Chapter 26
Chapter 26
sanar dashi" "Zan fadamasa ogah seemah" Bansami kowa a farlon ba da alama ummeeh da shige dakinta shikuma gogan yah fita,shaheedah ce ke biye a bayana fuskarta tayi narai narai da alama bata son tafiyahta,saidai ni kuma a nawa bangaren tunda naga abinda yah faru naji banason zama a karkashin wani ba iyah gidannasu ba ma,address din wajen na karba da kuma numaber wayarsa kafin na tari taxi. Bayan na shiga ne na juya naga shaheedah tana matse Kwallah,hakika nima banso mu rabuba saboda ita kadaice kawa mace dana tava yi a rayuwata,amma ni nafita juriyah badai mutum yaga raunina ba kama,ta inda muka banbanta da itah kenan,duk da ta iyah tsiyah amma tanada rauni gakuma shagwaba.ni kuwa wa yaga dutsi. *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤18❤ Tafiyah mukeyi a cikin birnin har muka shiga wajen da babu gidaje sosai sai jeji,ga kuma garin yayi duhu sosai da alama cikin kowanne lokaci ruwa zai iyah kwacewa. Driver ne yakalleni ganin muna ta shiga cikin jeji har munzo inda babu wani gida amma bance mun iso ba, "Gaskiya kiyi hakuri amma daganan zan ajiyeki duniyah babu yarda karnaje ke mai cutarwa ce ki cutar dani,kiyi hakuri bazan sake yin gaba ba gashi kuma hadiri ya hadu inason komawa wajen iyalai na ni.............." "Yah is a haka zaka iyah saukeni,banason dogon zance" Bayyi musu ba kuwa yah fara fitomin da kayana daga cikin motarsa saida yagama kafin na bashi kudinsa yayi gaba. Samun wani wajen kiran waya nayi na zauna saboda wayata babu charge. Tun daga nesa nake ganin hasken fitilar har yah fara isowa inda nake,ban matsa daga inda nake ba bare na tashi saidai kallon mai tahowa danake duk da bansan wayeba. Lokacin da suka iso wajena ne nakula ashe mazane guda uku sun saka rain coat bakake,zagayeni sukayi da bindiga kafin daya,daga cikinsu yasa, "Ke wacece,sannan kuma waya aikoki" "Bai shafeka da sanin ni wacece ba,saboda ba matsalarka bace" Kallon na raina musu hankali suka faramin saboda jin amsar dana basu, "Dolene ki amsa tambaya a wajen ogah binlad,ku daureta yanzunnan,sannan ku rufemata ido,sai iyayenta sun kawo kudi tukun" Tashi nayi daga zaunen danake ina kallon su,kayana na dauka na rike kafin nace, "Wanene wanda zan hau mashin din nasa,yazo mu tafi kar dare yayi ga kuma ruwan sai karuwa yakeyi" Nafada ina kallon hadarin a sama,ko ban kalli fuskokinsu ba amma yanda nayi magana nasan sunyi Mamakin action dinane,hakan a jinina yake bawa mutane mamaki da halina. Dukkansu tada mashin dinsu sukayi,ni kuwa saida naje gaban ogannasu mai barazanar kafin na dale mashin dinsa ina gyara zaman jakata. Kara nausawa cikin dajin muka kara yi,munyi tafiyah mai nisa kafin muka iso wani gida da aka yi katangarsa da karfe,masu tsaron bakin wajenne suka bude mana,dukkansu kowa yana rike da manyan bindiga a rataye,kana ganin su kaga manyan yan iska. A bakin wani babban d'aki muka tsaya,wanda yafi dukkan dakunan wajen girma,shiga sukayi nima nabi Bayan su. Wani farin balarabene a zaune yasha askin tankwal sai uban gemu kaman zayyi magana,bakar jallabiyace a jikinsa ga idonsa yasha kwalli,a takaice dai jan wuyane kawai. Sallama yamin na amsa kafin yace, "Sunana Binlad" "Nasani basai ka fadaminba" Yayi Mamakin yanda nayi masa magana babu tsoro amma kuma sai yah basar, "Baki fadamin sunanki ba" "Kaima baka tambaya ba" "Miye sunanki karamar yarinya" "Sunana sameemah " "Yayi barkanki da zuwa" "Toh" Daga nan na katse maganar tamu ta hanyar zuyawa ina kallon wajen,shima bai sake cewa komai ba sai kareni da kallo kawai dayake wanda inajin yanayin kallonsa a jikina,maganar sa na jiyo yana cewa, Akwai dokoki a wajennan sannan kuma saboda ke macece akwai matsayin dazaki tsaya bakomai zamu sakaki ba kar shirinmu yah wargaje", juyowa nayi Nima ina kallonsa kafin nace, "Ka barni a tsaye haka ake taryar sabon member ,toh ina jin bacci kuma sannan nagaji dayawa,inayaso koma mai za'a cemin sai gobe kuma" Daga haka na kalli wanda mukazo tare ina tambayar sa inda zan zauna,binlad ne yayi masa alamar ya kaini kawai inayso sai goben. Da safe kuwa wata tsohuwa ta shigo hannunta dauke da tea da kuma gurasa,karba nayi na ajiye kafin naje gyara jikina tukunna,saida na shiryah na karyah tukun naji dan aike na shaidamin kiran Ogah,wani dan gyale nasaka, a kaina bayan dogon wandon dayake jikina da kuma riga iyah gwiwa. Ya u ma kaman jiya yana zaune saidai yasaka rawani,samun kujera nayi na zauna tun baice na zaunaba, "Ke Baki iyah gaisuwa bane" "Na iyah amma banayi,kayi hakuri" "Keee,..........." "Kana Bata lokacin ka,bayan na fada maka ra'ayina,muwuce wannan shafin kawai,kafadamin menene abinda zanyi kawai" Buga bencin dake gabansa yayi idonsa yayi jaa,da alama furucina yah bata masa rai, "Tabbas ke baki sanniba kina bukatar a horar dake,inaso yanzunnan,samad kuyi mata bulala hamsin da dorina" Matsowa sukayi da niyyar kama hannayena ciki harda wata mata jikinta a murde,dakatar dasu nayi kafin na wuce inda mai bulalar yake,kwanciyah nayi akan table din hankalina kwance. Saida naji yah irga hamsin tukunna na tashi daga wajen na dawo na zauna akan kujerar danake zaune dazu, "Yanzu shugaba zaka iyah cigaba da bayaninka tunda hankalinka ya kwanta ka horani din" Bude baki yayi yana kallona,duk da yana kokarin boyewa amma alamun tsoro ya bayyana a fuskarsa,komawa yayi yah zauna tareda cewa, "Zaki fara koyon sand'a ko wuce waje batareda wani yah gankiba,sannan nagaba kuma harbi da bindiga saikuma koyon fada" "Saikuma me?" "Banson musu ki koyi wannan din tukunna" "Shikenan and gama ogah" Tun daga ranar na fara koyon harbi da kuma fada babi dare babu rana,nikadaice mai koyon saboda babu sabon shiga a lokacin shiyasa masu horon ni kadai suke yiwa. Cikin sati daya na kware wajen harbin bindiga da kuma fada,hatta wanda suke koyamindin sai sunyi dagaske su yi abinda zan aiwatar,labarine ya isa kunnen ogah binlad na himmata da kuma rashin tsoro. Saboda yanayin nasarar dana taka a cikin wata daya sunana yah fito a cikin wanda zasu je fashi,da farko su Samad sunyi bakin ciki ganin yanda nake taka matakin da saida sukayi shekaru kafin su taka,nikuwa harka ta nake ni kadai ,saidai idan aikine yasamu muke zuwa in group,shima wani lokacin Samad ya jagoranci shirin wani lokacin kuma ni,kuma duk aikin dana jagoranta ba a samun cikas,saboda koda harbi ake nice na ke tarewa saina zo gida kafin na cireshi,idan wani yayimana cikas kuwa cizo kawai nake masa kafin bayan sati daya mutanen mafarkina sun zuk'e jininsa,dan dama abinda suke so kenan,su kuma ko yaushe cikin karamin karfin jiki sukeyi idan nakai musu jinin da suke so. Bayan kwana biyu shiru banji labarin shaheedah ba duk da tacemin zatazo wajennamu,abinne yabani mamaki hakan yasa na shiga cikin gari da b'adda kama,mai gadinsu na tambaya a gefen gidansu nan yake shaida min kanin babanta yah tafi da itah gidansu wai zayyi aurenta a can,da farko nayi bakin cikin bamu sake haduwa ba,,amma nayi mata murna domin hakan shiyafi dacewa da itah,sama da rayuwar damuke,dan irin wannan rayuwar nikadai yakamata da dungayi tunda hakane kaddarata. Komawa nayi jikina da sanyi jin bata gidansu ta tafi inda rayuwarta zata inganta,tun kafin na isa na watsar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55