Chapter 28
Chapter 28
masauki. Tun daga washa gari muka fara aiki ba dare ba rana,wanda cikim saka abu a rai da kuma kwazo banyi wata shida ba saida ya zamo ko ina sunan RAUDAH ne yake zagawa har na fara mantawa da Sunana sameemah in ba Hakeem yakirani muna mu kadai ba. Sukuwa sojojin palastine har murna suke saboda a cikin tawagarsu nake,shikanasa ogahn duk abinda ban saniba shiyake nunamin domin burinsa na fito da tauraro wanda zai daga kasarsa. Lokacin da muka shiga shekara ta biyu aiki yah fara tsananta,domin har wajen kaiwa a hari ake turamu,ni ina a cikin rukunin yan hacking amma wani lokacin idan naga yannamu zasu kasa yi,bansan lokacin danake shiga cikin filin ba,da haka ta nan ma nafara koyon aikin sojoji na shiga filin yaki,dan idan na bisu mukanyi sati biyu har wata bamu dawo sansaniba. Wani lokacin wasu su mutu,wasu kuma su dawo a wahale,mune yan basu taimako da kuma cigaba idan wasu sun gaza. Tunda nake binsu fili ban taba dawo wa da ciwo ko dayah ba,domin a wajen yake warkewa da kansa cikin yan mintuna,duk da babu wanda ya taba yimin magana nasan kowa na mamaki,saidai suka barshi a matsayin kwarewa ta ce kawai. Bayan mun shiga shekara ta uku sannan kam na kware a ta bangarori da dama ciki harda abubuwan da ban taba tunanni zan gansu ba ,irin tuka egwuwa,da kuma harba bombs. Kowa hankalinsa ya tafi yanda zaici gasar karshe saboda yakoma kasarsa cikin abin alfahari da yabo. A cikin wata na takwas kafin shekarar ta kare muka fara shirye shiryen tafiyah wajen gasa tah karshe,wanda zamu shiga cikon wani bakin dajine mai cike da arna duk wanda yah fito da rai cikin kwana goma toh sune wanda za'a bawa tutar yabo. Mukuma masu hacking wani mission aka bamu wanda zamuyi bayan wata daya,akan wasu gogaggun barayin hacking a kasar Canada,duk wanda yayi nasara shima shine da tutar yabo. Shiga nayi cikin yan zuwa daji muka tafi,ko ba komai zan kashe kwarkwatar ido,aikuwa naga abin mamaki,nan akayi ta artabu aka kashe mutane da dama,mu wanda muka fito babu fi mu dari ba,dan ma na taimaki wasu da yawa. A wajen hacking kuwa kwana muke a gaban computer sai bacci ya kama mu muyi,idan mun farka mu cigaba,mun fi sati muna abu dayah kafin wani yaro a cikin mu yagano lagonsu,muka afakamusu. Idan aka sakawa abu rana toh sai yazo,yau mune a tsaye a fili da kayan sojoji muna kiran karbar sakamako,tun waccen satin aka fara sallamar wanda sukayi nasara,dayake mune Batch C,muna kasar Brazil,yayinda Batch A suke America,sai Batch B a Canada. Nice na karbi numaber yabo ta uku,bayan wasu guda biyu a kasashe daban daban sun karba. Daga kyautar nayi a hannuna,ta silver sai sheki take,anyi alamar soja mace a jiki da kuma sunana wato RAUDAH, yayinda a daya bangaren kunnuwa na suke jiyomin karar sauti tafi rafff rafff da kuma harbin bindiga,kuma duk ni akeyiwa. Kowa murna yakeyi acikinmu zai koma gida da irin nasarar daya samo,wanda suka mutu kuma saidai muce Allah ya jikansu da rahama. Shugaban tawagar palastine ne ya taramu murna a cikinsa kamar ba gobe,bakinsa yaki rufuwa saboda murnanar nazo tah uku,a cikin kasashe da dama,magana yah faracikin harshen turanci maimakon larabci,wanda yasan kowa yah iyah saboda zamanmu cikinsu. Kowa zuwa yayi yah kwanta da niyyar gobe za'a fara shirye shiryen komawa gida jibi kuma mu tafi, Wani duhu nake gani saidai duk da bana gani sosai nasan gidanmune na Nigeria,wutace take cin cikin gidan amma kowa yah ki kaiwa taimako,gani na nayi a tsaye a gefen gidan mutanen cikin gidan suna ta ihuu amma babu wanda ya kulada ni,wani mutum ne naga yazo wucewa na ja rigarsa,tsayawa yayi yana kallona kafin nace, "Bawa allah baka ganin suna neman taimakonka ne?" "Nagani amma ke da kike yar gidanma aikin barshi ina kuma yani,ke mai zai hana kidawo ki taimakesu hannunka a baya rubewa kayanke ka zefar,saidai kayi masa magani koda kuwa maganin akwai wahala har ka samu yah warke........kidawo gida,saboda wanda yabar gida ,gida ya barshi. **** Da sauri na tashi daga kan katifata jikina duk gumi,mafarkin danayi kuwa har sannan yana ta dawomin cikin kaina,babu abinda nakeson gani sai kasata Nigeria,zaman kasar wasun yah isa haka. Filin jirgi muka iso kowa yasha kayansa yana jan trolly a kasa,tafiyah muke cikim tawagarmu tah yan palastine kowa ka ganshi murna yake saboda nasarar da aka samu. A waiting room muka zauna muna jiran sunanmu yazo layi zuwa jirgin palastine din,shugabanmu ne yah fita shida wani daga cikinmu zuwa dubo wani abu wanda bamu sani ba. Sunana ne yake amsa kuwwa a jirgin da zai tafi Nigeria,wato SAMEEMAH UMAR,tashi nayi hankali kwance na maida glass idona tareda jan trollyn na nufi hanyar jirgin,Hakeem ne yah ankare dani tunda dama yasan sunana,hakan yasa sauran ma suka farga da jirgin danake kokarin hawa,saurin riko hannun doguwar rigata yayi tareda cewa, "Kee sameemah mai kike kokarin yine,wannan fah ba jirgin kasarmu bane" "Eh ba jirgin kasarku bane,amma ni jirgin kasarmune ai,koh baka ganine" "Hankalinki d'aya kuwa,kinsan mai kike shirin aikatawa,idan ogah Binlad yagano mai zakice,kinfi kowa sanin ya matsu ki dawo saboda nasarar da kika ciyo" "Toh so what Ubana ne shidin,kuma ta ina zai hadu dani din,daga yau babu wanda zai sake ganina a cikinku saidai tarihina,dama shine abinda nake barwa duk wanda muka zauna,ni zan tafi kasarmu nasara kuma kai ta shafa bata shafenba,daga nan ma bazan sake maganar ta ba" Har na fisge hannuna na tafi,sai kuma najuyo,har sannan yana tsaye kaman kungi da Mamakin abinda na aikata,Murmushi nayi masa tareda cewa, "Ka gaidamin kowa idan ka isa lafiyah,musamman ogah,kace ina yi masa missing๐๐๐" Karfe biyu na rana dadai na sauka a kasata wato uwa Nigeria,tundaga yanayin mutanen nasan Nigeria ce kam,a garin abuja muka sauka,ana tah hayaniya wai wani dan sanda sai yah caje wata mata a airport din,duk da ba hausa nakeji sosai ba a wajen saboda dadewa da nayi banyiba,amma na cafki wasu kalmomin kuma nasan shine baida gaskiya. Rike hannunsa nayi wanda yake kokarin dorawa a kugun matar,wanda hakan yasa fadan yah dawo kaina,matsowa kusa dani yake wai nima sai ya cajeni,banyi tsammaniba kawai naji hannunsa a kan kirjina,bansan lokacin dana sauke masa dukkan training din danayi ba na tsawon shekara uku akan fuskarsa ta hanyar zabga masa mari. Tun kan na sauke hannuna na nemeshi na rasa ashe yah zube kasa sumamme,karfe naji a hannuna saida na duba ashe ankwa ce suka sakamin dan zuwa police station,banyi musu ba na bisu muka tafi inda suka bukata,saboda koda zanyi magana ba zasu gane so sosai ba hausar tawa sai a hankali. File suka fara cikewa akan nayi attemp din kashe dan sanda ,nidai ban ce musu komai ba har suka gama rubuce rubucensu suka gama,a raina nace mai hali baya fasawa,wato mutanenemu na Nigeria sai a hankali wajen san kai sa kuma yin hukuncin zalunci,wannan kam sun rufe kofah a kai. Prison a ka turani kasancewa babu wanda zai min beli na tsawon wata shida,banji komai a raina ba,allah na tuba nayi shekara shida ma a prison ai ,menene kuma wata shida ,kaman gobene,kuma wallahi tunda a prison din duke aiki dukkan su,zasu ci ubansu a guna sai sun kwammaci sun sallameni yah
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55