Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 20

Chapter 20

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,277 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wanda aka sanjashi tun daga mutuwar ummah,takaicine yah cika zuciya tah ganin wanda zan ji sanyi a wajensa ma kallon na takura masa yake,yana kallon na takura masa,dole na sanja tunani na tsaya da kafafuna kawai. Tashi nayi cikin sanyin jiki na koma d'akin na kwanta, Jeji ne wajen mai cike da duhun dare da kuma ban tsoro,idan walkiyah ta haska babu abinda nake gani sai wasu halittu a tsaye,matswa nakeyi jikina yana rawa had'e da karkarwa,ji nayi na dungura da wani abu kaman bishiya alamun babu inda zan sake matsawa kenan,saidai abubuwan basu fasa matsowa inda nakeba shiru kawai nayi dan na saddakar da sake rayuwa a lokacin. Rike fuskata daya daga cikinsu yayi yana hada kallona dashi,cikin wata irin murya yake magama mai cike da amo wanda nakejin ta har cikin jikina ba iyah kunnena ba, "Hakika dole watarana zaki sallama ki dawo inda yah dace dake,kedin mallakinmu ce,duk da busan inda kike ba har yamzu amma dole muna hade dake,dole zaki dawo inda ya dace dake watarana,sakin fuskata yayi wanda saida wajen yah faramin zafi saboda rikon dayayi min,wata kwaryah suka mikomin mai cike da wani abu kaman jini,kin karba nayi ina kallonsu kawai,dannima gwana ce a taurin kai insu suna gadara da iyah shege,yah mutsa fuska nayi tareda kawar da kai, "Bazan saha ba" Shine kawai abinda nace, "Hhhjhh babu dole a harkar musamman ma ke kinada muhimmanci a wajen mu muna jiram amincewarki" Tun daga lokacin na ga kamar an wayemin wani duhu sai kawai na ganni a dakinmu,toh mafarki nakeyi ?ko kuma gaskiyace ni kadai nayiwa kaina tambaya sannan na kasa bada amsa. Tashi nayi naje na sha ruwa na dawo,har sannan mafarkin danayi yana tsaye a raina,yau kusan kwana uku kenan kullum sanayi irin mafarkin,duk da ina shakkar daukarsa a matsayin gaskiya amma nasan yanada alaka da wani abun,saidai banida wanda zaikula da halin dana ke ciki bare yatayani yaki da abinda yake shirin tunkaroni,zama nayi akan gadon duk abin duniya yah isheni,da kuma wane irin aiki zan samu na dungayi saboda magance lalurin rayuwata,tunda nagane abinci ma baza'a bani mai yawa ba ina kuma ga sauran abubuwan bukata na rayuwa. Da safe ina tashi bayan na cinye d'an dumamen da'aka bani nayi wanke wanke sai na fita waje wajen abokaina su wanda yanzu suke zuwa gonaki aikin gona,ina zuwa kuwa na samu suna jirana saboda munyi dasu nace nima zanje. Gonar da nisa sosai haka muka tafi a kafa,dayake tafiyar yarace bamu damu da nisan ba haka har muka isa. Gonace mai girma sosai babu komai a ciki sai wake,yah nuna yayi kyau,roro muka fara cikin buhu naira d'ari d'ari,da murna na fara jin zan samu kud'i nima na sai abubuwan danake bukata. Saida muka kai har lokacin wajen azahar kafin kowa yaje yah faracin dan tuwon daya zo dashi,nikam ban tashiba saboda nasan idan naje wajenma babu abinda zanci tunda banzo da komaiba,su iliya ne sukai takirana nazo muci amma naki,saboda banason a yanzu dogaro da abin wani koyaya yake kuwa. Kafin a tashi saida na cika buhu guda biyu,ko su dasuka saba zuwa buhu daya sukeyi,mamaki na bawa shikansa mai gonar inda yah bani dari biyu da hamsin saboda dagewa danayi,karba nayi tareda godiya muka kamo hanya muka dawo gida. Ina shigowa gidan naji karar karan dawa a bayana,tun kafin mai dukan yayi magana nasan inna ramatu ce,aikuwa bata gama sauke karan ba tabini da uwar ashar tana fadin, "Yar kusun uwa shegiyah,gidan uban wa kikaje tun safe sai yanzu kika dawo ina ta neman ki ki iyo markad'e" Babu alamar kuka na kalleta raina a bace nace, "Aikin kudi nabi yara wata gona" "Eh lallai wuyanki yayi kauri nawa kike harkin fara wani neman kudi,ke yanzu har kinkai a barki da kudi?,bani kudinnan naga naira nawane,wuyarki danake sha duk wani kudi kika samu dama ki kawomin su" Kallonta nake da Mamakin jin furucinta,su kuwa su inna larai suna gefe suna zigata kaman in anamin azabar cetona sukeyi,maida hannuna nayi baya alamun bazan bata kudin ba,wata wawiyar cafka ta kawowa hannuna na yi saurin gocewa saiga ta tashsh a kasa tayi zaman yan bori,daga kai tayi tana kallona da mamaki,saidai babu alamar tsoro a idona saima kallonta nake kaman zan kai mata duka,hakika in idona yagani dadai kaman na ga alamar shakka a idonta,wuceta nayi na nufi d'akinmu,na tona rami na boye naira d'ari,kafin na d'au hamsin na tafi wajen mai shayin unguwarmu domin nasiya. Daga ranar tunda nagane da aikin gona ko yan anguwarmu bazasu je ba saina je,dan yanzu nagane da zamana babu kudi hatsarine tunda babu wanda zai kula da rayuwata. Yauma tafiyah mukeyi nida su iliyah kaman kullum,saida mukayi kusan rabin tafiyar,mun bar gari a baya,turus muka tsaya ganin wani maciji a gabanmu,abin yara da tsoron macijj cikin sauri muka koma da baya zamu koma,saikuma cikin rashin sa'a yah sareni saboda nice a gaban tafiyar dan yanzu nazama shugaba,dan a jinina yake koh cikin yara yawanci nike jan ragamar abubuwa. Kallona sukeyi da Mamaki kaman idonsu zai fito saboda ganin abinda yah faru,saurin kawar da mamkinnasu nayi tareda cewa, "Kai Karku damu nasha maganin maciji babu abinda zaimin" Ganin sun yarda da abinda nacene yasa hankalina ya kwanta saboda kullum ina kula da gargadin da ummah tayimin game da halittata,alama nayi musu akan suyi gaba ina zuwa,yarda sukayi da abinda nace kafin sukayi gaba,saida naga sun bace babu alamarsu kafin na bude inda macijin yah sareni.Wajen ciwon ya warke sai wani abu daya fito daga cikin ciwon baki kirin da alama dafin macijinne,irin yanda ya tabayi sanda kunama ta harbeni lokacin ummah tana da rai,rude kafar nayi kafin nabi bayan hanyar da macijin yabi bayan ya sareni. A kwance naganshi a jikin wata bishiyah,yah murde kaman igiya yayi baki,tsugunnawa nayi ina kare masa kallo tareda Mamakin shin wane irin jini ne dani,duk wani abu inya dandana shi sai yah mutu. Tunani na tafi lokacin baya,idan na tashi da safe sai ummah ta kade shimfidina saboda duk sauron daya cijeni mutuwa yakeyi,kafin safiyah sun taru a gefen shimfidina,haka kunamar ma itama mutuwa tayi ummah ta zefar da itah ,toh gashi macijin ma ya mutu. Tun lokacin da ummah tana raye ban taba tunanin tambayar taba saboda yanayin yarinta,amma yanzu na gano cewar nidin dabance da sauran mutane kaman yanda dodannin mafarkina suke fadamin,amma har yanzu zuciyahta taki yardar cewar nidin dabance har yanzuina ji a jikina nima mutumce kaman kowa,tunda yah sameer ma mutumne yaza'ayi kowa na gidan mutum kuma niba mutum ba,hakan ba mai yiwuwa bane . Da haka na kawar tunanin a raina na tashi daga tsugunne a gaban macijin na kade rigata na bi bayan su iliyah wanda sunyi nisa yanzu. Ina zaune a tsakar gidan a gefe kowa yana ta harkarsa yau banje ko ina ba saboda an kare amfanin gona saidai muna tunanin tafiya wani gari aiki,saboda yanzu mun kware a wajen aikin kodago sosai musamman ma ni ,wani yarone yah shigo da sallama tareda cewa wai nazo inji yah sameer,gyara dan kwalina na nayi nabi bayan yaron,a zaune na sameshi akan benchi gefen dakinsu,samun waje nayi na zauna banyi magana ba, "Ke Bali I yah sallama bane bare kuma gaisuwa" Shiru nayi ina jinsa dan ina akwai wanda nakejin haushinsa toh

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});