});